Sashe 23
Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
kenan, don haka yaro ya ci suna Shaddad. A hankali na rinka jin kaunar yaron tana shigata, sai dai kullum kamanninshi da Munnir kara bayyana take, ban ta6a ganin da mai tsanabin kama da ubansa ba irin haka. Zuwa yanzun zcyt ta dake,watanmun 3, Wata rana Doctor Hindu ta zo mana da lbr mai dadi, wai ta samu miji, tsohon ministan ilimi na kasa. Muka yi ta murna, ita kam har da Azumi 2 don nuna godiya ga Ubangiji. Sati 4 aka sa bikinta, mu ne har Katsina gidansu. 'Yan uwanta da take bamu lbr duk mun gansu,ita ce ta dinka mana ankon dinner. Ranar daurin aure da dare aka yu dinner. Sam na kasa sakewa,saboda kallon da maza ke min, duk da yaron da ke kafadata. Ni kuwa yanzu duk namiji da zai kalle ni ko da bisa rashin sani ne ai bn da makiyi kamar su. Mun sha biki,sannan muka dawo,mun samu gidan yasha gyara,an zuba komai sabo,shi yana zaune a Abuja da Iyalansa, amma ita zata zauna a gidanta saboda aiki. Ada na cika wasa da tsokana ga son raha, amma yanzu na koma miskila,masifaffiya, mara fara'a.Bugu da kari yanzu ba ni da tsoro, musamman akan namiji. Kwanci tashi hr Asabe ta yaye 'yarta, kuma tuni an kaita gidan su Yasir. Bayan hukuma ta shiga batun don kare lafiyar yarinyar. Sannan ta samu miji a can kauyensu, mun je har can bikinta garin da aka kaita ya dan fi kauyensu zama birni. Ni kam kullum cikin yiwa Likita naci nake, ta samar min aiki ko na gida ne, ta ce an gudu ba a tsira ba, dubi abin da ya faru da Asabe sanadin aikin gida. Cikin satin da muka yi wannan maganar tazo min da lbrn cewa ta samo min aiki a wani Super market, amma da nisa tsakaninsu da unguwarmu.