← Book details Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 34

Sashe 19

Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

in zauna can gidan Likitar, ko Inna ba zan fadawa ba in na haihu sai muyi aure." Ga mamakina sai na ga yana dariya, a zato na zancen ya masa dadi, kuma shawara ta ta shige shi. Amma sai naji ya katse tunani na da cewa, "Amma ban taba sanin baki da hankali ba sai yau. Kina zaton ko aure na yi yanzun nan da shekara goma zan haihu?" Ya girgiza kai, "Ba zan haihu ba, saboda haka dole ne a cire wannan cikin, in kuma kin dage to kije can ki nemi Uban danki." Da sauri na dube shi, "Munnir ka san me kake fada?" Ya ce, "Eh, ina da ja kan wannan cikin, cewa nawa ne. Daga sau 1 shima ba cikin kwanciyar hankali ba amma shine ciki zai shiga?" Bakin ciki ya hana ni magana, idanu kawai na tsura mishi, shima ni yake kallo cikin harara gami da daure fuska. Na ce, "Allah ya sani ni ba mazinaciya ba ce,,,,,,,,," Kuka ya kwace min, "Kai ne ka soma keta min mutuncina, ka raba ni da 'yan matanci na, yanzun kuma ka bini da sharri. Allah ya isa tsakani na da kai." Ya matso kusa da ni, "Zan mare ki in kika zage ni, banza butulu. Duk taimakon da nayi miki da kokarin da nayi miki amma kin kasa gode min, shashasha, Kin zata zan kashe miki kudi a banza ne tsawon shekaru? Ki sani in kin ga kare yana shinshina takalmi to dauka zai yi, ni ba ajinki bane don ki sani." Kuka mai karfi ya kwace min, "Allah ya isa Munnir, dama yaudarata kake yi kace zaka aureni?" Ya yi 'yar dariyar mugunta, "Kin dai yaudari kanki, to ai ni ne ma zanyi Allah ya isa tsawon shekara 3 zuwa 4 ina miki bauta ke da me kika taba saka min?" Ban san lokacin da nayi kukan kura na shako wuyanshi ba ina kuka ina cewa, "Allah ya isa." Shi kanshi yayi mamakin yadda ya so kwacewa daga jikinshi ya kasa.Muryar Mom dinsu muka ji tana cewa, "Lafiya? Ke, ke sake shi mana me ya faru?" Na kasa magana sai wani irin kuka nake yi ina fadin, "Ya cuce ni." Ta dubi Munnir, "Me kayi mata?" Ya ce, "Ban fa ko sanya ba daga aiko ta gurina ta shakeni wai na mata ciki." Wani kallo Mahaifiyarsa ta watso min sannan ta nuna ni da yatsa gami da cewa, "Ke! Shiga taitayinki, tafi can ki nemi wanda ya miki ciki." Cikin tsananin kuka na ce, "Wallahi shine ya min fyade. Kuma da shi muka je asibiti Likita ya ce ina da ciki." "Ke!" Ta kara daka min tsawa, "Fita a nan." Na ce, "Nifa ba inda zani sai dai ya san yanda zayayi da ni......." Saukar mari na ji, sannan ta ce, "Fita ko in kirama Iyayenki 'yan sanda." Ta fita da sauri tana kiran Baba megadi, ya iso ta nuna mishi ni, "Baba fita da wannan bana son in kuma jin ko labarin an ganta a layin nan, in haka ta faru har da kai zan hukunta." Ya dubeni ya cem "Mu je." Na tsaya ya ce, "Shige mu je mana ina magana kina kallona." Na dago jajayen idanuna na kalli Munnir, wani murmushi ya saki na mugunta sannan na ce, "Akwai Allah." Na fita megadin yana biye da ni sai da muka fito ya ce, "Yarinya kin yi kuskure, koda ban san abinda ya faru ba, amma na san yana da nasaba da abinda yayi ta faruwa da wasu 'yan mata a gidan nan." Na dube shi, "Baba me ya faru da wasu 'yan matan?" Ya ce, "Samarin gidan nan da abokansu suna kawo 'yan mata ta hanyar yaudararsu da kudi, su yi lalata da su." Na dube shi bayan mun fito wajen gidan, "Baba ni nawa salon yaudarar ya bambanta da na saura
Chapter 19 · 0% Book details