← Book details Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 34

Sashe 4

Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanadin Boko 1 02 Posted by ANaM Dorayi on 09:42 AM, 10-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Na Maryam Abdullahi K/Mashi Katon falo ne, yana dauke da kayan more rayuwa, sai kofofi guda uku, yace in zauna kan kujera, na zauna. Ina kallon ko ina, ya nufi kofa daya daga cikin kofofin, jim kadan ya fito dauke da gwangwanin maltina da kofi ya zauna hannun kujerar da nike. Ya balle hancin gwangwanin ya cika dan kofin ya mika min, na girgiza kai tare da cewa, "Na gode. Ya ce, "Wasa ki ke yarinya, rike nan ko na dura miki. Da sauri na amsa saboda nasan halin shi sarai, zai iya. Kurbata biyu na aje, ya kama hannuna na kwace tare da mikewa. "Tunda ka huce ni zan tafi. Ya ce, "Dama ni banyi fushi ba. Na kalli fuskarshi muka hada ido, ya kashemin idonshi daya, nayi saurin kauda idona saboda yarr din da tsigar jikina tayi. Na ce, "Yaushe zaka zo? Ya ce, "Zauna to mu tsara in da zamu dinga haduwa, don Babanku ya ce in manyana ba su zo ba kada ya sake ganina. Na ce, "Fada min daidai ina ne zamu dinga tsayawa? Ya dan yi shiru, "To ni bansan yaya zamu yi ba, na ce zan hada miki phone kin ce a gida ba za a barki ba, wai ke ba ki da irin 'yar dabarar ku ta mata ne? Ki saka ta a silent. Na ce, "Barta kawai. Ya dube ni, fatin kuma fa? Na marairaice murya ina kallon shi da idanuna, da na lura yana son su. Mu bar maganar party din nan, wallahi ba Babana ba har Innarmu in ta sani zan bani, ka ji. Ya tsare ni da manyan idanunsa. "Yanzun nayi asara kenan? Ya ci gaba "Ban san me yasa gidanku ake yin haka ba, ni kinga kannena su Nana da Suhaila Mom din mu da Dad din mu sune suka shirya musu party din su last week. Amma ku sai ana hana ku. Wannan duhun kai ne, yanzu fa an waye. Na ce "Ba wani duhun kai, kowa da irin tarbiyar da yake son ya yi ma 'ya'yanshi. Ya ce "Shikenan dai, mu bar maganar, naji nayi asarar kudina, kuma ba wani gida ke ce dai ba ki ga dama ba. Wani friend dina yarinyarshi itama 'yar Geto ce, amma ta jirga Iyayenta da cewa suna biki ne tazo muka yi shagali, amma ke kin kasa. Na ce, "Ni dai kayi hakuri kawai. Ya zuba min ido, sai kin yi min kiss zan hakura. Da sauri na dauki hanyar fita, sai kawai naji ya rungume ni ta baya, jikina ya dauki rawa. Cikin rawar murya na ce, "Munnir la..la....lafiyarka? Don Allah sake ni. Da kyar na kwace, kamanninshi sun canza, da sassarfa na fito na dau hanya. Ya biyo ni da mota shi da abokinshi, wai na shiga su kaini gida, na ce, "A'a don na tsorata, dole suka bar ni. Da na zo barci na jima ina tuno abin da Munir ya min, dama an ce mace da namiji in suka kebe na ukun shaidan ne. Ba don son da nake yiwa Munir ba, da tuni na bar shi. Mun canza gurin hira, bayan layinmu yake tsayawa. Na fada ma Innarmu ta ce saboda me? Na ce, Baba ya hana shi zuwa nan. Inna ta ce, "Mallam ho! Shikenan, ki dinga zuwa da Ummi kin san mutane da sa ido, yanzun sai ace wani abin ne yasa ku ke zuwa can. Fatana ki kama kanki. Na ce, "To, nima zuwa da Ummi zai fi min, duk da Munir ganin Ummi bai hana shi son taba jikina ba. Cikin haka muka soma shirin zana (JAMB), Baba bai sani ba, Munir ne ya sai min form, sai dai tsorona daya randa Baba zai sani. Na zama cikin sa'a kamar ko yaushe, Munir ya tsaya tsayin daka har na samu gurbin karatu a (B.U.K) Kano, sai dai ya zamuyi da Baba? Haka na ce ma Innarmu, ta ce yau na yanke shawarar sanar da shi komai, tunda gobe za ku je yin rijista. Kusan goman dare, lokacin ina kwance muryar Innarmu nake ji tar daga dakin Baba, domin bangonsu daya. Tana sanar da Babanmu komai. Bai katse ta ba har ta kai karshe, ya ce, "To bokon nan ba da yawuna ba, bayan shekara shidan da na hakura tayi yanzu kuma wata zata? Wai lahira take so ko duniya? Inna ta ce, "Duka. Ya ce, "Karya ne, duniya ku ke nema, kuma ga ku gata nan. Jami'ar da aka ce 'ya'ya suna lalacewa? Yarinyar ta fada a gabanki sama da shekaru amma baki damu ba. To magana ta ni uku ce, bata kai hudu ba. Na farko duk abin da ya faru da ita SANADIN BOKO ba ruwana, zai shafe ki ne da ita. Na biyu ba zan yafe hakkina da ku ka tauye ba, matsayina na Ubanta, kuka hana ni in sauke nauyin da Allah Ya dora min. Na uku kuma ta nemi Ubanta ke kuma ki nemi mijinki, duk ranar da wata ashsha ta samu SANADIN BOKO. Ba innarmu