Sashe 27
Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
zabga min harara sannan ta ce, "Ai wallahi Hafsat kina bani haushi, ina lura da ke duk matse-matsen da kike yi cikin satin nan, har ta kai baki da abinda za ki ci amma ba zaki iya tambaya ba? Ni kam ko yaushe gidan ki nake cin abinci, saboda ina daukarki 'yar uwa ta jini." Na ce, "Rahma dama ni dake ai babu wani bambanci duk daya ne." Tsaki Rahma taja, sannan ta dora min dari 5 kan cinya, zan yi magana ta ce, "In kin ce tak Allah ya isa." Da kallo na bita har ta fita sannan na saka dariya, Rahma kenan. Karatuna ya shiga wani hali, har ina ganin in ba wani ikon Allah ba tsayawa zaiyi. Cikin wannan matsatsi aka sa ranar auren Rahma da Sagir, kullum tunani na me zanyi ma Rahma lokacin bikinta? Da dare Rahma tana min kitso muna hira na ce, "Rahma kin san me nake tunani?" Ta ce, "Kudin Registration?" Na ce, "A'a, so nake ki fadi abin da zan miki lokacin biki." Cikin tsokana ta ce, "Italian bed da leader sit." Muka sa dariya, na ce "Allah ya hore, har kayan kicin sai na miki." Ta ce, "Ni dai Hafsat nafi son ki bada hadin kai lokacin bikina kin ga dai bani da wata aminiya sai ke, sauran duk kawaye ne." Na ce, "Tabdijan! Rahma kada ki sani yin abinda ba zan iya ba." Ta saki kaina, "Kin san Allah?" Ta nuna ni da kibiya, "In bikina ya yi kyau ke ce in ya baci ke ce, kuma yanzune zan san matsayina a gurinki." Na ce