← Book details Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 34

Sashe 26

Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dabadan Rahma ba ce dana zabga mata ashar. Amma Rahma ta wuce in zage ta, kema da zan fada miki ki ji da sai na ce miki kada kije, ta ce ko zan san dalili? na ce yaudarar mazanzamani.Tayi 'yar dariya, "Hafsat me yasa kin matukar tsanar maza ne? Me suka miki har haka?" Murmushin takaici ya subuce min na ce, "Sun min da yawa." Ta ce, "Kada ki manta shekararmu 1 da Sagir kuma kudin gaisuwarshi na gidanmu." Sam ban san lokacin da maganar ta subuce min ba sai ji nayi ina cewa, "Shekaru 3 da watanni muka yi ni da Munnir, amma hakan bai hana shi yaudarata ba."Hawaye suka soma zuba daga idona. "Rahama zan fada miki amanar sirrina, in kin boye min kin kyauta, in kin tona min don kanki ke da Allahn ki." Nan na kwashe komai na labarta mata, ni kuka Rahma kuka, ta rungumeni babu mai ba wani hakuri sai da muka gaji da kanmu. Na ce, "Rahma zan koma boko ne kawai don faranta Ran Mahaifiyata, Insha Allahu zan kawo haske cikin zukatan Iyayena SANADIN BOKON nan." Rahma ta ce, "Ina bayanki, Allah ya shige mana gaba. Lallai zan ja baya da Sagir kuma ba zanje gidan Yar tasa ba." Na ce, "Na kula Sagir dinki kamar bashi da matsala, duk daba anan take ba. Ki ci gaba da mishi yadda kika saba amma ko da wasa kada ki bishi wani guri. Amma ni a kan kaina na gama soyayya, na kuma sha alwashin duk namijin da yayi gangancin cewa yana sona zan ci zarafinsa matuka. Rahma ko kinga laifina?" Ta ce, "A'a."Rahma 'yar amana ce, ko Mahaifiyarta bata fadawa labari na ba, haka na ci gaba da Karatuna tare da aikina, na tsare mutuncina ko a makaranta nasha jin ana zagina wai na cika girman kai, daga ganina ni ba 'yar kowa bace sai shegen Iyayi, ga daure fuska. Sam ban damu ba, sai dai mutum in ya isa ya zo gabana ya fada. Kwanci tashi har na hada Diploma, kuma ina da burin ci gaba da HND,shekara 2 kenan. Cikin shekara 2 har Shadad ya isa shiga Makaranta, kuma na lura zaya dauki Karatu sosai, shekarunshi 4 kenan da 'yan watanni. A hanyar zuwa gurin aikina naga wata Makaranta Al-Iman, boko ce da Islamiyya don haka na je Makarantar na karbar masa form, sun ce yaro ya zo tun 8 na safe sai 6 na yamma. Duk da Islamiya da hadda, sati da lahadi sai karfe 2 zai je. Alhamis da Juma'a karfe 2 zasu tashi. Tsarin makarantar ya min daidai domin zan samu lokacin daukan shi, sati na zagayowa ya soma zuwa, da dare kuma inai masa bita. Tambaya daya ya min wadda ta sa ni kwana kuka, tare da tunanin me zai faru nan gaba? Ko ba komai nasan nan gaba akwai kura, abin da ya faru ranar da ya fara zuwa Makaranta ya dawo muna yin home work ya ce, "Anty." Na dube shi, "Menene?" "Me yasa da kika kaina Makaranta baki sa min sunan Babana ba? Duk 'yan ajinmu ana kiransu da sunan Babansu, ni kuma ana kirana da Shadad H." Gabana ya fadi, amma da yake shi karami ne yanzun ba zai fahimta ba sai na ce, "H din nan farkon sunana ne Hafsat na sa maka ko baka so?" Ya ce, "Anty kowa sunan Babanshi yake sawa, wani yaro yace min wai menene H? Wai Hamza sunan Babana?" Na ce masa, "Ban sani ba, nace ba sunan Babanka ba ne, sunana ne kaji ko?" Ya ce, "To." Can kuma sai naji ya ce, "To shi Babana ya sunan shi?" Gabana ya sake faduwa na daure na ce, "Na manta, amma in na tuna zan fada maka." Na mike don kar ya sake yi min wata tambayar. Shadad karamin yaro ne amma in ya maka magana sai kayi zaton Babbane. Ina tsoron nan gaba kadan ya tsareni don in fito masa da Ubansa, abu 1 na sa a raina, shine zan zama uwarsa kuma ubansa, zan yi masa komai da uba zai ma dansa. Tun da na bar gida har yau ban daina kuka ba, ban daina tunanin iyaye da 'yan uwana ba, kullum sai na zubar da hawayena tare da yin Allah ya isa kwando dubu ga Munnir, ba zan zagi Boko ba sai dai ba zan gaji da cewa itace sanadin shigata matsala ba. Haka kwanaki suka yi ta shurawa Allah ya taimake ni na koma don samun HND sai dai manejin rayuwa nike, albashina yayi karanci ya dauki nauyin karatuna da na Shadad, don ma na tara kudi da farko lokacin Dr. tana nan. Sai dai na dauki alkawarin ko zamu kwana ba mu ci ba bazan taba neman taimakon abokin halitta ba, sai dai in nema a gurin Mahalicci. Cikin wannan halin yarinyar Hajiya Iya wadda ke zaune a Saudi ta zo ta dauke ta tare da barin amanar gidan a hannun Babban Yayan Rahma. Amma ni Hajiya Iya ta ce in yi zamana kyauta har sai lokacin da Allah ya daga, don ta ce ina lura