Sashe 29
Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sanadin Boko 1-8 Posted by ANaM Dorayi on 12:13 PM, 18-Sep-15 Under: SANADIN BOKO , "Maida wukar, Allah ya kaimu. Yauwa dama ina son in miki batun da ke raina. Ina son in samu manaja ya bani koda rabin albashina ne in sai ma Shadad takardu." Ta ce, "Kin san rashin mutuncin sa, abinda zai fi dai in tambayar miki rance gurin matar Yayana." Na ce, "A'a ki bari zan same shi in yaga dama zai yarda." Rahma ta ce, "Hafsa kenan, ke bakya son bashi sam! Kuma ai naga bashi hanji ne yana cikin kowa." Na yi 'yar dariya. Haka kuwa na yi, na samu manaja da bukata sai ya ce, "Kin cika daure fuska, da ace kina da fara'a har karin albashi zan miki. Banda kyautukan da zaki yi ta samu a kai-a kai." Na sake hade fuska, "Bana bukatar karin ko wata kyauta. Hakkina kawai nake so." Ya ja tsaki, "To sai ki jira lokacin baki hakkin ya yi, ke bazaki taba ganewa ba. Wai me ma zakiyi da kudin?" Ban amsa shi ba har sai da ya sake maimaita tambayar, Na ce, "Zan biya kudin littafan makaranta ne na yaro."Ya yi tsaki, "To sai ki jira lokacin don in kin ga na yiwa mace mutunci itama ta yi min ne." Na mike ba tare da na sake magana, don Manzon Allah ya ce ka fadi alkhairi ko kuma ka yi shiru, amma na so in zabga masa ashar in ya so ya kore ni gaba 1 daga aikin. Cikin kwanakin sai manaja ya soma shige min, duk da dinke fuskar da nayi masa, ya zo ya kawo min albashina wai gashi nayi bukatar da zan yi, na ce ya barsu ai ni na ma hakura. Kwatsam! Rannan sai naji ana buga min gida, lokacin 9 ta gota na dare, don har na soma bacci. Na zo na bude, nayi mamakin ganin manaja a gidanmu na ce, "Lafiya?" Ya ce, "Kalau, na zo ne mu gaisa." Na ce, "Na gode da gaisuwa. Sai da safe." Na juya ya ce, "Kina nufin har mun gaisa? Bai dace ki yi min haka ba." Na ce, "Za a min fada an hanani fita." Na fadi haka da nufin karema kaina mutunci. Ga mamakina sai naji ya ce, "Haba yarinya, ni zaki yi wa karya? An ce miki bansan cewa zaman kanki ki ke yi ba? Ni zaki saki jiki ki ci arziki ki saki, in ba zaki saki ba talauci sai ya yi ajalinki." Jikina ya yi sanyi lakwas, na maimaita kalmar zaman kaina! Na ce, "Ni ce mai zaman kaina?" Ya ce, "Sharri na miki? Kowa ya san ke kadai ce ba kuma a san iyayenki ba." Ya ja tsaki tare da cewa, "Banza mara rabo." Ya tafi. Ranar na yi kukan da ya isheni, wato kowa ya san zaman kaina nake? Wata zuciya ta ce, "To yanzun ai an daina kiwon dabba mutum ake kiwo." Sai dai da mutane zasu min adalci ya kamata su san cewa bana hulda da maza, da ace ina da wani aikin lallai zan bar super market din nan, sai dai bani da zabi. Da safe duk da kirkiro fara'ar da nike yi sai da Rahma ta gane cijewa nake yi saboda damuwar da ke raina. Ta kafa min tambayar me ke damuna? Nanfa na fada mata, na kara da cewa, "Dama duk mutanen unguwar nan kallon da suke min kenan? Ina zaman kaina?" Rahma cikin muryar lallashi ta ce, "Sam, shi dai yabi diddigi ya ji cewa ke 1 ce anan. Amma ba maza kike tarawa ba, kowa yana yabonki a unguwar nan don kin tsare kanki, kuma shi ya fada hakane don takaicin bai samu abinda yake so ba. Ki barshi da Allah." Nace, "To in ban barshi da Allah ba yaya zan masa? Ai bani da yanda zan yi dashi. Da ace ma ina da wani aikin barin musu wurinsu zan yi." Rahma ta ce, "To ai ba gurinshi ba ne shima cin arziki yake yi, don haka ba inda za ki je." Daga wannan lokaci muka sa 'yar tsama da shi, ya bi duk ya tsane ni, nima kuwa ya kara dasa min tsanar maza, yana son ya ga nayi wani dan kuskure ya tozarta ni, niko duk wata hanya da zata ja min cin mutuncin shi na 'ki sakaci da ita, lokacin zuwa aikina baya cika nake isowa, musamman in zuwan safe zan yi. ******** ******** ***** Munnir an kammala karatu an kuma dawo gida. Tuni ya manta da wata Hafsa da labarinta. Ya iso gida cike da soyayyar Mina, yarinyar wani kusa ce a gwamnati, sun kulle ne tun a yanar gizo ta (Facebook), sun jima suna soyayya kafin suga juna, bayan ya zo hutu itama ta dawo daga inda take karatu, suka hadu. Sun yaba da juna, sai dai sanin cewa ba za ayi musu aure da wuri ba suka kazanta soyayyar su ta hanyar biyan bukatar zukatansu. Sam! basu dauki hakan laifi ba, nasu ganin duk cikin soyayya ne a nasarance suke koman su don boko suka sani, shi suka