Sashe 5
Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Munnir ya aiko shi muje tare bashi da lafiya. A rude na je na fadawa Inna, ta ce, "Yana asibiti ne?" Duk da ban sani ba sai na ce mata, "Eh." A zatona yana asibiti ne, sai da yaja mota sannan nace, "Wane asibiti ne." Sai ya ce, "Ai yana gida." Har gefen su Munnir Bello ya raka ni, ina shiga sai yace mun, "Toh yana ciki ni na wuce ki fada masa don ya dameni in kawo ki har ciki. Na ce, "Toh!" Na nufi ciki da tafiya cikin dari-dari. Tsakiyar falon na tsaya na zabga Sallama, ga mamakina sai ga Munnir ya fito daga kitchen sanye da gajeren wando da vest duka farare tas, hannunshi dauke da ruwa (C way) yana sha. Na ce, "Ah! Ka samu sauki ne?" Ya ce, "Eh, A'a." Ya nuna min kujera, "Zauna." Na zauna ina kallon shi tare da son jin karin bayani, "Ban gane eh, a'a ba?" Ya tsugunna a gabana, "Ciwon ya dade yana ci na, ga shi zan iya tafiya Makaranta cikin kowane lokaci ba tare da na samu maganin ba." Na ce, "Wane irin ciwo ne?" Ba tare da shakka ki tunani ba ya ce, "Ciwon sha'awarki....." Gabana ya fadi, na mike tsaye da sauri. Shima ya mike, "Hafsat kin san ina son ki, wallahi na gaji da sha'awarki. Ki so ni kamar yanda nike son ki." Na ce, "Munnir ka san ina son ka." Ya ce, "To ki nuna min." Na ce, "Ban gane ba? Sau nawa nake cwa ina son ka? Ka sani." Ya ja tsaki, "Kin dai gane nufi na, ina son yau daya ki taimaka ki nuna kaunarki gare ni." Na ce, "A'a ba zan iya ba, domin haramun ne." Ya ce, "Ni fa zan aure ki!" Na soma tafiya don fita ina cewa, "Sai ka jira sai ka....." Maganata ta tsaya sakamakon murda kofar da naji nayi ta a rufe gam. Na dube shi yana murmushi ya ce, "Ki bani hadin kai don yau ta karfin tsiya ma zan iya biyan bukata ta." Jikina ya soma bari na ce, "Wallahi Munnir zan maka ihu, ka bude min kofa." Ya zauna, "Ko kin yi ihu ba wanda za ya ji ki. Mom bata nan tana gurin aiki, Dad ma haka, su Nana da Suhaila suna Makaranta." Na zube gwiwoyina biyu a rude ina cewa, "Ka min rai kada ka sa ni cikin matsala, don Allah." Na soma kuka. Ya ce, "Nima ki taimake ni na gaji, wanene za ya gane me muka yi?" Na ce, "Allah ya sani, na tabbata zai kama mu." Amma da yake Shaidan ya hura ma Munnir kaho sam ya ki karban uzirina. Muka yi ta zaga falon har na fada wani daki, sai dai kafin na rufo tuni ya banko, mun yi damben bala'i dashi kafin ya samu nasarar aikata mummunan nufinshi a kaina, bayan ya bi duk wata gaba ta jikina ya bugeta, fuskata kuwa ta sha mari sai na ga kamar ba Munnir dina ba. Kuka iya kuka na yi shi, na mike ina gyara daurin zanina, da kyar nake tafiya na fito falon, ya ce, "Duk kin sa mun wahala, a yanzu wa zau sani in ba kin fada ba?" Na ce, "Bude min kofa kawai ni dai na tafi." Ya nufo ni, "Come on kiyi wanka sai na kai ki." Ban san lokacin dana daka mishi tsawa ba, "Budeni mana" Sabon kuka ya kwace min na ce, "Allah ya isa tsakani na da kai, Insha Allahu sai Allah ya saka min." Ya tashi ya bude tare da cewa, "Sai na zo." Ban kulashi ba na fita, dole na share hawayena saboda Maigadinsu, na fita ko ina a jikina ciwo ya ke. A haka na kai gida, kallo daya Inna ta min tace, "Lafiya?" Jikina ya soma bari, ta ce, "Ba dai jikin nashi ba? Na ga duk kin rude fuska a kumbure." Na ce, "Umm jikin ne." Ta ce, "To shine na kuka? ki masa addu'a." Na ce, "To." Na nufi ciki. Ta ce, "Hafsa zo nan, menene wannan a zaninki?"mummunar faduwar gaba ta ziyarce ni, zufa kuma ta shiga keto min, amma sai na yi saurin cewa, "Fashin Sallah ne." Duk da ban juyo ba kuma ban san mai ta gani jikin zanin ba. A gani na in muka hada ido zata gane, ta ce, "Haka kika ratso titi? Ga ruwa da na daura chan kan wuta na tuwo ki diba ki maida min sai ki dauraye jikinki." Cikin bayi ina wanka ina kuka tausayin Innarmu ya cika zuciyata, na karya alkawarin da na daukar mata, Allah ya isa Munnir. Cikin kwanakin da suka biyo baya ko Munnir ya zo bana fita, ranar da zan koma Makaranta har goman safe ina kwance a tsakar daki, Innarmu ta ce, "Ke da naji kina cewa sammako zaki yi? Har yanzun kin kasa tashi?" Na ja tsaki, yanzun na