← Book details Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 34

Sashe 25

Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanadin Boko 1-7 Posted by ANaM Dorayi on 12:29 PM, 12-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Cikin satin da muka yi wannan maganar tazo min da lbrn cewa ta samo min aiki a wani Super market, amma da nisa tsakaninsu da unguwarmu.Na ce ba komai zan iya, ba d jimawa ba na yaye Shadad, na ci gaba da zuwa aikina, a wata dubu goma ake biyana. Shawara ta bani, wai in bude (account) tunda bn rasa komau ba, hatta sutura tana bani nata. Dan Adaidaita ta samo min duk wata sai dai in biya shi, sauran na kai banki, Nayi-nayi ta dinga cire wani abu a cikin albashina, amma sai ta ki ta ce ita don Allah take zaune da ni,matsala daya a gurin aikinmu ita ce manajanmu ba shi da mutunci.Farkon zuwana ya yi ta shige min shi yana sona, ganin yanda na birkice mishi sai ya sama min lfy, amma akwai zuga rashin mutunci. In minti daya ka kara bisa karfe 8, to zaya iya korarka, ban ta6a kai takwas ba tare da naje ba, sbd ina matukar son aikina. Shadad yana da hkr yana zaman shi gurin mai aiki. Cikin haka muka wayi gari cikin farin ciki, Doctor ta samu juna biyu, Mijinta mu2m mai mutunci da sanin ya kamata. Yayi murna, sai dai cikin yazo mata da matsaloli masu dama, ko dn ta manyanta ne? oho. Kwanci tashi ta shiga watan haihuwarta, mijin ya ce ta shirya su tafi Abuja ta haihu a can, wani asibiti na musamman. Sun tafi ko yaushe muna waya da ita, maganarta daya kullum ita ce mu sa ta addu'a, sannan ta ce min " Hafsa koda bn dawo ba kiyi kokari ke nemi mahaifanki tare da neman yafiyarsu. Mummunan lbrn da ba zamu ta6a mantawa da shi ba, musamman ni, shi ne na rasuwar Doctor Hindu, nayi kuka tamkar raina zai fita. Ta rasu bayan awa daya da haihuwarta, ta samu 'yan tagwaye mace d namiji, Innalillahi wa inna ilaihin raji'un, ko dangin Doctor basu kai ni jin mutuwarta ba, domin ni ita ce dangina uwata kuma ubana. Can Abuja a kayi jana'izarta, amma gidanmu ake zamn makoki, in da dangin ta da na shi suka zo. Tun kafin bakwai na soma tunanin gurin zuwa, don kan yanzun asirina ya tonu, gatana ya fadi., A zaton danginta ni 'yar aiki ce, amma dangin mijinta sun zaci ni 'yar uwarta ce, yaranta tubarkalla, lafiyyu ana ta ji da su. Ranar 7 kuwa subahanallah,tunda aka ce mu hada kayanmu za su rufe gidan hankalina ya tashi, mai aiki kuwa dama daga kauye take, bata samu matsala ba don ta riga ni tafiya. Ga shi gobe zan koma aiki hutun da gurin aikina suka bani a matsayin uwata ta rasu, kamar yanda na fada musu. Rahma ce ta fado min a rai, yarinyar da muke aiki shago daya da ita.Rahma tana da mutunci, bari in nemi taimakonta. Na kira lmbrta t daga, na ce Rahma don Allah ina nema wani agaji, ta ce na me? muryata ta sarke, Rahma ina son dakin haya a unguwarku, zan samu? Ta ce yau-yau din nan? Na ce eh, ta ce gskiya ba za a samu ba, sai dai in an bincika a hnkl. Na ce na shiga uku! Ta ce wai me yake faruwa? Na ce ba ni da gurin kwana, ta ce, gidanku fa,? Na ce ba gidanmu ba ne, kuma yau masu gidan zasu rufe gidansu, Ina da matsala. Ta ce ok, yanzun kina ina? Na ce ina gidan ina hada kayana, ta ce to za ki gane gidanmu? Na ce eh, ba Tukuntawa ba? Ta ce eh, Mama tana nan sai kiyi mata bayani kafin na dawo, na ce to na gode. Sun bani kayan sawa nata da yawa, na nemo dan tasi ya dauke ni zuwa Tukuntawa unguwar su Rahma, Mama da matar Yayan Rahma ne kadai a gidan. Muka gaisa, Mama ta ce daga ina? Sobada ganina da ta yi da kaya riki-riki na ce sunana Hafsat gurin aikinmu daya Rahma. Ta ce oho, yarinya da ku ka zo duba ni kwanaki ko? Na ce eh, ta ce ba Rahma ta ce min Mamanki ta rasu ba? Na ce eh ba Mamana ba ce, ta rike ni ne kuma yanzun 'yan uwanta sun zo zasu rufe gidan saboda ya zama na 'ya'yanta. To shi ne nake son ko zan samu dakin haya nan kusa da ku? Ta ce to za a cigita, sauke yaron ki shiga da kayan ki can dakin Rahma. Ina jin dadin zama da su Rahma don ina yin biyayya gare su, matar wan Rahma ce ka dai ke son min tambayar kurilla,tana yawan cewa to wai ina iyayenki? Ban ta6a amsamata ba, don ko Rahma bata san komai a kaina ba, bata san Matsayin Shadad a gurina ba, duk da ta cancanta in fada mata. Matsawar