← Book details Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 34

Sashe 16

Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yarinya ba za ta fi sha takwas ba, ba ta da lfy tana laulayin ciki. Ya ce min, Matarsa ce. Sai na soma tunanin cewa in nemo samarina na da mana,duk wanda na bncika sai in samu lbrn cewa yayi aure. Hankalina ya tashi matuka, yanzun gurin mu2m daya nake sa rai,wato Nasir wanda ya soni tamkar ransa, duk in da zan samu lbrn Nasir naje amma bn samu lbrnshi ba. Wata safiyar Asabar, misalin karfe goma na safe,na nufi supre markte don siyan kayan shafa, domin nawa sun kare. Ina sa kafa daya kan na dago dayar,wata 'yar kyakkyawan yarinya 'yar kimanin shekara sha biyo ko sha daya ta rugo da gudu daga ciki sai ko ta rungume kafata tana cewa . Anty 6oye ni Fadil za ya kwace min (Teddy)na. Na daga ta sama,daidai lokacn da yaron ya iso, daga gani kaninta ne yana da kiba. Ya ce, Anty nima ki ce ta bani boll dina. Na dube ta, ina boll dinsa? Tana dry ta ce, Anty boll dinsa fa tana mota. Na ce to dauko masa, zan sauke ta ta sake kankame ni. Anty Fadil yana da karfi zaya ture ni ya kwace (Teddy) na. Dry na ke t musu, ga shi sai naga sun shiga raina, na ce to muje in sai maka wata boll a ciki. Muna isa daidai gurin kwallaye na ce za6i wadda ka ke so, yarinyar ta ce Anty nima zan kara (Teddy) daya. Muryar Babnsu naji ya ce, sannu da kokari sun dame ki ko? Ina daga ido na sauke kan Nasir, da sauri na ce Nasir! Da alama sai lkcn ya gane ni, ya ce a'a Hjy Hindu BOKO uwaka ubanka ya karatu? Sai naji tankar ya min habaici ne, na ce Alhmdulillah, mun gama hr na soma aiki,ya ce lallai kam buri ya cika, na ce yaranka ne wadandan? Ya ce, eh Fadil da Fadila,sai kanwarsu Yasmeen. Na karkata kai tare da cewa, Allah ya raya su. Ya ce Amin. Na ce, yanzun kana ina ne? yace muna Abuja ne mun zo hutu ne, ke fa? kafin nayi magana wata mata kyakkyawa ina ga zan girmeta ta iso tana sanye da after dress me shegen kyau. Ta ce Beby ka gan su? Ya ce ga su nan sweet heart, ta dube ni ta yatsina baki tare da cewa, wannab fa? Ga mmkina sai na ji ya ce,Ina tsohuwar budurwata Hindu,? To ita ce wannan. Nan take ta watso min wani mummunan kallo, sannan ta figi yaranta gami da cewa, mijin mace daya zo muje. Yayi murmushi tare da daga min yatsu 2 gami da cewa bye. Ban iya tsayawa siyan komai ba na fita. A gida ma ina shiga kai tsaye dakina na nufa,na fada kan gadona ina kuka. Tambayar kaina nake, wai dama gaske ne da Bature ya ce dama sau daya take zuwa ma mu2m a rayuwa? In ko haka ne na cuci kaina na bar damata ta wuce. A ranar ne na soma tsanar BOKO akida, tun daga nan na koma ga Allah, ko yaushe nayi sallah addu'ata ita ce Allah ya ban miji. Kawayena, sa'annina duk sunyi aure da yaransu,kuma bn tsere musu a karatu ba,tunda aina aiki suma suna aiki. Amma sun tsere min don suna da aure ga kuma 'ya'yansu. Doctor Hindu ta dube ni, Hafsatu kin ganni nan da kama aikina yau shekara goma sha biyu kenan,amma babu miji. Har Malamai na shiga don kawai in samu miji. Daga wanda zai ce Aljani ya aure ni, sai wanda zai ce asiri aka mini,suka yi ta cin kudina suna min karya, daga karshe naga babu wani ci gaba na watsar da su. Yanzu na rumgumi kaddarar da nawa kaina, mahaifina ya rasu shekaru hudu da suka wuce abin da yasa nabar gida katsina na dawo nayi asibitin kaina shine, kannena yaran amaryar babanmu duk sun raina ni gashi ba mu cika shiri da hajiyata ba. Shiyasa da aka raba muna gado na yo nan na gina asibiti da gidana, sai dai ina zuwa gida kan lokaci in duba su hajiya ta. Share hawayenta nima sharar kwalla na ke tayi, dan murmushi me kika fahimta ko nace wane darasi kika samu cikin labari na? Nace na farko ba kyau wulakanci, sannan mu daina sanya boko ya zama gaba da aure kamar yanda nima nayi. Tace hafsatu naki mai saukine dan ke kin kama saurayi shi ne dai wanda kika kaman ya cuce ki. Amma ni abinda nayi saboda boko! Ta jin jina kai sanna tace ko rabi ban fada maki ba kuma halin da nake ciki yanzun nima na kirashi SANADIN BOKI, nace auty haryanzu baki wuce aure ba. Tace to in ban wuce ba hafsat ina mijin? Kwata kwata na daina burge maza, sam ba sa jin sha‘awa ta sai yan yara wanda da nayi aure kan ka ida na rantse miki hafsa da yanzu inada kamarki koma wanda yafiki don haka sha warata dake ki daure ki haifa dan cikinki baki saniba ko shi kenan kwanki a duniya. Sannan kiyi