← Book details Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 34

Sashe 2

Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

sun fara aiki balle ni. Na ce, "To sai yanda Innarmu ta ce". Ya ce, "Bana jin Inna, zata yarda". Ya sake yin kasa da murya "In dan yi kissing din kunnenki?" Naja baya tare da cwa, "A'a". Ya ce, "To bari na tafi". Yana magana yana kallon agogon hannunshi, "Zan kalli wasan Arsenal yau." Na ce, "Kai kam har yanzu kana nan da kallon kwallon nan." Ya ce, "Kema za ki koya in kinzo gidanmu". Nayi dan murmushi. Ina son Munnir, shi yasa zan jure na jira shi, amma Allah Ya sani ina son aure, don ina zaton ina cikin mata masu bukata.... Ya katse tunanina da cewa, "Ko kada in tafi ne?" na ce, "A'a kaje sai gobe". Ya ce, "Shikenan." Ya miko min wata farar leda. ""Gashi kisha, ice cream ne da fresh milk." Na ce na gode, amma don Allah ka daina yimin irin wannan dawainiyar. Innarmu ta dubi ledar bayan na ciro kayan ciki, ashe har da kayan tea. Ta ce, "Kai yaron nan baya gajiya da dawainiya. Ni da zai fito ayi auren nan tunda yana zon karatun kyayi can a dakin shi. "Inna nayi mishi wannan zancen ya ce min in kara hakuri." Kamar na fadawa Inna zancen party din gobe, sai na fasa don nayi imani ba zata barni ba, duk da tana son abinda nike so. Yau Baba dakinmu yake, don haka dakin Babah kishiyar Innarmu zamu kwana. Ina kwance kan yaloluwar katifata mu da Sakina, can kasa sauran kannena da aka musu shimfida. Ko wannan cakudin na daga cikin abin da yasa nake son in ganni a dakin kaina. Washe gari tun safe muka soma aikin alalar siyarwa da Innarmu ke yi. Misalin uku saura Nazifi ya shigo yana cewa, "Hafsa ga saurayinki a waje. Ko da bai ce na kira ki ba, nasan gurin ki ya zo. Dama tuni nayi wankana, ina sanye da riga da siket na atamfar (Java), gyale na sura na ce "Inna Munnir na kirana." Ta ce, "To." Na nufi waje kai tsaye. Yana sanye da kananan kaya kamar ko yaushe, ina isa ya budemin gaban motar na shiga, sannan shima ya shigo. Na gaida shi ya amsa tare da yiwa motar key, na ce, "Muyi sauri ban ce zamu fita ba." Ya ce, "To". Wani (Boutique) muka je, duk tsinannun kaya ne a gurin, shi dai ya zabi nashi, amma ni nace ban ga wanda ya yi min ba. Nan ya shiga jidar min, na bata rai tare da nuna mishi sunyi yawa. Ya ce, "To zabi wanda ki ke so." Na daga duka babu na arziki, siraran wanduna ne da *yan riguna, sai doguwar riga wadda in nasa da kyar zata wuce gwiwata. Na aje su gefe, na dube shi. "Duk ba su yi min ba". Ya bata rai sosai, "Tashi muje". Na kafa mishi ido. Ya ce, "Tashi mana". Cikin daga sauti na ce, "To, to naji zan amsa, amma ni na gane kamar zasu yimin kadan." Ya dan sassauto "Muje gidanmu ki gwada." Da sauri nace, "A'a zasu yi min." Yayi murmushi, sannan muka je ya biya muka shiga motarshi. Ya ce, "Muje mu dan sha Ice cream". Na ce, "A'a kai ni gida, Innarmu bata san na fita ba, kuma nasan zata sa a leka ni, fada kuma zata yi min". Ya ce, "To naji sarkin tsoro, ke dai kawai kina tsoro ne kada na cinye ki." Gabana yayi muguwar faduwa ganin Baba zaune a dakalin kofar gidanmu, na ce na shiga uku, ga Babana, ya ce "To menene? Ina jin mamakin ki wallahi. Shi yasa Dad din mu yake matukar burge ni, baya takura mana, shi dai in dai zamuyi karatun boko to duk abin da muka ga dama muyi. Kuma zai kashe mana the last kudin shi don muyi karatu. Na ce, "Uhm, don Allah ka tafi da kayan, na karba, amma ka fito ku gaisa. Tare muka fito daga motar, jikina har bari yake. Na nufi cikin gida, Munnir yayi gurinshi. Ina isa Inna ta ce, "Daga ina ki ke Malam ya shigo yana ta fada yaga lokacin da ki ka shiga mota? Na ce, "Um asibiti muka je dubo kanwarshi". Ta ce, "Shi ne ba za ki fada ba? Kin san fadan Malam, don Allah ki rufamin asiri kada ki ja min surutu sanadin bokon nan." Na ce, "Kiyi hakuri Inna." Ina rufe baki Babanmu yana shigowa, tun kafin ya karaso na jiyo muryarshi yana cewa. "Na