da nayi da son samun dakin shi yasa su Mama suka sa ne man dakin, amma d ta ce in yi zamana a nan gidan tun da ba ni da matsala, haka dana. Na ce, a'a ni dai na fi sobn na samu daki gidan mutunci gidan Hjy Iya aka samu dakin sai dai sun ce min sai nayi hakur, don tana da fada. Na ce, ba komai, in dai sai an tsokane ta ne zata yi to ba za ta ta6a yin fada da ni ba. Matsalar in da zan dinga kai yarona kafin ya isa shiga makaranta, ko da rainon kudi ne. Ta ce, ki dinga kawo shi nan mana tunda shi ba mai haya niya ba ne, Mun je naga dakin, karami ne ta ce dubu shida shekara, dari biyar kenan dk wata, na ce ba komai, zan biya. Naje banki na ciro dubu ashirin cikin kudina nazo na bata shida, naje kasuwa na siyo kayan abnci da yar tukunuya da dan risho na dawo. Zaman mu da Hjy Iya ba matsala, don ina bn ta sau da kafa,daga ni sai ita a gidan tun Asubahi in na tashi zan wanke mana bandaki, in share tsakar gidan, komai na dafa zan bata. In ko zan yi wanki na kan ce kawo naki Hjy, kullum sai dai ka ji tana shi min albarka, Shadad kuwa dama tuni ta ce in dinga bar mata shi tunda in bana nan ba shi da matsala, musamman in ya gane cewa gidan muke kwana. In ko unguwa na fita dashi kiwa ce dashi, sannan ya yi ta 'yan rigime-rigime. Mun zauna yanzu albashina da kyar nike kai dubu biyar banki a wata, saboda hidimomin gida wanda a da ban san suba, kai ko kan wannan ba zan manta da Doctor ba, domin ita ce ke yi min komai. Burina na gaba shi ne, in koma makaranta, amma yaya zan yi da aikina wanda shi na dogara da shi? Wata rana da dare na shiga gurin Rahma muna hira, na ce mata ina son na koma makaranta, ta ce aikin fa? Na ce shi ne matsala, amma ina son in samu ko 'yar Diploma ba sai nayi jami'a ba, ta ce hakan ma yana da kyau. Aikina daga karfe takwas din safe ne zuwa hudu na yamma, sannan wasu su zo masu kaiwa dare, na ce Rahma ko in koma aikin dare ne. Ta ce albashinsu fa bai kai namu ba kuma yawan cinsu duk maza ne, na ce to ya zanyi? Haka nan zan hakura in dai manaja zai yarda ta ce matsayaci ba, sai shegen iko sai ka ce gurin shi. Na ce ai dama ba shi ne da gurin ba? Ta ce ba shi ba ne, na wata Hjy ce mai kudi, ina zaton ma ba a kano din nan ta ke ba. Na ce to Allah dai yasa in dace zan tare shi in masa mgn, Rahma ta ce to in ya ki fa? Na ce ki taya ni addu'a ya yarda, Rahma ta ce to Allah yasa a dace, in za ki masa magana sai muje tare .Haka ce kuwa ta faru, domin washegari muna tashi daga aiki sai muka nufi ofishin manaja, yana zaune gabn shi laptop ce. Muka gaishe shi, cikin daurewa ya amsa, na ce "Yalla6ai nazo neman uziri ne. Ya harare ni,wannan karon ko me kika zo nema kuma kowa ya mutu ba zan ba ki wasu kwanaki ba, sai dai in ki nemo wadda zata zauna madadinki. Rahma ta ce, Sir, ba mutuwa akayi ba, tana son koma mkrnt ne. ya ce, to sai ta bar aikin. " Ya ci gaba da abn da yake yi. Muka kalli juna ni da Rahma, na ce ko zan iya komwa akin dare? ko kuma in zo duk lkcn d nike free hr dare? Ya ce wace makaranta? Na ce poly zan shiga, ya kalle ni dama ba ki riga kin shiga ba? Na ce eh, ya ce to in kin shiga sai muyi magana. Ni da Rahma muka yi godiya, bai amsa mu ba, mu dai muka fita muna mamakin yanda ya saurare mu. Ina jin an fara saida form na garzaya na sayo. Rahma tana ta min dariya wai na cika zumudi, Allah shi ne mai shirya ma ba wa al'amuran shi. Yau gani na samu gurbin karatu a poly, daga karfe daya zuwa biyu nake tashi, uku in zo shago, bn damu da rage min dubu biyun da aka yi cikin Albashina ba, saboda na samu shiga makaranta. Kuma na samu irin course din da nake so, wato (Mass comm) Rahma da murnarta take shaida min saurayinta Sagir zai turo magabatan shi, na ta6a baki tare da cew. "Yau an yo odar kaya a shop din nan, kin lura? Tace eh na lura mana. Amma me yasa kullum na dauko batun Sagir sai ki daure fuska? Haka nan ranar da na ce kuje ku gaisa kikaki.Shi ko kullum sai ya ce in gaishe ki. Na ce, um, ki dai yi hattara da samarin yanzun. Ta ce, Sagir yana da kirki kuma aurena zaiyi, na kafa mata ido, kada ki ba wa namiji amana fa, in kin yarda kenan. "Ta ce, to zan kula. Wata rana ta ce min za su je gidan Yayar Sagir, zata gaishe ta, wai tayi 6ari, na shirya muje na kalle ta
Chapter 25 · 0% Book details