Sashe 7
Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sanadin Boko 1-03 Posted by ANaM Dorayi on 09:47 AM, 10-Sep-15 Under: SANADIN BOKO NA Maryam Abdullahi K/Mashi To ku dan bamu wuri." Suka fita. Ta zabga min harara, "Kin bashi kan ki ko?" Murya ta a sarke na ce, "Wallahi Anty fyade yayi mun." Ta ce, "Tun yaushe?" Na ce, "Za'a kai wata daya." Ta bani wata 'yar roba ta nuna min wata kofa, "Shiga toilet ki bani fitsarinki." Ina fitowa naga wata nurse tsaye ta ce, "Don Allah sister ina son result yanzun nan." Ba jimawa ta shigo, Likitar tayi ta juya takardar sannan ta dube ni ta ce, "Kina da cikin wata daya da kwanaki." Nan da nan na soma zufa, zuciyata na kwadayin ina ma mafarki ne? Cikin tsananin kuka da kunan rai na ce, "Ya cuce ni. Mai zance da Innarmu? Abun da Baba yake tsoro ya faru. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Kuka na ya shigo da su, ta mika mishi result ya duba sannan ya kalle ta, "To yanzu doctor ya za'a yi tunda gaskiya ni da ita karatu muke yi, bamu shirya taron Baby yanzun ba." Na dube shi yana magana hankalinshi kwance kamar wanda ya aikata abin arziki. Ta ce, "Baka shirya tarban Baby ba mai ya kaiku aikata haka?" Ya ce, "Tsautsayi ne." Ta ce, "A'a ku ji tsoron Allah, aure shine ya fi dacewa da ku, karatun boko ba zai hanaku aure ba. Amma sai kaga ana wasa da Sunnag kun zabi boko sama da raya sunnar Manzo (S.A.W), to ku sani Manzon Tsira (S.A.W) ya ce aure Sunnar shi ne, duk wanda ya ki sunnarshi baya tare da shi. Kun fi yadda kuyi ZINA fiye da aure." Ta nuna shi da biron hannunta, "Musamman irinku 'ya'yan 'yan boko, Iyayenku sun rike wuta sai kunyi karatu mai zurfi basu damu da halin da zaku shiga ba kasancewarku balagaggu, burin su ku iya turanci tare da kawo musu kyawawan sakamako lokutan jarabawar ku. Ba su damu ku san addininku ba bare kusan illar ZINA."munir yace to doctor, yanzu menene mafita? Don matsala ne cikin nan don Allah a cire shi tayi suru tana tunani. Bello yace in bazaki iyaba muje wani asibiti doctor hindu tayi shuru tana nazari, tace to zan tai makeku sai a lokacin naji sanyi ya ratsa zuciya ta. Ta bani wasu kwayoyi wai kafin nan da sati daya zai fita, suka ce nawa? Tace dubu goma nan take suka biya. Sun saukeni makaranta sanan suka wuce, da alkawarin zaya rinka kira yaji abinda ke tafiya. Yau kwana tara shuru sai laulayin da nasoma gadan- gadan, ga sheka amai nan ga zazzabi na kwasa na koma wajen doctor hindu ana kai mata kati na tace a turo ni duk da yarinyar da naga ta shiga bata fito ba, itama yarinyar duk a firgice take, taci kuka ta gode Allah nace sannu doctor. Tace yauwa ya jiki? Cikin saurin baki nace da sauki amma fa har yanzu bai fita ba. Ta mikye tare da diban wayoyin ta ce ku biyo ni. Muka biyo ta cikin harabar asibitin muka nufi wani gida kirar zamani dan madaidai ci. Ta umurce mu mu zauna kan kujerum da ke kayatacen falon,ta shiga wani daki daga cikin dakunan biyu dake cikin falon. Jim kadan ta fito ta canja shigarta zuwa doguwar riga ta atanfa. Ta shiga kicin yafito da doguwar gorar ruwa (swan) da kofuna guda biyu. Ina takure cikin hijabi na, zazzabi ne ya rufe ni ta tsiyaya ruwan ta miko min, sha ruwa nace a a sanyi nake ji ta koma takawo min paracetamol na sha. Ta zauna ta zuba mana ido, ta dubi dayar tace asabe ko? Yarinyar tace eh, menene labarinki? Yarinyar ta ce, Sunana Zainabu,amma an fi kirana da Asabe.Mu 'yan asalin nan kano ne, a karamar hukumar kunci can wani kauye ana ce masa kurje. Wata mata mai suna Gambo tana zuwa kayaunkan garinmu tana diban yara 'yan aiki, wata rana taxo gidanmu ta ce da Babata su bada ni ana samun kudi sosai, wai can zan samu kudin kayan daki. Sai na ce ni ba zani ba, nafi son nan don ina talla kuma ina zuwa karatun allo. Sai Babata ta ce to abar shi, don Babanmu in ya ji ba zai yarda ba, ta ce can ma ana karatun Muhammadiyya, kuma za su saki ga cima mai kyau za ki canza. Haka dai ta zuga Babata hr ta yarda, sai da suka yi rigima da Babana sannan ya yarda. Gidn Hjy Mairo aka kai ni, ba wani aiki sosai kuma bata da tukara. Ba ta da Matsala in kaga damuwarta to ran danta ya 6aci, don shi ne dan ta kwallin tal. Yawancin aikin nawa duk nashi ne don tana zuwa aiki shi ma yana zuwa makaranta, amma ya fi ta zama gida.Ba mu cika shiri da Yasir ba, don shi yana da fada. Watana 3,ranar wata Litinin ina kicin, ya shigo wai in dafa masa Idomie, nan na