da ita, kuma duk abinda na ci sai na bata koda bata san da shi ba. Na ji dadin samun wannan rangwame duk da cewa kudin ba wasu yawa bane dama, amma sauki yana da dadi. Na dawo ni 1 a cikin gidan, in zan fita na kulle, in sati ne ko lahadi ko dai wane lokacin ne Shadad ba zai je Makaranta ba sai na kai shi gidan su Rahma gurin mama, in ko ba nisa zanyi ba nakan yi kasadar kulle shi ya taka kujera ta ciki ya sa sakata, in na dawo sai na kwankwasa ya bude. ****** ******** ******* A garin Kaduna tun da aka wayi gari Hafsat ta gudu, bakin ciki ya karu ga zuciyar Innarta, don haka ta tattara yanata-yanata ta fice ta bar su Ummi suna ta kuka, Baba tana lallashinsu. Har ta isa Malimfashi idanunta basu kafe da hawaye ba, bata boyewa 'yan uwanta komai ba,sunji bakin ciki suma saidai sun bata shawarar tayi mata addu'a kada ta mata baki.Haka ta ci gaba da zama har zuwa lokaci mai tsawo. Wani abokin wansu Babba ya zo ziyara daga Huntuwa ya ganta ya ce yana sonta, bata da zabi tunda duk yayyinta sunnuna sun amince, kuma aurenta da uban 'ya'yanta ba kome. Alhaji Danlami Matarshi ta rasu wurin haihuwa, amma yana da yara kuma yana zaune tare da su ne, shekarunsa 3 kenan rabonsa da aure, ta tare a gidansa dake Nasarasa Funtuwa, dole ta koyi hakuri domin zama da yara sai hakuri, in ta kalle su sai ta tuna da nata da ke can wani gida. Sai ta kyautata musu ko don a kyautata ma nata, yadda take kula da Yaran sai suma suke son ta. Cikin haka ta samu ciki ba don san ranta ba, amma ba zata butulcewa kyautar Allah ba. Ta haifi danta namiji ya ci sunan Rabi'u. Umar ya kan kawo mata ziyara da 'yan kannanshi, mijinta yanada kara don in zasu tafi yanai musu shatara ta arziki. Shi kuwa Babansu Hafsa har yau yana bakin cikin tafiyar ta duk da shine ya koreta, yana kuma addu'a Allah kada ya bashi mai irin halin Hafsa cikin 'ya'yansa, ganin halinta ne da na Uwarta, ko wani buri suka ci na son abin duniya shiyasa suka dage da boko, boko har taje ta yi abinda taga dama.Ni kuma lokacin rayuwa ta min tsanani, zuwa wannan lokacin kudin da ke cikin account dina sun kare, albashina ya min karanci, karatuna ga na Shadad, ga abinda za mu ci, omon wanki, sabulun wanka har da suturar sawa, duk a dubu 8. Don ma bana biyan haya. Yau na wayi gari ko na karyawa bani da shi, ga shi wannan watan shine zan bada kudin term na Shadad dubu 4, gashi zan yi registration, gashi bamu da komai na abinca ga kudin dan adaidaita sahu. Hakika komai ya tsananta gare ni, kukana ya karu, nadamar barin gidan Iyayena ta sake shigata sai dai ba zan iya komawa gidan yanzu ba, duk da kuncin rayuwar da nake fuskanta. Lallai babu komai cikin barin gida in ba takaici ba, danabi Mahaifiyata na san danginta za su saurareni za kuma su fahimceni, zan samu gata ni da dana kafin Allah ya min sakayya akan Munnir. Bana ba duk wata 'ya mace shawarar barin gaban iyayenta don gudun zubewar mutuncinta. Hawaye na bin kumatuna ban damu da na share su ba, domin da hawaye na karewa da yanzun nawa sun kare. Muryar Shadad ce ta katseni, "Antyna menene yake damunki kullum kike kuka?" Na share hawaye tare da kakaro murmushi, "Babu komai." Ya dafa cinyata, "Kina tunanin Iya ne?" Na ce, "Eh." Ya tambayeni ni don ya san kalmar da zan fada mishi kenan, a duk lokacin da ya tambayeni haka nake ce masa. Ya bata rai, "Anty to muje gurin Iya din, ni bana so kina kuka." Na ce, "Da nisa jirgi ake hawa kuma bani da kudi." Ya ce, "To ina girma zan saya mana jirgi muje ko?" Na ce, "Allah ya sa." Kicin na shiga ina dubawa, ko zan ga dan wani abin na baiwa Shadad, duk da nasan cewa bani da komai. Shiru na yi tare da tunanin abinda zan bashi. Rahma ta yi sallama, na amsa, ta shigo kicin din tana cewa, "Ina Hajiyar gidan nan?" Na yi guntun murmushi tare da cewa, "Rahma kenan, duk tsokana kin santa." Ta ce, "Na zo shan tea din kin nan mai kayan kamshi." Na ce, "Sai dai na baki kayan kamshin ki je ki dafa." Ta zuba min ido cikin sanyin jiki, sannan ta ce, "Hafsa kin 'ki daina kukanki ko?" Na ce, "Ina kika ga ina kuka?" Ta ce, "Haba Malama, ga idonki nan?" Ta shiga bude-bude, bata ce min kala ba ta fita. Ina cewa, "Rahma zo ki ji." Bata juya ba ta wuce. A zuciyata na ce Rahma kenan, ita dai ta tsani ta ganni cikin damuwa, ina son zama da ita don ita kadai ce kan sani murmushi. Jim kadan sai gata da kunshin kosai da jug dauke da koko, bata min magana ba ta zuba ma Shadad. Na ce, "Rahma koko kuka dama?" Ta
Chapter 26 · 0% Book details