← Book details Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 34

Sashe 11

Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanadin Boko 1-04 Posted by ANaM Dorayi on 09:56 AM, 10-Sep-15 Under: SANADIN BOKO @* NA Maryam Abdullahi K/Mashi "Da sauri na isa gurin shi, me buga kudi ina ka tafi na daina ganinka? Ya ce aikin kudin ki ne ya 6oye ni, na ce Allahu! Har ina cewa ka gudu. Ya yi dry, na gudu da kudin ki ki ke zato Na ce eh, nima ina dry. Ya ce kai kina da bn dry, to ga kudinki,amma muje gidan ku na bawa iyayenki kada wani ya bi ki ya kwace. Cikin murna na ce to daga nan ma in sun gan ka sun fi yarda. Na kama hanya a kafa ya ce ga mota can zo muje, in kin san hanya direbn mu sai ya kai mu, ba tare da wata shakka ba na ce to. Sam na manta da su Sa'a, sai da zamu shiga motar naji muryarsu,suna cewa ke Hafsatu ki ka sani ko dan yankan kai ne? Na dube shi, shima ya ji amma sai yayi tamkar bai ji ba, na ce ba wani dan yankan kai na shiga motar da dan tirena, shima ya shiga ya ce kawarki fa,shawara suka baki nace tame? Yace kin san ni ko dan yankan kai ne? Duk da gabana ya fadi amma sai na dake nace, bakayi kama dasu ba yace suna da kama ne? Nace oho amma kai bashi bane yace, dama sunanki hafsatu? Nace eh abakin su sa‘a kaji ko da suka kirani dazu ko? Yace eh nace yan bakin ciki ne, dan fa nace masu kana buga kudi sai suka ce mun karya ne, kai malamin makaran tane. Yace gaske ne ni malamin makaranta ne, amma daga yau na gama nace, duk da kudin da kuke bugawa basu ishe ka ba sai kayi koyarwa? Yayi dariya yace bautar kasa aka turoni daga jahar mu. Nace bautar kasa kuma? Yace kema watarana zakiyi in dai kikayi karatun da kike fadi, gwamnati zakiyi wa aiki na wata tara ko shekara. Ban gane nufinshi ba amma nace Allah yasa naga lokacin. Da gudu na shiga cikin gidan mu ina cewa inna fito kiga mai buga kudi ya bugo min inna ta saka hijab ta fito tana cewa ni ban gane wanan shirmen naki ba, ina mai buga kudin? Wannan yarinya da wautar tsiya kike inna tayi turus lokacin da tayi arba da rantsatsiyar motar tace hafsatu aina kika jajibo wadan nan...? Cak! Maganar ta tsaya lokacin da saurayin ya bude motar ya fito kyawunshi yasa inna tunain ko aljani na janyo, ta soma karanta (ayatul kursiyu) zata juya gida na rike mata hannu. Inna dan Allah ki tsaya mana zo muje gurin su tace a a hafsatu muje ciki bana tsamanin wadannan bil‘adama ne nifa nasan banda aljan ke ina kika isa kiga mai buga kudi, sai dai in jabun kudi. Saurayin yatako har gaban inna ya dan rusuna ya gaishe ta, ta amsa tana dan dari dari, nace to wanan ce inna ta sai ka bata kudina inna tayi ta maza tace samari daga ina? Ni fa ban fahimci surkulen da yarinyar nan take yi min ba? Yayi mur mushi ya dube ni jeki kawo min ruwa nasha, da gudu nayi ciki ban saurari inna ba da takecewa in dibi na baba yafi sanyi ina tafiya ya dubi inna yace mama zolayarta nake yi, ni dan bautar kasa ne an turo ni daga Adamawa state, ina koyarwa a makaranantar da take zuwa talla. Yawan wasanta ke burgeni har na shiga sabagarta, sai kuma na fiskanci cewa tana son karatu amma rashin hali ya hana hakan. Dan ta fada mun tana talla ne dan kawai ta tara kudin makaranta. To ni nazo ne in ba damuwa zan taimaka mata don ni daga yau in sha Allahu na bar kaduna kenan, don na gama abin da ya kawo ni, dai dai nan na taho da ruwa na ce masa gashi. Inna tace mika mashi yace a a dama basha zanyi ba bakiga na sha ruwa a mota ba? Nace eh yace to maida. Yaci gaba da cewa dama nawa ne kudin nata? Tace ni ban tambayi nata ba amma lokacin na wanta inaga dubu uku muka kashe? Ina ga ba zai wuce hakan ba. Ya ciro yan daurin nera goma gama guda uku sababbi fil ya mika mata ga wanan mama dan Allah ku biya mata kudin makaranta, ku cika burinta har tazama abin alfahari nan gaba. Allah ne kadai ya san al‘ummar da zasu anfaneta. Innarmu jiki yana bari ta amshi kudi tana ta zubo mashi godiya ma, sai daka tsale nake tamkar yarinya karama, ina cewa shi kenan na huta talla. Innarmu ta harareni tana cewa to kiyi mashi godiya mana, nace na gode yayi murmushi ya tafi yana daga mun hannu nima haka. Sai dai kash nayi mantuwa ban tambayi sunan shi ba, a lokacin ban damu in san sunan shi ba muka nufi cikin gida da murna innarmu bata da rufi, don haka a tsakar gida ta fada musu cewa wani bawan Allah ya taimaka min da kudin makaranta. Wasu suka