Sashe 15
Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
SANADIN BOKO 1-5 Posted by ANaM Dorayi on 11:57 AM, 12-Sep-15 Under: SANADIN BOKO Nan dai aka yi dogayen rubuce-rubuce, kowa yasa hannu Daga nan ta tafi. Likita ta dubi shugaba ta ce, " Amma ko da Asaben zata ba su dan su sai an sake zama, don kada suje su halaka shi, kin san mutane ba imani. Shugaba ta ce, wannan ka'ida ne, yanzun ki dauki yarinyar nan ki koma da ita gidanku,gobe zamu je mu samu iyayenta. "Doctor ta ce, Insha Allahu." Washigare suka nufi kauyen kurje, iyayen Asabe sunyi murna da zuwanta, amma da suka ji dalilin zuwan nan suka soma kuka tare da yiwa Asabe Allah ya isa. Asabe na ta kuka, Doctor suka yi ta bai wa iyayen baki tana rokon su yafe ma Asabe. Da kyar suka shawo kan su, sannan suka yi musu bayanin komai game da yanda suka yi da Yasir. Mamanta ta ce, to ni dai ba za ta zauna min a nan va, kauyen nan suyi ta zagina suna yada ni 'yata tayo ciki. Ta sake rushewa da kuka, Likita Hinda ta ce zan tafi da ita in zauna da ita hr ta haihu, in ta yaye sun dauki dansu sai ta samu miji tayi aurenta, ko a nan ne. Maman Asabe tana ta gdy, shi ko Babn tunda yayi waje hr suka tafi bai dawo ba, suka dauko hanya bayan sun ba uwar Asabe sha tara ta arziki. ***** ***** ***** Sati 3 daidai babu alamun cewa cikin jikina zai zube,duk da cewa kusan kullum sai na je gun Likitar, ita kuma sai tayi ta kwantar min da hnkl, wai in jira sati 3n su cika,don ba za ta iya bani wani magani ba tunda aikin wannan bai kare ba. Sam lkcn bn san yaya Asabe take ciki ba, don nima ina cikin nawa tashin hankalin, gara ma Asabe. Bana iya cin abnci,yunwar ma ba jin ta nake ba,karatu kuma ina mantawa cewar shi na zo yi, don ko na shiga aji ba na fahimtar komai, ga laulayi mai tsanani. Munir kuma bai kuma zuwa ba,wayar ma sau 2 ya kira ni, cikin sati 3 da likita ta bani yau kam ko sisin mashin bani da shi, a kafa na sabi hanyar zuwa gidan Doctor. Asabe tare da me yiwa Likita aiki wata gyatuma ana kiranta Yalwa, su na samu. Asabe ta ce min Likita tana cikin asibiti zama nayi don jiranta. Sai uku da rabi muna sallar La'asar ta shigo, da fara'ar ta tare ni tana cewa? na dai san bukata ta biya tunda ban gan ki ofishina ba. Kamar ko yaushe,sai hawaye suka soma zuraro min, na ce wlh Likita ya ki fita, ni dai a kwakule min shi. Ganin tashin hankalin da na shiga, sai ta lallashe ni da cewa, nayi hakuri bari ta dan huta. Na koma na zauna ina kuka,wanda ya zama abn yina koda yaushe, tun da Asabe ta bani lbrn yanda aka kwashe da tata rigima hankalina ya kara tashi. Addu'ata Allah yasa nima kada Likitar ta ce haka za a yi, domin zancen cikin ne sam bana kaunar Innarmu taji bare Babana. Sai shida saura ta fito, na dora sabon kuka Nan ta hau ni da fada,wai in tashi ni tafi kukana ya min magani. Na share hawayena, tare da bata hakuri,ta ce "Hafsatu! Ina son ki bani aron hankalinki, ki saurare ni, na ce to. Ta ci gaba da magana. Cikin nan naki ba zaya fita ba, domin na baki duk wani magani mai karfi,amma a banza. In ko ki ka ce a kwakule shi akwai yiwuwar ki rasa ranki. Da sauri na ce gwara na mutu zan fi son akai gawata ga iyayena fiye a kai ni gaban su da ciki. Ta ce, To naji amma kin shirya abn da za ki fada wa Mahalccinki? Kin mutu gurin kisan kai ko in ce ma kin kashe kanki? Kin fi son kunyar lahira fiye da ta duniya? kada ki manta, kin ce fyade ya miki ko? Na daga kai cikin kuka, ta ce to ki dauki wannan abn a matsayin kaddara. Kada ki manta, Ubangiji ya kan jarabci bayinsa don ya gwada Imaninsu, ke me zai hana ki rungumi kaddara? Allah ba ya dora ma wata rai abn da ba zata iya ba, Zufa ta rufe ni, na ce Likita ba za ki gane ba ne.Innata da Babana auran zai mutu SANADIN BOKONA. Alhakin Babana ne kash! Hakika da na san haka zata faru gare ni da na yarda Babana ya aurar dani, in yaso sai in ci gaba da karatun acan gidan mijina. Likita ta ce, Yanzun dai shawar da zan baki ita ce, kije ki samu shi saurayin ki tunda yana sonki, ku sulhunta, in kin haihu a daura muku aure. In kuma kina son sako hukuma kamar na Asabe to in sako, za su tsaya miki a kwatar miki 'yanci. In ta kama hr kotu kuma ko su waye iyayenshi. Na ce A'a zan fi son in same shi muyi magana don bana son asirina ya tonu a unguwarmu. Likita ta ce, yauwa, in kun sasanta ni kuma zan fahimtar da iyayenki, na rike kai, Boko! Boko!! Na jajirce sai nayi boko,yanzun kuma gashi