bar komi na shiga dafa masa, don Hjy ta ce kome nake yi in yazo da nasa in bari in masa don a zauna lfy. Ba ta so ta ga yana zagina, na ce to. Da na gama na nufi dakinsa, na aje zan fita ya ce in dawo, cikin sauri na dawo don ina matukar tsoronsa, kawai sai ya ce in cire kayana. Na soma zare ido, ya ciro wuka da sauri na cire ya kwantar dani ya aikata alfasha da ni, sannan ya hana ni kuka. Ya kuma ce idan wani ya ji sai ya kashe ni. Naja baki nayi shiru, duk uwar wuyar da na sha tun daga nan muka daina fada, Yasir ya maida ni tamkar matarsa. In Hjy bata nan sai ya kira ni dakinsa, akwai lkcn ma da Hjyn taje Umra ta barmu tare da wata 'yar uwarta don ta lura da mu, da kuma gidan,amma Yasir cikin dare zai zo ya buga in kofa, dakinshi nake kwana. Nan da nan nayi wani girma, kirjina ya cika. Daku abn da ya gani zai sai min,wata rana na tashi ba lafiya,sai amai nake shekawa,Hjy ta kira Likitansu tun kafin ya gwada Ni ya ce yana zaton ina da ciki,ya ce amma bari dai ya gwada. Gwajin Farko ya nuna ina da ciki, nan ta shiga salati da sallallami, ta tsare ni wai in fada mata wanda ya min, na ce Yasir ne. Nan ta hau ni da duka wai na masa sharri, dan shekara ashirin da biyar dinne yaya iya yi min ciki? Da ya dawo ta tambaye shi da har ya musa sai yaga ta watso min kayana, wai na tafi zan yi ma danta sharri, sai ya ce mata shi ne,amma tsautsayi ne. Ga mamakina, bata yi masa wani fada ba, sai dai ce masa tayi kada ya kara, kuma Babanshi zai dawo. Ta kai ni wani asibitu aka cire min shi ta dinga min fada wai ko ya kira ni kada naje. A cewarta, wai bashi da laifi ni ce mai laifi. Sati biyu ina jinya, Sannan na gyagije, ganin ta sa mana ido, sai ya ce in dinga barin dakina a bude zai ringa zuwa. Na ce Hjy ta ce mu daina. Ya sake zare min ido, dole na bi yanda yake so, wai baya so Hjynshi ta sani, don ta ce mishi in ya sake sai ta aura masa ni, shi yasa duk ya tashi hankalinsa yanzun. Doctor ta ce, To shi baya son ya aure ki ne? Asabe ta ce, tab ita ma nasan tana tsorata shi ne, domin ba ta da burin yayi aure yanzun. Burinta shi ne ya yi karatun boko mai zurfi,kuma ya zama wani abu a kasar nan SANADIN BOKO." Na jinjina kai, tuni zazza6ina ya sauka. Labarin Asabe ya ta6a ni, kallo na dinga bn ta da shi, Yarinya ce ba zata wuce Shekara sha uku zuwa sha hudu ba. Wanna ma ai child abuse ne, ya kamata a hukunta su shi da Hajiyar shi. Doctor ta katse min tunani da cewa Hafsat me ya faru da ke kuma, menene labarinki?? Na zuba mata ido, hawaye suna zubowa, ta ce fada min ina so ne in taimake ku, na ce zaki cire min cikin? Ta ce Eh, zan cire miki in har naji labarinka, kin cancanta a cire miki.Ina nufin in ban da son ranki hakan ta faru ba. Na share hawaye,sannan na ce da ita. "Sunana Hafsatu, Mahaifina dan asalin jihar Borno ne, ya fito daga gida tun zamanin yana saurayi, a kano ya yada zango, nan yake 'yar sana"arshi.Sun hadu da Mahaifiyata a can lkcn tazo gidn yarta a Na'ibawa. Babana Shi ne ta tambaya ya yi mata kwantancan gidan Malam Ma'aru me Almajirai mijin yarta kenan.Daga lkcn ya nuna yana sonta, ta amince hr yaje Maliunfashi jihar Katsina, unguwar Fayamasa. Ya samu kar6uwa cikin dangi, don yana da nutsuwa da ilimin addini aka ce ya turo magabatansa.Mahaifanshi sun rasu sai babban wansu Babagana, shi ne ya zo suka hadu da wani uban dakinsa. A nan kano suka zo, sune suka amsar masa auran Innarmu.Ba su jima a kano ba ya soma zuwa kaduna, ya fara sana'ar saida lemo da Ayaba,daga bisani ya nemi gida a hayin rigasa ya dawo da Innarmu,lkcn tayi haihuwar farko wato Yayana Ummar. Gidanmu gidan haya ne, Mai girma gaske a layinmu kaf ba gidan da ya kai namu yawa don gidan yawa ake ce mana. Mata goma sha ne, kowace da 'ya'yanta wasu hudu wasu shida,wasu goma sha. Babana ya sake auro wata matar daga kano, itama nan gidan ya samu daki kusa da na Innarmu., Babah tana da kirki da nutsuwa, shi yasa duk yanda Innarmu taso suyi rigima bata biyewa, dole itama ta saki suka zauna lfy. Yanzun Babah 'ya'yanta 6, Innarmu 8. Ni ce 'ya ta 2, masu bina 3 duk maza ne, sannan mata. Innarmu gidan su 'yan boko ne, ko na ce kowa yasan Katsinawa da boko. Don haka tana da burin mu 'ya'yanta muyi boko, shi ko Baba ba ya da burin mace ta wuce primary. A nashi ra'ayin nayi saukar Alkur'ani mai girma ya min aure. Tun muna kanana Innarmu ta kwadaita mana boko, don haka ni da yayana mun taso muna son karatun