← Book details Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 34

Sashe 1

Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanadin Boko 1 01 Posted by ANaM Dorayi on 09:25 AM, 10-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Na Maryam Abdullah K.Mashi Ina sauraren duk hirar da kowaccen su ke yi, motar ta kacame da surutu. Wasu na murnar ganin Iyayensu, wasu kuma suna zancen auren su. Mafi yawa daga ciki kuma suna fadin makarantun da za su ci gaba, wasu su ce poly wasu Jami'a, wasu Nursing school. Sa'adatu da ke kusa da ni ta ce, "Hafsy don Allah kema ki shigo (A.B.U Zariya) mu hadu mana." Nayi dan murmushin takaici. "Samun (A.B.U) fa ba kamar shiga Bakori ba ne, saboda in ma zan samun bani da wani tabbas akan za a barni." Ta zaro ido. "Kada kice min kina cikin wadanda za'a dakile a kai gidan miji? Na sake ajiyar zuciya. "Ke dai Sa'a taya ni da addu'a, Allah Yasa ina da rabo, dan kuwa ina son in ga karshen boko." Jamila ta dube ni, "Hafsy ko yaushe kina bani mamaki in kina cewa za ki ga karshen boko. To bari kiji, sai dai boko yaga karshen ki. Ance miki wannan lokacin yana jira ne? Na ce, "To Malama, ban saka bakin ki ba, ina ruwanki. Ke ba kince aure ba?" Jamila ta ce, "Aure kuwa insha Allahu ba ya hana karatu, zan yi aurena na ci gaba da karatuna. Sa'a ta ce, "Wahala ai daya za ki zaba, don da kin yi ciki za ki watsar da batun karatu. Na ce, "Dubu nawa akayi? Ai ni boko yanzu muka sa dan ba." Ta ce, "Shikenan, Allah Ya taimaki kowa kan niyyarshi ta aikhairi". Na ce, "Ga magana da za ki yi kawai, Amin". Da tafiya tayi tafiya, sai ka ji kowa shiru. Ni kam fargabar Babana nake yi, nasan inba wani ikon Allah ba, da wuya naje wata Makarantar. An sauke *yan zariya, sannan mu *yan Kaduna muka nausa hanya, motar makaranta da ke Bakori Katsina, ita ce ta debo mu zuwa gidajenmu, bayan mun yi bankwana da makarantar wato mun kammala. Gidanmu ya kaure da sowa, yara na ta murna "Ga Hafsat ga Hafsat". Innarmu ta fito da gudu ta rungume ni, ina ta dariya. Almajiran da suka dauko min kaya suka sauke, na ce, "Innarmu ba su hamsin". Ta kwance habar zani ta mika musu. Yaran gida suka taya ni da kaya zuwa cikin daki, matan gidanmu kowa sai sannu da zuwa suke min ina amsawa. Inna ta aje min kwano tare da cewa, "Alalar har ta huce". Ta dire min kofin ruwa na ce, "Har yanzu bata kare ba ne?" Ta ce, "Ta kare mana, ai tun kwanaki da Kawunku Bako yazo ya ce min cikin kwanakin nan za ku kammala, kullum sai na aje alalar sai dai in naga magariba tayi ne sannan in ba yara. Nayi dariya tare da cewa, "Innarmu kenan! Ina Yaya Ummar?" Ta ce, "Tun safe bai dawo ba, kin san nasai mashin da aka yi mana rabon gadon nan, Kawun ku Bako na kawo min kudin na ce a sai mishi mashin wannan yaran, tunda zaman banza yake, aikin gyaran wutar nan ba ko yaushe ake samu ba. Ina fama da kannan shi ina fama da shi. Na ce, "Kinyi dabara Innarmu, in yayi Achabar sai a rufa asiri". Ta ce "Kwarai kuwa. Ummi ta zo ta zauna kusa da ni, na ce "Ummi da ba ina ta kiranki kin ki zuwa ba? Inna ta ce, "Kullum sai ta ce Innarmu ina Auntyna?" Na rungumota a jikina ina cewa, "Gani na dawo". Ta rufe fuskarta, ita dole taji kunya. Cin alalata nake ina jin dadi ga ni ga Innata, ta ce "Kin zo a daidai bikin su Hajara da Sakina ya kusa". Na rike baki, "Inna har da Sakina?" Ta ce, "Eh! Na ce, "Uhm! Ni da so samu ne in ci gaba da karatuna ma". Innarmu ta ce, "Malam ne matsala, amma ko Nas din nan da 'ya'yan Kawunki suke yi ai zan so kiyi." Na ce, "Wane Nurse? Ni fa Jami'a nake so, burina in zama 'yar Media". Ta ce, "Me kenan? Na kafa kofin ruwa na daddaka, sannan na ajiye tare da cewa, " 'yar jarida mana! Sai dai matsalar kudi ne". Kai lomar alala da nayi baki, ta zo daidai da sallamar Baba, nan take naji wani daci tamkar na tauna madaci. Innarmu ta mishi sannu da shigowa, tare da shimfida mishi tabarma. Cikin fargaba na soma gaida shi, ga mamakina yau fuskar shi sake ya amsa, har da ce min "An dawo lafiya?" Na ce, "Lafiya lau". Innarmu ta ce, "Allah cikin ikonSa Malam yau dai su Hafsat karatun Sakandire ya kammala." Ya ce, "To dama tunda da mai sonta sai ta yi masa magana ya fito in hada su da Sakina in huta". Inna ta ce, "Anya kuwa? Ina ga daurewa da zaka sake yi ta tafi makarantar gaba da..." Wani kallo da ya mata shi ne ya dakatar da ita. Ya mike tsaye ransa a bace. "Na gaji da wasa da hankalina da ku ke yi, ba zan iya ganin Hafsa gandandan cikin