← Book details Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 34

Sashe 12

Sanadin Boko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yar dariya nace eh mijinane wasa ne ya ruda ni na kasa sukuni, tare da boyiwa innarmu don kada ta hanani fita, sai dai har tara banji ance ana kiran hafsa ba,har fita nayi gurin bakin titi ina tunanin wai ko yazo bai gane layin ba na dawo daf da zan shiga gida na ganshi tsaye kofar gidan mu. Wani sanyi naji acikin zuciyata, sai na soma tunanin zan jene na ce mashi gani ko ko ce mashi zanyi ni kake nema? Sai na yanke shawarar na bi ta gabanshi, har na daga labulen buhun da yake kofar gidadanmu zan shiga, sai naji yace hafsy sai na tsaya tare da sauke a jiyar zuciya, sannan na wai wayo na tako cikin irin tafiyar da ban taba sanin na iyata ba. Duk da yake dare ne a kwai kwan lantarki a kofar gidan, yace nafi minti 5 ina jiranki nace ina yini? Yace lfy da farko dai sunana munnir jafar dalibi ne a (A B U) zariya ina shekara ta 2. Sanan muna zaune ne a nan makarfi road son munnir ya kara shiga ta, don a rayuwa ta inaso in auri miji dan boko nace ni kuma na gama js3, yace me ya hanaki cigaba? yanayin garin ne. Haka muka ta fira sam bansan dare yayi ba har 10 ta gota ba sai da naji karan raidiyon baban mu ya nufo gida. Ya tsaya tare da cewa wacece nan? Ke hafsatu me kikeyi haryanzu? Na dubi munir nace ga baba na. Ya cire hular kansa hana sallah yace ina yini baba? Ya dubeshi lfy lau zo ki shige muje, nace to sai anjuma yace zan zo gobe nace to. Tun kafin mushiga daki baba yake min fada tare da tambayata wanene wannan yaron ya dame kugu? Nace dazum ne muka hadu dashi. Hayaniyar shi ne ta tashi inna daga dan baccin da ta soma, tana tam bayarshi lfy malam kake fada da tsohon daran? Yace amma dai ke sakaryar uwace, 10 ta wuce yarinyarki tana can tana zance da wani kato ke kuma kin hamgame baki kina bacci Inna tace hafstu na can tayi baci tuni dakin babarsu, ba ita kagani ba ita da bata fita zance ma yace to ga tanan ma bare ki karyata ni. Inna tace hafsa zance kika fita? Ya mukayi da ke? Baba yace ni dai tashi ya turo mun iyayensa dama ni burina in aurar da ita. Inma shi bayi zaiyi ba akwai mutane da dama sun min magana. Inna tace je ki kwanta itama ta maida kai ta kwanta alamun zancen baba bai shigeta ba. Da safe ta tsareni da son jin wajen wa na fita? Nace inna wlh jiya ne fa da kika aikeni ya ganni shine yazo. Tace amma nace maki ki fita hanyar samari ko? Kin san babanki matsawar zaki rinka tsayawa zance kina son karatun nan zaki barshi ko nace inna naga shi wannan yana son karatun, don su gidansu yan boko ne. Maman shi da baban shi duka aikin gwamnati sukeyi yace min jami‘a yake yi (A B U) zariya tace to ni dai banaso kurinka tsayawa nace yama ce zai bani kudi nacigaba da karatu na. Inna tace to indai ko haka ne sai dai kitafi makarantar kwana, saboda kin san babanku sarai. Koda munnir yazo washegari, haka na zauna na fada mashi komai dangane da ma haifina game da kin boko. Yace taf kice cutarki zaiyi? Tun kina karama zai kasheki da aure ai gaskiyar innarki ne kada ki yarda. Nace kudine matsalar mu sai dai in shiga ta kwana yace haka ne, yace zan baki kudi bari dad dinmu zai bani kudi in yadawo tafiya. Nayi ta masa godiya yace a a shidai abinda zanyi mishi kada in saurari kowa kuma na saki jikina dashi, nace kada yaji komai cikin sati 1 na gama yarda munir na sona, nima kara sonsa nake duk zuwa yakan zo min da wani abu, turare ko dan zobe ko dan wani abun kwalama. Bana manta ranar lahadin da yazo min sallama zai koma makaranta ya kuma bani kudi naira dubu 20 har kuka nayi mashi dan bana so rabuwa dashi. Ranar shida abokin sa sukazo wai shi faisal, kawai sai naji munnir ya rumgume ni, wani abu naji tun daga tafin kafata har tsakiyar kaina,shiko sai cewa yake inyi shuru in daina kuka hannun shi kuma na zaga sassan jiki na, fadan inna ya fado min cikin rai inda take cewa. In kula da kaina wasan banza da namiji zai iya sawa in sami ciki, nayi sauri na janye jiki na daga gareshi, yasa hannu yana share min hawaye muka yi ban kwana na shiga gida. Suna tafiya faisal yace munir dagaske kana son yarinyar an? Munir yace da dai nazo na dan kwashi rabo nane, sai kuma na gane yariyar ba yar hannu bace. Sannan kuma nasamu kaina da sonta na gaske faisal yace ka dai san dadinka ba zai barka ka auri yar geto ba ko? Yace kai nif zan zaba da kaina ba zan yarda ace min naje ga yar wani ba. Nikam