taya mu murna ciki harda babarmu, wasu kuwa sun nuna bakin cikinsu a fili don Ade ina bayi naji tana cewa, maman abba yau kinji matar nan mu zata rainamawa hankali ta dai tura yarinyar ta maula. Maman abba tace ai shegen son kudi irin na maman hafsatu ya isa, ace mata sai rashin godiya Allah duk fa kokarin mujinta ta raina. Daga can asabe ta sako baki shi wannan mujin nata ai tuni ta gama dashi katsinawa kuma da shegen asiri? Dubi fa fada irin na mutumin nan sai da tasha karfin shi ga kishiya kuma sai yan da akayi da ita Ade ta ce, ayi dai mu gani, kina nan yarinyar zata janyo mata abin kunya, Maman Abba ta ce ta dage sai yarinya tayi boko, za su ga boko ai. Na fito cikin takaici ina kallon su, sai nan da nan suka canza mgn. Asabe ce suna ta zagin ki,wai kina asiri ke Bakatsina,wai zan ja miki abin kunya. Inna tana da fada, balle in an ta6o ta, ta fita da sauri Yayana Umar ya hau ni da fada,wai don ubana ni mahaukaciya ce da zan fada mata, na ce ka ji gulmar da suke yi ne? Hayaniyarsu ce ta fito da mu, Umar ya je yana cewa, Inna ta bari ta dawo daki, nan dai haka gidan kan rikice wani lkcn. Musamman in ana fada kan yara, ko gulma. Innarmu tana da fada kowa a gidan yana shakkar ta6o ta. Bayan komai ya lafa, muna daki ta ce "Hafsatu kin dai ji da kunanki, ina so ki baiwa mara da kunya, ki kare min mutuncinki, kiyi karatunki ki zama abn sha'awa da kwatance na ce to Inna. Cikin kwazo na soma karatuna, kudin dan gayu mai buha kudi ya bugo min sun taimaka min kwarai. Inna tayi musu kyakykyawan adani,sun ishe ni har zuwa lkcn da na gama JS 3, lkcn shekaruna 14 girma ya soma zuwa min 'yan alamu sun bayyana. Na kan ji mutane suna cewa, wai ban cika kyau a fuska ba, sai dai jiki. Yawan fadin ina da diri shi ne ya sani jin cewa ni mace ce musamman in nayi kwalliya. Wata safiyar Jumma' naje fitsari sai naga jini, cikin fargaba nazo har da hawaye nake fada wa Inna. Ta ce, Hafsatu girma ne ya kama ki yau nawa ga watan bature? Na ce 7. Ta ce to duk 7 ga wata za ki ga wannan jinin. Ta iya yiwuwa yazo kafin 7, ko bayan 7, amma duk wata dai za ki gan shi. In kuma ba ki gan shi ba hakan na nufin kina da ciki. "Na zaro ido ta ce ai ba a samun ciki haka sai in kin kasance me wasan banza da MazaNa sauke ajiyan zuciya,don nasan bana yi. Na ce ni dama ba ruwana da maza, ta ce na sani, amma ki kara.sannan ki kara sa tsoron Allahn ki cikin zcyrki. Daga yau din nan an bude miki fayil dinki, duk aikin alkairi ki ko akasin haka za a rubuta miki, don haka sai ki kula, ki kuma san me ki ke ciki. Tun daga wannan lkcn nasa ma raina tsoron maza, nake kuma duba duk wani aiki da zan yi zunubi zai ja min ko lada. Marubuciyar tace'Yan uwa mata zan dan mana wani tuni nan gurin, mu nutsur da 'ya'yanmu muyi musu bayani mai kyau tare da nutsa tsoron Allah cikn zukatansu, lkcn da suka samy kan su a irin wannan yanayin na balaga.....Allah yayimana jagora Ba zan manta da Jumma'ar ba, misalin 4 da mintina na yamma gari yayi sanyi La'asar, nayi kwalliyata da riga da wandon pakistan da Inna ta sai min a gurin wata mai gwanjo. Kore ne kalar lemun tsami da gyalanshi, Sakina kanwata yarinyar Baba kishiyar Innarmu ta ce " Yaya Hafsatu zan biki." Na ce, zo muje gidan kanwar Innarmu zan je Hayin Malam Bello na kai mata kudin dashin sabulu da suke yi. Ko can gidan matan gidan suna ta yaba yanda kayan suka yi min kyau.Dai-dai kan layin Biliya wasu matasan samari suna tsaye jikin mashin, kallo daya na musu na dauke kaina ban kuma kawo komai a raina game da su ba. Sai naji takun tafiya, ana cewa 'yanmata ji mana,maza sun sha yi min haka bana tsayawa, don Innarmu ta fada min karatu basa haduwa da soyayya, kada na sake na kula kowa. Ya zagayo ta gabana Beby saurare ni mana. Na' kalli fuskarshi,sai zcyta ta buga, ina son mu2m mai kyau, daga ganin shi dan gidan 'yan gayu ne. Na harde hannuwana a kirjina, ya sake dubana daga sama kuwa gsa kasa, "Wow! Ya sunanki?" na ce "Hafsatu." Ya ce "Nice name, Hafsy ina ne gidanku?" Kawai sai na samu kaina da yi masa kwantance, can kasa muke Abuja Road, layi na shida marar kwalta, kana zuwa layin ka ce ina ne gidan yawa za a nuna maka. Ya dan yi shiru don ya fahamice a geto take amma sai yace zan zo anjima ko gobe zan samu ganinki? Nace eh yace to sai kin ganni na tafi ina wai wayanshi sakina tace yaya hafsat mijinki ne? Cikin
Chapter 11 · 0% Book details