Sashe 34
Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
shi ya tsaya kusa da ni, "Ki yi hakuri kin ji ko?" Sannan ya fita.Ni kam ban ko kallesu ba. Tunanina 1 ina ya kai min yarona? Lokacin tashina nayi na nufi Makarantar su Shadad na dauke shi muka nufi gida. Tun akan hanya ya isheni da labarin Uncle, Anty Uncle ya sai min ice-cream ya kai min da muka yi break da su sweat, kuma ya tambayi Auntynmu wai ina karatu? Ta ce mishi inayi sosai, kuma ana lura dani wurin yin home work, yana ta jin dadi. Na yi tsaki tare da cewa, "Yi min shiru." Da dare ina Sallar Isha'i naji bugun gida, sai da na idar sannan na nufi zauren nace wanene? Ba'ayi magana ba har zan juya aka sake bugawa nace wanene wai? Yace Abubakar ne. Na gane muryarshi amma sai nace, "Wa kake nema?" Ya ce, "Shadad." Na yi shiru ina nazari, hausawa sunce mai Da wawa, inna bar wannan mutumin zaya fake da dana ya cutar da ni, gara in masa rashin mutunci ko ya fita daga harkata. Na bude kofar sannan na dogare bakin kofar, "Kai Malam! Ka fita idona, ina ganin kimarka bana son ta kaimu ga rabuwa fata-fata ni da kai, ina nufin in zabga maks rashin mutunci, ka ja tsumman rayuwarka ka yi gaba, ka fita harkar yarona, anzo za'a fake da yaro a cuceni." Na ja tsaki tare da maida kofar garam na barshi tsaye da leda shake da kaya. Daga ranar ban kuma ganinshi ba, hakan ya min dadi don haka na godewa Allah. Sai dai damuna da Shadad keyi na kiran Uncle har da kuka. Kwana 8 bayan haka ina ta kici-kicin girkin rana, yau lahadi sai da yamma zan fita aiki. Tuwon shinkafa miyar alayyahu nake son mana na gama kwashe tuwon cikin leda na zuba a kula na samu Shadad yana home-work na ce, "Yauwa ka zauna zanje kasuwa in dawo." Daman nakan barshi. Ya ce, "To Anty." Ya tashi ya dauko kujerar da yake takawa yasa sakata ta ciki. Na nufi kasuwar don ba nisa sosai. Ban fi minti 30 ba na dawo, sai dai me? Kofar gidan a bude, haka na nufin Shadad ya cire sakata, a hanzarce na shiga. Takardun shi suna gurin, takalminshi suna gurin. Kaf babu inda ban dyba ba cikin gidan amma ban ganshi ba, da hanzari na nufi makota duk da na san baya zuwa,,,,, Me ke shirin faruwa da nine? End of 1
Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100
Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100