tun ban je ko ina ba bokon na tsane ta. Likita ta ce, "Hafsaty duk wanda ya dauki boko sama da aure a karshe sai yayi nadama, saboda halin da ki ka shiga ina son ki kwana a gidannan anjima zan baku lbrna, don ki san kinyi kuskure kema." Tara na dare da 'yan mintina Likitar ta shigo sanye da kayan bacci masu kauri riga da wando, tire ne a hannunta dan karami mai dauke da kayan marmari, lemo da ayaba da abarba. Ina zaune zugum kan sallaya Asabe na kwance a tsakar daki ta dubi Asaben "Tashi! "Tashi!! Tun yanzy kin soma bin sanyin kasa? kada na kuma ganinki.Asabe ta tashi, Likitar ta ce In bacci ne ki hau gado mana. Ta zauna bakin gado ta turo mana plate din kayan marmarin bayan ta dauki abarba guda daya dama ina jin bakina babu dadi sai shiga bayi nake ina zubar da miyau Na dauki lemu guda daya ina dan lasa, Asabe ma ta dauka. Likitar ta dube ni Tun ranar da naji lbrnki naji ina son in fada miki nawa. lbrn. Amma kafin na fada miki ina son ki sanar da ni daga ranar da ki ka fara ganina zuwa yau me ya birge ki a tare da ni? Na gyara zama, Na farko iliminki,sai kyan halinki,ga shi kina da kyau,ke ba kya tare da matsala kina da kudi. Tayi guntun murmushi,sannanta dubi Asabe ta ce, Asabe ban yi kama da mai matsala ba ko? Asabe tayi murmushi. Anty ai ke ba ki hada hanya da damuwa ba, bare matsala. ke kam kin ji dadinki. Likita tayi shiru na dan lkc sannan ta ce. "Sunana Hindu, mahaifiyata Bafullatana ce, mahaifina yana da kudi sosai,don lkcn da aka haife ni ma yana matsayin Sakataren Gwamnati. Mun taso cikin daula da gata, haka nan muna da kyau 'yan gidanmu tamkar mu ne muka hallice kanmu. Yayyena 2 maza,sai kuma kannena guda 5. Mu 8 ne gurin mahaifinmu, amma a gurin Mamanmu mu 5 ne, Kishiyar ta ke da 3. Tun da na taso nake da tsananin son BOKO burina kullum in zama Likita,wannan yasa mahaifina ke matukar sona,don shima dan bokon rikau ne. Shi irin matanan nan ne wadanda za su iya hana cikinsu su ba ma boko,takarda komai tsadarta in dai ta boko ce zai siya. Wannan tasa nake zaton dama an halicce ni don nayi Boko. Lokacin da na gama secondary ina da shekara 18, kyawuna ya kara fitowa Nan fa samari suka min ca 'ya'yan manyan mutane,masu kudi da sarakuna.Ni kam lkcn wani faifai na bude na walakanta samari, don in fito in zage saurayi ko dan wanenr baya damuwata.Bana manta wani saurayi Nasir,Babanshi shi ne Gwamnan jiharmu wancan lkcn tamkar zai yi hauka don sona, kullum sai ya zo gidanmu ya min kuka,amma na ce ni fa sai na zama Doctor. Babana ya daure min gindi, ina ta tsulawa samari tsiya. Yayuna maza sukan suna son aure,mma Babanmu ya ce suma ba yanzu ba. Amma shi a wannan lkcn ya sake dallo wata amaryar wadda bata wuce sa'a ta ba.Sam ban damu ba, Su Hjy kam ransu ya 6aci,haka yayuna. Babban sai ya shiga dibn mata yana kawo su wai don Babanmu ya gani ko zaya mishi aure,amma sai Baba ya kira shi yana zagin shi. Abn da in na tuna yake bani mmk lkcn Baba hr d cewa in zya nemi matan shi yaje can ya nema,amma ya daina kawo masa gida. Na ce Alhj fada zaka masa ya daina,ya ce kyale shi Hindu, yaje yayi ta yi,wata rana kan shi zaya bari. Ni dai har na tafi Jami'ar Ahamadu Bello,ba suyi auran ba.Karatu gurina ba sauki,sam bana wasa da BOKO. Shekarata 3 a Jami'a sannan aka yi wa yayuna aure, shima da kyar suna ta hada Babanmu da mutanen da yake jin kunya. Kwanci tashi na kammala karatuna,tsawonshekara 7. Lokacin ina da shekara 25. Saboda kwazona, na samu damar zuwa wani kwas kasar Germany na tsawon shekara 2. Hjyta hr d kuka,don bata son tafiyar burinta in yi aure,amma na kekasa kasa na ce ko na gama karatu sai na fara aiki. Haka kuwa, ina gamawa ban jimaba na soma aiki a babban asibitinmu a matsayin babbar Likita. A lokacin Shekarata 30 babu kadan,sai a wannan lkcn ne hankalina ya dawo jikina. Nayi boko na zama Likita,yau gani inna aiki. Nan fa maza suka sake min ca! amma duk wanda na ta6a babu na aure,sai dai in zan yarda a lalace,daga wanda zai ce in zo in raka shi Abuja,sai me cewa in zo in raka shi Dubai. Da na nuna ba haka nake ba, sai na dinga nemansu daya-bayan-dayaina rasawa,daga karshe duk suka gudu. Lokacin ne kuma idona ya raina fata,wasu suka dan soma zuwa amma fa ba yaro,don ko wani ma zaya girmi Babana, na ce tab, ni kan ai saurayi sabon jini. Kafin shekara na nemi suma tsofaffin na rasa.Bana manta wani dattijo da ya soni na ki, sai gashi ya kawo min wata 'yar