gidan nan ba, duk wanda ya shigo ba zai bambance ta da matan gida ba, duk wata tana zubar da jini, ta zama Uwar mata. Wannan karon zamu yi tsiya da ku yanda bakwa zato. Wai menene cikin wannan bokon da ku ka nace mawa? Ina ce karatun gidan duniya ne?" Inna ta kufulo itama, ta ce, "To dama ka saba ka min tijara cikin gida gaban kowa akan Hafsa, tun da babu sisinka kasa ido, kuma karatu ba fashi. Ya ce, "To zan ga wanda ke auren wani, tsakanin ni da ke". Ya fita. Na dago ido da hawaye, takaicina ace kullum Iyayena basa rigima sai a kaina, bari Munnir yazo anjima, zan ce masa kawai ya turo manyansa ayi magana, ko ina dakin nasa zanyi karatuna. Ban dai fadi ma Innarmu kudurina ba. Na mike ina tattara kwanukan gabana, Inna kuma sai mita take, na ce "Innarmu ki bar batun haka, kinsan gidan nan da gulma, yanzu kowa ya baza kunnuwa yana sauraro". Ta ce, "Suyi ta sauraro din, ina ruwana. Iyaka dai mace tayi da ni naji mu kwashi 'yan kallo ni da ita". Na idar da sallar isha'i, ina zaune a gurin ina istigfari, wani yaron gidanmu yayi sallama, bai jira amsa ba ya ce "Innarsu Ummi wai ana kiran Hafsa a waje". Ta ce, "To". Na mike, nasan Munnir ne, don na aika masa da letter cewa na dawo. Na bude jakata na ciro turarena forever na fesa, sannan na sabi gyalena na fita. Tun kafin na karaso na jiyo kamshin turarensa. Yana zaune saman motarsa kirar (Toyota camry), baka wuluk, sanye yake da wando jean baki, rigarsa fara. Cikin farin ciki na isa gabansa, nayi masa sallama ya dago da kanshi daga wayar da ke hannunsa yana latsawa. "Babyna". Sunan da yake kirana kenan. Na ce, Na'am". Ya diro "Zo muje cikin mota." Na ce, "A'a mu zauna can". Na nuna mishi dakalin kofar gidanmu. Ya dan gyara tsaiwa, "Kin ce fa baki son Baba ya dinga ganina da kananan kaya, kin san dai in muna can zai ganni dole ko?" Na dan yi jim ina nazari. Hakika Baba na fada cewa Munnir ba dan mutunci ba ne, ya gane haka ne tun daga suturar da yake sakawa. Amma bana son shiga motarsa saboda ya cika son taba jikina.. Ya katsemin tunani da cewa. "Zo muje, na zo da muhimmiyar magana". Na ce masa, "Nima ina da nawa muhimmin zancen". Baya ya bude ya shiga, nima na shiga dayan gefen, sai dai ban rufe ba. Ya ce "Rufo kofar mana". Na ce, "Ka barshi haka ma ya yi. Ya kunna wutar motar, haske ya bayyana, ni da shi muka kalli juna cikin ido. Nayi saurin janye nawa idanun, domin wani abu da na ji yana bin jijiyoyin jikina. Ya ce, "Ina sonki Hafsy, ban san irin son da nake miki ba." Ya kama hannuna na kwace, tare da mai da su baya na ce, "Don Allah Munnir ka daina son taba jikina, haramunne fa". Ya ce, "Zamu fara ko? Haba Hafsy, ni ne fa zan aure ki. Ko yaushe ina son in gwada miki so sai ki yi ta ki, yaya ki ke yi tamkar wacce bata je makaranta ba? Sai ka ce ba *yar boko ba? Ni fa kullum ina fada miki ba zan auri mata muje kina min wani kunshe-kunshen jiki ba. Na bata rai, ya shafi kumatuna. "Small beby, dan yi murmushi. Ba kya yin kyau in kin daure fuska". Shikenan, ban san lokacin da murmushin ya subuce min ba, matsalar ina mutuwar son Munnir. Ya ce, "To fada min maganar kafin kiji tawa, don tawa in kinji saikin bani goron albishir. Na ce, "To ni dai dama ina son ne in ce maka ya dace yanzun muyi aure, don wallahi da kyar Baba ya bari na gama karatun nan. Sam shi ba ruwan shi da da boko, ka dai sani". Ya ce, "Haba Baby, aure fa ki ka ce? Kin manta alkawarin da muka yi ni da ke?" Na ce, "Ban manta ba". Ya ce, "To ki kyale fadan Baba kawai, ba nine ke biyan komai na karatunki ba? Come on aje wannan topic din. Na shirya miki gagarumin party ne saboda murnar gama karatunki, don haka yaushe zamu je kasuwa musai kayan sawa? Takaici ya cika ni, don haka ban tanka ba. Ya sake matsowa in banyi magana ba nasan zai iya cewa zai rungume ni. Da sauri na ce, "Duk lokacin da ka shirya". Ya ce, "Gobe yayi? Dan ranar sati ne party din." Na ce, "Um". Ya ce, "Wai ba ki murna ne angel dina? Kada ki damu, kwanan nan za ki zana (JAMB), sai kin zama *yar media insha Allah. Na dube shi, "Yanzu sai zuwa yaushe zamu yi aure?" Ya ce, "Mun kusa, ai shekara hudu ya rage min na hada master dina, before time din kin zama *yar media ko? Nayi shiru. Ya sake matsowa har muna jin numfashin juna, bakinshi daidai kunnena ya ce, "Kin san ina son aure nima tuntuni damuwa daya Dad dinmu shi ne yaki. Yayyena guda uku suna nan harda mace, kin sani dai ya ce duk sai sunyi master
Chapter 1 · 0% Book details