ba, ni kaina zancen ya girgiza ni. Baba kishiyar Innarmu ta fito daga uwar dakinta, ta zo kusa dani ta zauna. Tasa hannu ta dan dake ni, "Tashi Hafsatu. Na tashi zaune jikina sharkaf da zufa, ta ce "Nasan kin ji duk zancen da Malam yake yi ko? Na ce, "Eh. Muryar Innarmu ta katse ni, ta ce, "Insha Allahu Malam karatun Hafsa zai zama alkhairi garemu da kai gaba daya. Ya ce "Ruwanku. Cikinsu ba wanda ya sake magana. Babah ta ce, " Hafsatu ki bar Babanki yayi iko da ke, ki ce ma Innarku kin fasa karatu. Kalamanshi ba baki yayi miki ba, amma ina ji miki tsoron alhakinshi kada ya kama ki. Na ce, "Babah wanda zan aura karatu yake yi, ba yanzu zai yi aure ba, kuma Iyayenshi ba za su yarda ya auri mara ilimi ba. Babah ta ce, "Sai shi? Akwai masu sonki da yawa, kuma sun ma Babanki magana. Nayi shiru ina nazari, nasan Babah gaskiya ta fada min, amma ya zan yi da son Munnir? Na dube ta, "Babah ki duba irin hidimar da Munnir yake yi da ni, ba zan mishi adalci ba in na ce ba zan jirashi ba. Ta ce, "To yanda ki ka gani, amma karatun nan tunda ba na Muhammadiyya ba ne, banga dalilin naci ba. Kuma ni sai in ga yaron nan tamkar yaudararki yake yi. Anya auranki zai yi? Na ce, "Allah Babah aurena zai yi, ki dubi dadewar mu da hidimar da yake min. Ta ce, "Ba ta a nan, amma fa shawara ce." Na koma na kwanta, ita kuma ta mike ta nufi cikin dakinta. Zancen Babah ya taba zuciyata, illah magana daya da ban kama ba, wai tana ga Munnir ba zai aure ni ba. Nayi guntun murmushi, me zai sa shi ya yi ta dawainiya da ni ba zai aure ni ba? Yanda na raba dare ban yi bacci ba, na tabbata Mahaifana biyu ma haka ne, duk SANADIN BOKO. Da safe ina zaune da kofin koko sai juya shi nake yi na kasa sha, Innarmu ma sukuku take. Lokacin da ta zauna tana shafa ma gwangwanayan alalarta manja, na ce "Inna ko dai zamu hakura da batun bokon nan ne? Ta dube ni, "Saboda me? Na sunkuyar da kai na ce, "Naji duk yadda ku ka yi da Baba jiya. Tayi shiru, can ta ce, "Abu daya zuwa biyu nike so ki min. Na zuba mata ido, na farko ki tsaremin kanki da mutuncinki, kada ki banzantar da kanki, na biyu kiyi abin da ya kai ki makaranta, wato karatunki wanda nike fata ya zama sanadin alkhairi. Ta haka ne za ki wanke wa Mahaifinki tsanar da ya yi wa boko, har kannanki suma su samu dama suyi cikin kwanciyar hankali. Yayanki da bai samu damar ci gaba ba yana jin haushi. Ke tunda kin samu dama kada ki bani kunya. Na hada ki da Allah, ki rufamin asiri. Tausayin Innarmu ya cika ni, na ce, "Insha Allahu zan kula sosai, kuma zan fidda ki kunya, SANADIN BOKOn nan kowa zai huta, Baba zai yi alfahari da ni. Munnir yayi tsayin daka har na zama daliba a jami'ar Bayero da ke Kano, har lokacin da zan tafi Innarmu bata daina rokona in rufa mata asiri in lura da kaina ba. Nan na tafi na barta da surutun 'yan gidanmu, da 'yan unguwarmu. Wasu suce tana so ne ta auri mai kudi, shi yasa muka nace boko, wasu su ce dan kyan nawa bai fi cikin cokali ba, amma mun kuke sai nayi boko. Wasu su ce dan-dan masu hali ke sona, duk dai ta toshe kunne watan kwaram daya ne. Baba har fushi yayi da ita, sun jima kafin ya soma amsa gaisuwarta. Karin haushi yakai kararta ga danginta, maimakon su bata rashin gaskiya suyi mata fada, sai suka ba shi hakuri suka ce wai karatun yana da amfani. Ya ce, shi ba ya ce babu amfani ba ne, a'a tayi shi can gidan mijinta. Aure shi ne sama da karatun ta, sai suka ce ya yi hakuri 'yan kwanaki ne zata gama, don haka sai ya dawo ya zura mana ido ******* ********** ********** *********** ********* Jami'a wata rayuwa ce da ta sha bamban da secondary, banga laifin Baba ba yanzun don ya kyamaci boko, sai dai na sha alwashin kula da kaina, don haka na tsare gida bani da kawa ko aboki. Duk da Munnir na shirin tafiya Dubai karatu don kammala Masters dinshi, haka bai hana shi zuwa duk bayan sati biyu ba. Tafiyar tashi bata yuwu ba har muka samu hutun first semester, sati biyu dai za mu yi amma naji dadi, sai dai wannan hutun ne hutun da ba zan taba mantawa dashi ba a rayuwata. (Kuma shi ne dalilin rubuta labari na "SANADIN BOKO" . Sauran kwana biyar na koma Makaranta duk da inata dokin zuwa gida amma zaman gidan bai mun dadi ba, ko gaisuwata Baba baya amsawa har ta kai da naji muryarshi zan boye. Bello Abokin Munnir shi yayi sallama da ni, na sha mamaki don bai taba zuwa shi daya ba. Ya ce,
Chapter 4 · 0% Book details