Sashe 30
Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
don ita wani bangare ne na farin cikina. Gidan su Maman Rahma naje na dauko Shadad, jikinshi naji da dumi, ina zuwa gida na bashi (paracetamol) Na kwantar da shi. Sannan na shiga gyaran gida. Ina zuwa na samu ma yayi bacci, nayi Shafa'i da wutiru nima na kwanta. Cikin dare na farka don yin nafila kamar yanda na saba, sai dai kawai naji jikin yaro sharkaf da zazzabi. Na cire masa riga na dunga goge masa jiki da ruwa mai sanyi. Sanna na kara bashi magani, kafin safe Allah ya taimakeni jikin yayi sauki. Sai dai yan rigin gimun da yake yi na shiga gidan su Rahama muka gaisa da su mama, ina zama Kiran Rahama na shugowa, ina ji dama nasan ita ce, dan bani da number kowa a cikin zumu dina na daga ina cewa hajiya kenan, amarsu ta ango. Ta katseni da cewa, ba wata hajiyarki, shine ko ki kirani da safe ko? Nace shi kenan sai na hau doka maki kira da safe kisa angonki ya ji haushi na. Tace wane ango? Kin san Allah ba nan ya kwana ba, tare da su hadiza kawaye na muka kwana, ba ke kinki ba? Nace ai gara da na dawo, dan na sami shadad da zazzabi haka muka kwana. Amma yanzu Alhamdu lilahi. Tace to Allah ya kara sauki. Tace don Allah ina sa ido gurin programme din nan, wlh in baki zoba bikin zai baci, don kina da muhinmanci matuka a gurin. Nace to zan kokarta duk da shadad nata yan rigingimu, kin sanshi in baya jin dadi sai yayi ta rigima, tace yaro kenan Allah dai ya kara sauki,nace amin, yace kizo da wuri dai. Sai da na fara yima shadad wanka, sannan na shiga na fito naga gari ya soma hadari, nayi alawala dan yin sallar la‘asar, haka kawai yau naji ina sha‘awar shafe shafe a fuskata. Na fito da kayan shafa da rahama ta di bar min na lefenta, har da jaka da takalmi da mayafi ta bani duk pink, tun asali ni mai son yin kyale kyale ce, halin da na tsinci kaina ne yasa na daina, nafi minti 30 ina kyalekyale a fiska ta. Na dinga kalon kaina a madubi nasan nayi kyau sosai, har shadad yana kallo na, nace nayi kyau? Ya daga kai ina kulle gida rahama na kira na, na daga tace aminiyata ki tai makeni kada kisa naji kunya, wlh guri yayi guri amma ke kadai muke jira da wani abokin sagir da ya sauka daga adamawa state, anje daukoshi daga filin jirgin don Allah kiyi sauri. Nace to zubaina ganin zuwa amma fa garin akwai hadari, Allah yasa in sami abin hawa da wuri. Tsaye nake a bakin titi duk wani dan a daidaitan da yazo yana dauke da mutane, masu son banza watan yan rage ma mata hanya suna tsayawa Amma ni ko kallon su bana yi. Wata jibgegiyar jeep ta zo ta gifta, sai kuma ta dan dawo.sai tin inda nake ta tsaya, gilashin motar ya sauka a hankali,naga mai tukin saurayine yana sanye da shadda yar gaske blue mai duhu, hularshi itama blue ce, amma kalar sararin samaniya. Ta gefen ido na kaleshi, sannan na dauke kaina. Yace, yan mata ina zaton guri daya zamuje in na lura da shigar da ke jikin ki ko? Na kaleshi nace ba dole hakan ta kasance. Yace, yace ki shugo muje kinga hadari. Nace kuje na gode. Glashin baya ya sauka, naji saukar galas din ne da wani sauti da yayi, amma ban waiga ba, saima na dan kara taku biyu ta baya na. Muryar da naji ne tamkar in waiga, amma sai