soma tsanar boko bani da daman in tona asirina... Yaron gidanmu ya shigo ya ce, "Hafsa wai in kin shirya wani mai mota ya ce ki fito yana can saman layi." Na ja tsaki, "Ka ce masa ya tafi na san hanya." Innarmu ta ce ma yaron, "Kai zo, je kace tana zuwa." Yana fita ta fara min fada wai bani da hankali, ta lura kullum zai kirani in 'ki fita, haka ake yi? In ma sabani kuka samu ba sai kiyi hakuri ba tunda shi har ya zo? Na kalli Innarmu a zuciya na ce, "Da kin san abinda ya min sai kin fini tsanar shi." Ban ce komai ba na ci gaba da shiri. Inna ta kwance habar zaninta kudine 'yan hamsin hamsin dubu uku na adashena na kwasa, sannan cikin robar can tumatir ne na tafasa shi ga sabulu can inji Baabarki..... Na ce, "Ki bar kudinki." Ta ce, "A'a na dai baki ne, amma badan zasu ishe ki wani abu ba ne. Yaron nan dake dawainiya da ke Allah ya gwada min aurenku." Yana zaune yana latse-latsen waya ya diro, "Gimbiyata, amaryata har yau fushi kike da ni? Gashi doguwar tafiya za muyi? Don Kano zan kaiki." Ban tanka shi ba ya amshi robar hannuna da leda ya daga but ya sa. Ni dai tamkar na haushi da duka nake ji, ya bude mun gaba na shiga don bani da yadda zan yi. Tunda muka dau hanya yake mun magana amma ban tanka shi ba. Ya ciro waya daga gefen shi ya ce, "Ga wayarki." Sai lokacin na yi magana, "Bana so." Ya daurata kan cinyarshi, "Dole ki so ta Hafsat don in na tafi karatu ta yaya zan dinga jin muryarki? Ki saki ranki, abun da ya faru ba wata matsala bace saboda ni zan aureki..." Na zabga mishi harara tare da cewa, "A ganinka kenan, amma ni addinina bai yadda don zaka aure ni kayi ZINA dani ba." Ya katseni, "Ki daina cewa Zina." Na daga murya na ce, "Ka biya sadaki na ne? Iyayenka sun nemi aurena gun iyayena ne an basu? Ko jama'a sun shaida." Ya ce, "Ba daya." Na ja tsaki ban kara tanka shi ba har muka kai. A dakinmu ba yadda bai yi ba na'ki tankashi, ya aje mun kudi da waya ya tafi. Na saka kuka nayi ma ishi na, tunanina in Allah bai yi aurena da Munnir ba fa? Ya sakani cikin matsala kenan don ban san mai zance ma mijina ba yayin da yace ina nakai budurcina? Dole in dauki hakuri in lallaba Munnir ya aureni. -Yana kiran wayata sosai, tun ina sharewa har na hakura don ban san yadda zan yi ba, sai dai bashi da wata daraja ko kima a ido ba, ko na aureshi gani nake ba zan girmama shi ba, tunda na ga irin nashi rashin Imani. Sai mene? Tun jiya sha hudu ga wata ya dace in ga al'adata amma har yau sha biyar shiru. Wannan ya tilastamin shiga rudani. Dora John dakinmu daya har ta gane ina da matsala ta ce, "Hafsy yaya ne?" Na ce, "Ciwon kai ne." Ta bani panadol da sauri na sha don kuwa kan nawa na ciwo. Kwanaki uku suka biyo baya gashi banji daga Munnir ba cikin 'yan kwanakin, naje na sai kati na kira shi, yana dagawa na soma kuka, ya ce, "Mai ya faru?" Na ce, "Banga period dina ba yau kwana uku." Ga mamaki na sai na ji bai damu ba ya ce, "Zan shigo wannan ba wani abun damuwa ba ne." Washegari sai gashi da wani abokin shi, yana shigowa na soma kuka nan take ya bata rai, "Kukan nan ya soma isata, zan barki ki karata in dai ba zaki daina mun kuka ba." Abokin shi Bello ba karamin tsanarshi nayi ba har da cewa, "Daga sau daya sai ciki?" Munnir ya ce, "Nima dai nayi mamaki bata fa tsaya ba ma, gaskiya in anyi bikin mu juya Mahaifarta za'ayi don bana son yara su wuce biyu tsanani uku." Tsabar bakin ciki ya hana ni tankasu, ni dai burina ya san yadda zai yi dani. Bello ya kira wani abokin shi anan Kano wai shi Nasir, ya zo suka tafi suka yi magana sannan suka ce inzo mu je asibiti. Mun shiga office din Likita mace 'yar kimanin shekara arba'in tana tsaye da farin gilashi, ta tsareni da ido bayan duk mun zauna ta kalli Nasir, "Me ke tafe da ku?" Duk muka yi shiru, Munnir ne mara kunya shine ya ce, "Mun kawota ne bata ga period dinta ba, so muna so a gwada ta." Ta tsareshi da ido, "Kanwarka ce?" Ya ce, "Budurwa ta ce." Bakin ciki ya cika ni, na sunkuyar da kai ina hawaye, "To ku dan bamu wuri." Suka fita. Ta zabga min harara, "Kin bashi kan ki ko?" Murya ta a sarke na ce, "Wallahi...