iya, kuma shi suke yi. Sun dai kulla alkawari ga junansu cewa za suyi aure in lokacin yinsa ya zo, Allah ka shirye su shirin Addinin musulunci. (Ameen). ¤¤¤¤¤¤¤¤¤ Bikin Rahma ya gabato don haka na ciro dubu goman da na makale na ce mata na ba da rabin kudin Registration naje nasai mata sestin kula da jug. Dubu bakwai na kashe, nazo na kai mata gida, batan hakan ya min dadi. Su Mama suna ta gdy, ta ce yanda garin nan babu kudi shi ne zaki ta wannan dawainiya har haka? Na ce Mama ta kama ne. Da dare ina krtn Alkqur'ani,sai gata ta ce, Yayi kyau Hafsa, ina kika samu kudin sayan kayan ban masu tsada?Na ce Daga Sarki Allah. Ta ce, ba dai kudin Registration din ba ne? Na ce in sune fa? Don Allah zo ki zauna muyi batun anko. Ta ce ba zama nazo ba ki zo in ji Sagir da wani abokinshi, ki fada musu kudin abubuwan da zamu yi. Da karfi na ce " What? hum........ hum..... Rahma kada ki sani cikin hulda da maza. kije kawai ki amsa, na yarda zamu je kasuwa siyayyar tare. Zata yi mgn na rantse mata da girman Allah cewa ba zani ba, ta juya ba tare da ta ce kala ba. Nasan tayi fushi, amma sam fushinta bai dame ni ba, in dai akan abin da zai sa nayi hulda da maza ne har nai musu dry. Don ni nasha alwashin namiji ya gama ganin hakorina. Mun je kasuwa, duk abn da zamu bukata gurin walima mun sayi, don Walima kadai zamu yi kayatacciya, sai dai ta ce, Sagir za suyi (Dinner) kuma za su yi (Pink & blue day). Kullum rokona take in je har dai na amsa mata zani. hakan ya tilasta min siyan shadda kamfala (pink) mai ratsin bulu,yayin da Shadad na dinka masa(blue) din shadda, atamfar walima kuwa Rahma da kanta ta sai min., Bikinmu yayi kyau, komai a gidana aka yi duk da cewa ina zuwa gurin aiki da mkrnt, kin yi wa Manaja mgn nayi don ba zan sake yi mishi wani zance ba, ko neman wani abu. Ranar daurin aure kam ban je makarantaba, kuma banje aikin ba, saboda aubuwan sun kwa6e min. Malamai sun halarci walima, sun kuma yi nasiha akan mahimmancin yin aure tare da falalar da ke tare dashi. Sun ja hanklin iyayen yara masu cewa su dole sai 'ya'yansu sunyi boko mai zurfi, ko sai sun kama aikin kafin suyi aure. da cewa wannan ba koyarwa addinin Musulunci ba ce. Suka ce, ita mace babu abinda yafi daraja da mutunci a gare ta irin aure. Sun ce boko ba ya hana aure, kamar yanda aure baya hana boko. In 'ya'yanku suka lalace saboda kun hana su aure sai boko, hakika laifin zai fi ta'allaqa a kanku iyaye., Nasihar da suke yi ta sani shiga dogon tunanin, ni kaina misalice SANADIN BOKO gani yau na zama 'yar kaina, domin da ace ban ce bokoba nabi zancan mahaifina nayi auran da yaso, da yanzun ina tare da dangina da ban kashe auran iyayena ba, da ban haifi shege ba, da maxa ba su dinga latsa ni suna son mu lalace ba. Ban san hawaye na sauka daga idanuna ba, sai dai hannun Rahma naji a kumatuna tana share min tare da yi min rada a kunne. Haba Hafsa cikin fa taro ki ke, ya ya za ki ba mutane damar yin tunanin ke wacece? Please ki share don Allah. Walima ta tashi lfy, na ce da Rahma bari na leka shop, kin san ban dauki uxiri ba, ta ce min ba damuwa. Naje na samu su Ishak, ya ce nasan kuna biki shi yasa ban tashi ba, na fada mawa manaja cewa zan zauna madadin ki har ku gama biki, ya kuma san auran Rahma ne shi yasa bai ce komai ba.Ya kara da cewa, ki koma har sai kun gama ki mata fatan alheri, mun so muzo daurin aure amma kin san Manaja. Na ce na gode, ya ce a'a ba komai, wata rana irin haka zata iya faruwa da mu, na dawo nake fada ma Rahma ta ce, Ishak da Musa suna da kirki sosai, dn dai kin kasa Fahimtarsu ne. Na ce, Ba zai sa don sun kar6ar min aiki in sakar musu fuska ba, gaisuwa kawai ke hada mu ko da, kuma ita zan ci gaba da yi kadai. Anje anyo ma Rahma danki(jere) an zo ana ta lbrn kyan gidan an ce ango ma ya zuba labulaye da kayan wuta, Sai an kai Amarya sannnan za'ayi sauran shagalgulan da ango suka shirya, wai ba a son mutane suyi yawa, sai ka nuna pass sannan zaka shiga. Da muka kai amarya unguwar Sharada, gidan kam ko ni ya min sosai, taso in kwana na ce mata ta min hakur sai gobe in mun hadu gurin (pink & blue day' . Ta ce don girman Allah kada ki ki zuwa, na ce kin sanni Rahma in har na ce zan yi abu bana fasawa, ta ce shi kenan, ki gaida min Shadad. Na tafi ina hawayen rabuwa da Rahma,