aure tun da kuruciya, aure ba zai hanaki boko ba kamar yanda mahaifinki yace. Magana daya zan fada maki, kada ki sake yarda saurayi ya taimaka miki game da komai na kudi, zai iya anfani da hakan ya cutar da ke, duk da nasan akwai masuyi don Allah. Asabe da ke gefe cikin tagumi sai yanzu ta tsoma baki, anty wallahi ban taba zaton kina da matsala ba, duk kalon da nake maki mijinki da yaranki suna kasar waje. Maganarta sai ta dan bamu dariya. Har likitar ta barmu ta koma dakin ta ban daina mamakin lbr ta ba, duk kyanta duk kudinsu duk bokonta ta kasa samun miji lalle kuwa boko yaja mata. Wata zuciyar ta ce min ba boko bane wulakancinta ne ya jamata, koma mene yanzu na fiskanci aure yana sama da komai. Washe gari gida na shirya wucewa kaduna, sai dai kudin mota bani dashi amma ba zan iya fada mata ba. Dan haka nayi shuru dari biyar ta bani wai nasha ruwa a hanya. Makaranta na koma na canja kaya na dauki kwalin wayata na nufi kasuwar masu waya ni dai ban tsaya ciniki ba, dan ba a cikin nutsuwa nake ba, yace dubu 6 inji mai siyan wayanr, bani kudin kawai nace don na kosa insami munir inji yadda zamuyi. Kai tsaye gidansu na dosa ko unguwarmu ban sauka ba, koda mai gadinsu yace min sun fita da maman shi sai nasami can gefen gidan na zauna. Ko shekara zasuyi sun dawo su same ni, na fada cikin raina. Kusan awa 3 sanan motarsu ta dawo tayi hon, mai gadinsu ya bude ban bata lokaci ba na mike na rufa musu baya. Daga inda nake tsaye ina hango kannanshi mata suna sanye da gajerun wanduna, kai ba dan kwali suna ta shiga da kaya. Dayarce ta hangoni sai naji tace mom ga wata can ko mai aiki ce? Matar ta waiwayo, kamanninta sak da munir haka ma kannanshi. Ta nufoni lafiya? Warin munir yayana ya aikoni, tace wai me? Nace abokinsa ne zan amsar masa sako ne, sunyi magana da munir din. Tace ok ta nufi ciki tana kwala mashi kira. Yafito daga cikin gida yana cewa yes mom.... ganina yasa shi yin wani turus! Tace gawata can wai yayanta ya aiko ta." Da sauri ya ce, "Oh na gane sako zan bata." Ya iso gurina fuska daure, "Lafiya Hafsatu kika biyo ni gidanmu?" Na ce, "To ciki fa bai fita ba." Da sauri ya dora yatsanshi a lebe tare da cewa, shishsh. Ya nufi gefensu gami da cew Zo. Muna shiga ya ce, "Kina nufin cikin bai fita ba?" Na ce, "Wallahi." Ya ce, "To ki koma gida zan zo anjima da dare in kaiki wani asibitin a fitar da shi, wannan bata san aikinta ba." Na ce, "A gaskiya ba zanje a kasheni ba, don Likitar tayi duk wani kokari don ganin ya fita amma abin ya ci tura. Ta kuma fada min in na matsa cewa sai an cire to zan iya rasa raina. In je in cema Ubangiji na me?" Ya ja tsaki, "To me kike nufi?" Na ce, "Shine na zo mu san abin yi." Ya ce, "To me kike ganin za'a yi?" Sanyi na ji cikin raina, Allah ya sa ya yarda na ce, "Ina ga mu hakura in zauna can gidan Likitar, ko Inna ba zan fadawa ba in na haihu sai muyi aure." Ga mamakina sai na ga yana dariya, a zato na zancen ya masa dadi, kuma shawara ta ta shige shi. Amma sai naji ya katse tunani na da cewa, "Amma ban taba sanin baki da hankali ba sai yau. Kina zaton ko aure na yi yanzun nan da shekara goma zan haihu?" Ya girgiza kai, "Ba zan haihu ba, saboda haka dole ne a cire wannan cikin, in kuma kin dage to kije can ki nemi Uban danki." Da sauri na dube shi, "Munnir ka san me kake fada?" Ya ce, "Eh, ina da ja kan wannan cikin, cewa nawa ne. Daga sau 1 shima ba cikin kwanciyar hankali ba amma shine ciki zai shiga?" Bakin ciki ya hana ni magana, idanu kawai na tsura mishi, shima ni yake kallo cikin harara gami da daure fuska. Na ce, "Allah ya sani ni ba mazinaciya ba ce,,,,,,,,," Kuka ya kwace min, "Kai ne ka soma keta min mutuncina, ka raba ni da 'yan matanci na, yanzun kuma ka bini da sharri. Allah ya isa tsakani na da kai." Ya matso kusa da ni, "Zan mare ki in kika zage ni, banza butulu. Duk taimakon da nayi miki da kokarin da nayi miki amma kin kasa gode min, shashasha, Kin zata zan kashe miki kudi a banza ne tsawon shekaru? Ki sani in kin ga kare yana shinshina takalmi to dauka zai yi, ni ba ajinki bane don ki sani." Kuka mai karfi ya kwace min, "Allah ya isa Munnir, dama yaudarata kake yi kace zaka aureni?" Ya yi 'yar dariyar mugunta, "Kin dai yaudari kanki, to ai ni ne ma zanyi Allah ya isa tsawon shekara 3 zuwa 4 ina miki bauta ke da me kika taba saka min?" Ban san lokacin da nayi kukan kura
Chapter 16 · 0% Book details