← Book details Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 27

Sashe 9

Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To mango park wanda aka kirkira da turanci, na rantse da Allah yaranan karya kake yi ba wani ciwon mantuwa dake damunka, kawai Kursum kake san kulawa shiyasa ka fake da haka." Muryar Kabir ce ta daki kunnansu, da mamaki Kursum ta kalleshi ciwon mantuwa kamar ya? Kursum ta tambayi kanta, shikuwa Kabir yana tsaye a kansu yana huci dan ya gaji da wannan rainin hankalin.

7065283730
Opay
khadija Abdullahi shehu.

Katin waya MTN ta 07065283730

Shaidar biya ta 07065283730 or +447894142004

Bonanza ki biya 500 daga yau zuwa 12th ga wannan watan kunsani ni da ku 5&6🥰

Ayusher Ce🏌🏻‍♀️
*RIBAR ƘAFA*

NA

Wattpad :-AyusherMohd

Arewabook:- Ayushermuhd

ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️

Paid Book

Shafi na Shida

Riƙo hanun shi yai yana mai alama da ya fitar musu daga gida, Kursum da sauri ta mike tsaye tace "Ya KB meke damunka wai? Koma menene sai ka jira Baba ya dawo." Wani kallo ya mata yace "Kema san zaman nashi kike a gidan?" Mamakinshi ne ya kamata, tasan yanada tsokana amma bata taɓa ganin ya takurawa wani haka ba, cike da mamakin dake bayyane a fuskarta tace "Kai ka sani, ni karka sani a case ɗin ku." Tana kai nan ta amshi littafinta dake hannun yaran, ta kama hannun Umma ta bar gun, Kabir ya zabgamai harara yace "Wani ya ganka sai ya ɗauka na Allah ne kai, ni haka kawai jikina ya kasa bani kai irin mutanen nan ne salahai, duk yanda kaso kai sumi-sumi bazan iya yarda dakai ba." Nafi'u sam bai kulashi ba, ga mamakinsa inda Kursum tai yake ƙoƙarin zuwa, baki ya saki yasha gabanshi da sauri yace "Ina zaka?" Yana kallan inda take tafiya yace "Na manta ban faɗa mata yanda zata gyara daya tambayar bane." Bakinsa a sake yace "Au duk maganar da na maka bakaji ba kenan? In koyarwa kakeso muje na baka aikin koyarwa a makarantar Baba amma magana ce bansan ka sake ma Kursum." Kallansa yai sai kuma ya wuce ɗakin mai makon ya shiga ɗakin Baba sai ya nufi ɗakin Kabir, kwanciya yai yana san tuno abu wanda ya rasa wani abu ne. Kabir ya shigo yana sake mai warning akan karya kuskura ya sake kula Kursum bai yadda ba dan ya kula maganarshi ma nata tashi sai da Kursum ko abinda ya shafe ta.