na dake yace shugo mana ga hadari nason zubo da ruwa gaki da yaro. Na dubeshi dan son in tuna inda na san wanan muryar, kyawunshi yasa nayi saurin kauda kaina, tare da cewa kuje ni ba zan shiga ba.daga cikin motar naji wani yana cewa don Allah mutafi amma za a taimaka mata tana yiwa mutane yanga,da sauri na kallesu cikin bacin rai, idanuna har kan kancewa sukayi don ta kaici, cikin kalon hadarin kaji nace taimako? Ce muku nayi ina neman taimako? Na dan duka tare da leka motar, kai me fadin taimakon nan kasani bana neman taimakon wani abin halita sai ma halincci, ni ban tsai da ku ba. Na kara rike hannun shadad da kyau, na soma tafiya dai dai da ruwan ya kece, kamar da bakin kwarya, ba tsanmani sai naga kofar ta wangale na bakin kofar ya sauko kafa tare da sauko hannu ya dauki shadad zuwa cikin motar, a gigice na dubesu yace ki shigo in kuma ba zaki shigoba ki samemu a can. Amma shi kam ruwa ba zai dake shi ba. Bani da zabi, tunda sun daukar min yaro dole na shiga. Gashi bana son dukan ruwan, don haka sai na shiga. Shadad na ciyar mutimin da muryarshi ke sani faduwar gaba, kamar na taba jinta ada innaso in tuna inda nasan muryar ko mai irinta. Muryar ta sake katseni da tunanin da nake yi, yace ma shadad boy ya sunanka? A zatona shadad ba zai yi masa magana ba, saboda shi yaro ne mara son ma gana, musanman in bai san mutun ba, sai naji yace shadad. Mutumin ya mai maita sunan shadad, sunanka yayi dadi, to wanan fa? Ya nunani ya sunanta? Shadad ya kalle ni, na zabga mashi harara, amma ga al‘ajabi na sai yaron nan ya kauda kai yace anty. Mutumin yace to kana zuwa makaranta? Yace eh al‘iman sunan makarantar mu, kuma muna yin (A B C D) har da(1234). Na rike baki inata al‘ajabin yaron nan, tunda nake dashi ban taba jin yana rarata surutu haka ba, harda kin kalona shida ko abu aka bashi da ya kali fuskata zai gane, in ina nufin ya karba ko karya karba amma sam ya ki kallona tunda ya gane ina hararan shi. Mutumin yace gud, kana yin kokari? Yace eh mana, har ma naci number one, aka min kyautar books. Anty na kullun tana koya min karatu, da su home work harda ma islamiyya, ban san sanda nace shut up stupit boy! Mutumin ya kalle ni, shikuma shadad ya kwanta lakwas a jikin mutumin. Ya tsorata dan bana mashi tsawa, ko yawan zaginsa. Na daga can gefen yace. Ke! Wai wane irin hayaki kanki ya keyi? Ko kuwa ance maki wani kyau ne dake? Ko ance miki sonki ake yi? Ko kuwa burgewa ce wannan masife masifen da kike yi. Nace kai saurareni bana son shishshigi da katsalandan cikin lamari na, nayi magana da kai? Ko nace ka kalle ni ne bare ka tan tance kyauna?gani na kayi a filin gasar kyau? Balle kace nace ina da kyau ne? Masifa kuma dole ku jita tunda ku ka nace sai kun dauko ni, haka nan bana bukatar burge kowa cikinku na fison in burge kaina. Don haka yi ta kanka dan dukanku bakwa gaba na, zaiyi magana mai dauke da shadad ya daga masa hannu alamun yayi shuru. Shi kuma yaci gaba da shafa kan shadad wanda yayi kwance a jikinsa. Wayata ta shiga ruri, ban ko kula ba dan nasan rahama ce, sai yi take tana katsewa, ana 5 din na daga a kufule, don itama haushinta nakeji ba don bukin ta bane wa za ya hadani da wayanan gardawan.