ina shiga gida muka soma murna da inna, nan muka shiga tsara yanda zamuyi wa baba bayanin munir. Washegari inajin inna tana cewa baba wai kananta da yayansu sunce ta kaini zasu nemmar min makarantar kwana. Baba yace a a shifa bai yarda ba, tace yayi hakuri kwana nawane zan gama? Baba yace nifa ba kin karatun nake ba, nafiso tayishi a can dakinta inaso kisani har in yarinya ta soma tsayawa da saurayi mafi kyawu shine ayi mata aure. Inna tace za ayimata malam, wannan yaro da ka ganta dashi shene yake son auranta na lura itama tana sonshi yace to ba sai ya turo magabatan shi ba muyi zancen manya! Inna tace yo shima ai karatun yake sai ya gama itama ta gama kafin nan. Shuru yayi bai sake tankawa ba shurun ba yana nufin ya yarda bane, shurunsa yana nufin mukarata can shi ba ruwansa. Kwana 2 tsakani muka shirya ni da inna muka nufi manunfashi kananta kawu sha‘iabu da kawu bashir harda wanta kawu kabiru sun sunji dadi sun kuma tsaya har saida nasamu shiga ss1. Haka baba ya hakura ya zuba muna ido, na cigaba da karatu cikin nasara da kwazo, yan gidanmu kam da makota sai gulma da tsegumi, ba mu damu ba. Fatan inna shine inzama abin kwatance nan gaba. A duk lokacin da nazo hutu munnir nazuwa, haka duk lokacin ziyarar dalibai in yana da sarari yakan zo. Hidimar karatuna shi yake yinta haka nan duk wani kaya na yan mata shi ne yake siyan min, wanan shine yasa na kara sake wa dashi. Matsalata dashi son taba jiki na, kawai lokacin da wani hawaye yayi min wai in bishi muje dakin wani abokin shi, niko nace a a muji tsoron Allah ba don son da nake yiwa munnir ba a tuni na hakura dashi. Cikin haka na gama karatuna na secondary. Na dubi likitar idanuna suna zubar da hawaye nace, anty ko lokacin da na gama karatu na baba ko gai suwa nayi baya amsawa, kannena yaran kishiyar mama na guda 2 ya musu aure. Sannan karatuna kafin na tahoshi sai da ta kai yace in har wani abu ya biyo baya abakin auran innata, sannan in nemi uba..... Kuka ya kwace min mai karfi, ina fadin na shiga ukuna zan kashe auran iyaye da kaina. Munir ya cuceni fyade yayi min anty ki taimaka ki cere cikin nan. Yan gidanmu da yan unguwarmu duk dariya zasuyi mana. Kalo kawai likitar keyi cikin tausayi har nayi kukana mai isata na gama ba wanda ya bani hakuri. Daga ita har asabe tace to, ke hafsat ki koma makaranta gobe kizo, keko asabe ki kwana nan nace anty don Allah nima zan kwana nan din, ko naje makarantar ba zan iya komai ba, tace shikenan. Ta mike sannan ta nuna mana wani daki, ku shiga nan kuyi sallah da komai a ciki. Ba tare da ta jira amsa ba ta nufi dakin ta, kaiwa da kawowa kurum take yi. Ta ina zata bullowa wayanan yara? Sam bazata cire cikin ba, bazata kuma bari suje su cire su zubar ba. Ta lura Asabe tafi saukin kai don haka da ita zata fara. Yanda naga rana haka na ga dare, alwaula kawai nayi na yi nafila. Daga bisani na koma istigifari, washegari bayan ta lalabemu mun karya, sai ta bamu wasu magun guna tace kada in damu in koma makaranta insha, suna da karfi na sati 3 ne, ta tabata cikin zai fita nayita godiya na komo. Sai da daktar hindu ta sami shugabar kungiyar kare hakkin bil adama. Tayi mata bayanin komai game da halin da asabe ke ciki, Shugabar Hjy Adama ta ce, to za su samu Hjyr Yasir su fara neman sulhu, in ta ki kuma to za a maka Yasir a kotu. Doctor Hindu taji dadin haka, don haka ta tambayi Asabe yaushe aka fi samun Hjy Mairo a gida? Asabe ta ce Lahadi da rana, sauran ranakun sai dare ake samunta. Sun same ta cikin Kasaitaccen falonta tana shan kayan Marmari, suka sanar da ita dalilin zuwansu. Ta ce, sam ita dai ba danta ba, ai ta ja mata kunne, nan suka nuna mata cewa zata amsa kira a kotu gobe Litinin. Yasir na dawowa ta hau shi da fada, ya ce tayi hakuri sharrin shaidan ne, ta daka mishi tsawa ta ce, yi min shiru,wawa kawai. Ta tausasa murya a bin da nake so da kai, za su shigar da mu kara, saura in mun je ka saki baki ka nuna kai ne, ina so ka bata rai ka hade fuska ka nuna sam ba ka sam ba ka san zancen ba. Ni kuma zan tsaya maka, Babanka zai tsaya maka, domin duk Alkalin garin nan ba wanda zai ketare bukata mahaifinka. Yasir cikin murna ya ce, "To Hjyta. A daran ranar ta kira mahaifin Yasir ta shaida mishi abn da ya faru, wai me aikinta tayo ciki tazo ta ce Yasir ne, yanzun haka kungiyar kare hakkin dan adam ta shigo cikin lamarin sun ce za su shigar da kara,Ni kuma na ce su shigar, ya ce amma ba ki da
Chapter 12 · 0% Book details