fada maka kenan, in da gaske ka ke yi ka turo min manyanka. Shekara nawa ina ganinka a kofar gidan nan wai ku *yan boko, zaku ce min sai kun gama boko, to ban laminci wannan ba." Hanyar uwar daka nayi, don nasan yanzun ya make ni, ya ce "Ke *yar boko kinbi saurayi kasuwa ko? Inna ta ce, "A'a Malam asibiti fa suka je." Ya zaburo tamkar zai kai ma Inna duka, ya ce, "In ji wa? Wa ya fada miki?" Inna ta ce, "Ga ta nan." Ya ce, "Makaryaciya, to shi abokin yawon nata ya ce min daga kasuwa suke, duk ya rasa wanda zai ce ya raka shi kasuwa sai ke?" Inna ta tsare ni da ido, "Kasuwa Hafsa?" Nace, "Kuyi hakuri, ba zan kara zuwa ba." Tayi kwafa tare da ci gaba da yin aikinta. Baba ya ce "To wallahi ba zan yarda da gantali ba, wai ku *yan boko." Inna ta dube ni, "Ai gara ki saka min da haka. Tunda ni na jajirce ki samu karatun boko." Na ce, "Don Allah Innarmu kiyi hakuri, wallahi ba zan sake ba". Ta ce, "To me yasa ki ka min karya? Kin san dai na tsani a min karya, duk abin da ya faru nafi son gaskiya ko?" Na ce, "Na sani. Haka nayi ta bata hakuri, kun san Uwa, nan da nan ta sauka. Ta min fadan cewa kada na sake yarda na bi saurayi wani guri. Kwana daya, biyu ban ji daga Munnir ba, lallai Babane ya kore shi letter na rubuta na ba Nasirun gidanmu na ce ya kai masa. Tambayarshi nayi ko lafiya? Na jishi shiru. A bayan takardar ya rubuto cewa Babana ya kore shi, don haka shi ya hakura da ni. Na girgiza da jin wannan zancen, don ina son shi kullum burina na aure shi. Shi kadai nake jin sha'awa. Na rasa yanda zan yi ko satar jiki zan yi na je gidan su? Innarmu ta gane ina cikin damuwa, ta ce "Hafsat ba ki jin dadi ne? Na ce, "Ciwon kai ne yake damuna." Ta bayar da Naira goma a amsomin panadol." Da dare nace Innarmu zan je gidansu wata yarinya *yar makarantar mu, in amso wasu takarduna, ta ce, "Kar ki zauna, maimakon kije tun ido na ganin ido?" Na ce, "Ai dazun ciwon kai ke damuna." Ban yi wata kwalliya ba, kada ta gane, sai kawai na dan fesa turare. Na zari mayafi, gidan su Munnir da dan tafiya tsakanin mu saboda mu muna Rigasa ne Abuja Road ta kasa, su kuma suna Makarfi Road. Tun daga nesa na hango shi su da wani tsaye, ga motarshi gefe, ina zaton fita zasu yi. Sai na kara sauri. Daidai ya bude motar zai shiga na ce, "Munnir" Ya juyo da sauri, ya mai da motar ya rufe. Abokin nasa yana ciki, ya ce, "Beby lafiya?" Na jingina da motar, sannan na sauke ajiyar zuciya, domin na gaji. Sai dai kuma lokacin ne naga rashin hankalina. Yanzun ince mishi me? Na zo in bashi hakuri ko nazo biko? Ya sake cewa, "Me ya faru Baby? Na ce, "Ai ba ka ma sani ba?" Dabara tazo min, na ce "Dama nazo ne na maka godiya akan dawainiyar da kayi da ni, don ko zamu rabu bai dace mu rabu ba zumunci ba." Ya ce, "Baby kenan, don na fada kina ganin zan iya rabuwa daKe? Ni ina sonki, Babanku ne ya tozarta ni" Kafin nayi magana ya ce, "Ina zuwa." Ya leka motar yayi magana, sannan ya ce, "Zo muje ciki kiji." Na ce, "A'a. Ya bata rai, "Bana son yawan gaddamar nan, ki daina kada muyi aure mu zo muna samun matsala. Na ce, "Ina jin kunya ne, saboda Mamanku, Ya ce, "Ba za ta san kin shigo ba, zo muje. Na bishi, ya tura Gate din gidan, muka shiga. Yau ne na soma shiga gidansu, ginin zamani ne ga haske tamkar rana, me gadinsu ya ce, "A'a, ka fasa fita dinne? Ya ce, "A'a Baba, yanzun zan fita. Na gaida maigadin muka tafi ginin farko daga cikin gine-gine ukun da ke harabar gidan, ya ce, "Yau kin zo gidan mu, ba don kunya ba da na kira miki kannena su Nana. Na ce, "Barsu yanzun zan tafi, kuma bai dace su ganni cikin wannan yanayi ba, ina nufin shigar da nayi. Ya ce, "Shikenan. Katon falo ne, yana dauke da kayan more rayuwa, sai kofofi guda uku, yace in zauna kan kujera, na zauna. Ina kallon ko ina, ya nufi kofa daya daga cikin kofofin, jim kadan ya fito dauke da gwangwanin maltina da kofi ya zauna hannun kujerar da nike
Chapter 2 · 0% Book details