Alhaji Nuhu Danbatta kuwa bayan yaje gyaran mota Kano ana gamawa ya sake wucewa yaje police station din jiya akan maganar Nafi'u, gun wani officer yaje yana tambayarshi ko sunji wani labari akan yaran da ya kawo jiya. Officer ya kalleshi yace "Wani yaro? Mu ba'a sanar mana da binciken wani da ya ɓata ba." Alhaji Nuhu Danbatta zaiyi magana sai ga DPO ɗin jiya nan ya ƙaraso da sauri yana gyara zaman belt din wandansa, kamar wanda aka koro shi, ya dafashi da sauri, Baba ya juya ya gaisheshi, alama yawa officers din su tafi kafin yace "Muje ciki muyi magana." Bai musa ba ya shiga office din, suna shiga bayan ya zauna yace "Wai zuwa nai inji ko Allah yasa an dace." DPO ya gyara zamansa ya miƙa mai hoton Nafi'u da sauka ɗauka jiya yace "Kaga hotunan nan duk na turawa ragowar police station, ina sa ran zuwa anjima zamuji halin da ake ciki, dan haka ka koma zan ƙira ka, ba sai ka ɗin ga zirga-zirga ba kuɗin mota ma da mai ya isheka." Baba ya amshi hoton yana cewa "Mungode sosai, da tunani nake ko naje gidan radio? Ko tv ko Allah zai sa su taimaka mana." Cikin sauri ya katseshi yace "A'a, in kaje kuma baka tunanin zai jawo matsala? Yanzu ace yaran nan rayuwarshi da matsala ko nemanshi ake ko kuma mugayen mutanen dake amfani da samari gun aikin banza su ganshi, me kake tunani in sukaji labarin baisan komai yanzu ba? Tsaf zasu iya amfani dashi dan jefashi wani hanyar, amma kai mutumin kirki ne shi yasa nakeso ka kara hakuri ya zauna a gurinka in har mukaji wani abu zamu sanar maka." Zuciyar Baba kokonto ne a cikinta yana ƙoƙarin sake magana DPO yai saurin cewa "A kan case ɗin nan karka yadda da kowa sai ni sai likitan da kuka je gunsa jiya, kwanakin baya an taɓa samun irin haka ashe ƴan mafia ne suka amshi yaran ko kwana biyu ba'ai ba sai ga gawar shi." Jin wannan labarin ba ƙaramin tsorata Alhaji Nuhu Danbatta yai ba cike da sanyin jiki yace "Zan ajiyeshi a gurina har sai ka nemeni insha Allah amma dan Allah inda hali ko gidan tv da radio ku duba ko ankai cigiyarsa." Fuskarsa ɗauke da murmushi sosai yace "Kar ka damu, sannan ga wannan ka ƙara mai sannan dan Allah kai ƙoƙarin rike bakinka akan yaran nan, inhar aka san baisan abinda ya faru dashi ba wani zai iya cutar dashi." Alhaji Nuhu Danbatta ya jinjina kai alamun gamsuwa sai dai yace "Kuɗinka ka barshi, nidai burina ku taimakemu." Fitowa yai ya saki ajyar zuciya zuciyarsa fal da kokonto amma ya rasa kokontan me nene, maimakon ya koma Danbatta gidan Bashir ya wuce, Bashir shine babban dan Inna wato Samira, sai dai shi mahaifinshi daban ta auri Alhaji Nuhu Danbatta ne bayan auranta na farko ya mutu. Samun matsalar da sukai shine ta tattara taje gunshi ta tare, yayi aure yana zaune a Kano da matarshi cikin rufin asiri. Gidan Bashir ɗin ya nufa cikin motarsa ta akori kura wanda aka gyara yau, a hanya ya tsaya ya ɗan sai lemo da ayaba. Koda ya isa gidan Bashir baya nan, matar Bashir Balki tasa ya shiga ciki sai da suka gaisa yace a ƙiramai Inna ta fito su wuce zaman ya isa haka. Sai ga Balki ta dawo wai ya koma shi kaɗai Inna bata san komawa. Agoggon hannunsa ya kalla kafin ya kalli Balki wacce kunyar sakon ya kamata yace "Kice mata na wuce sanda ta shirya ta taho." Jiki a sanyaye ta miƙe dan Itakam ba tasan wannan zaman na Inna dan dai ba yanda zatai ne, har yaje ƙofa tace "Baba ko zaka mata magana? Ɗakin da take ba kowa in dai ba matsala." Kallan Balki yai sam ba ya san shiga ciki sai dai da alamu ya fahimci itama ba tasan zaman Inna kuma hakkinsa ne ya taimaka mata. Gaba tai ya bita a baya har zuwa ɗakin, labulen ya yaye ita kuma Balki tabar gun, tana zaune tanacin shinkafa da wake da salad ɗin da aka kawo mata. Ganin an bude labule bata dago ba tace "Balki ya wuce?" Jitai ance "Ko kunya bakya ji kizo gidan ɗanki ki zauna." Waigowa tai da sauri, ganin Alhaji Nuhu Danbatta yasa ta ajiye cokalinta, mace ce dattijuwa wacce a kalla tayi shekara hamsin zuwa hamsin da biyar, in ka ganta kaga Adda Yagana dan kamar an tsaga kara saboda kamar da suke. Komawa tai kan katifa ta ɗau ra ƙafa daya kan daya ta harde hanayenta tare da juya baya, yana nan daga inda yake yace "Zaki taso mu tafi ko na wuce?" Bata kalleshi ba bare yasa ran zata tashi, yana nan daga inda yake yace "Samira banasan shirme dan Allah, ko kinaso muyi magana akan alkawarin dake tsakanin mu?" A hankali ta juyo nan danan yanayin jikinta ya canza, yanda take kallansa yasa yace "Bansan me kike tunani ba da kika taho sai dai karki manta da alkawarin da kika ɗauka kafin ki aureni, ni har yau ba na ji na karya wannan alƙawarin amma ke da alama baki ɗauke ni da mahimmancin da zaki rike alkawarin da kika ɗaukar min ba." Bai jira me zatace ba yace "Ki shirya zan jiraki a waje na minti goma na baki in har baki fito ba zan wuce, kuma karki sa ran dawowa." Yana kai nan ya juya ya fita, shiru Inna Samira tai, tana tuno alƙawarin da yake nufi wanda ta sani shine yasa ya aureta, mikewa tai cak ta ɗau karamar jakarta ta fara zuba kaya, kallo ɗaya zaka mata kasan zuciyarta cike take da tunani. A falo taga Balki a tsaye tai murmushi tana juya kai tana cewa "Yaran nan basu dawo ba gashi zan wuce, kinsan Alhaji sam ba ya iya samun nutsuwa in bana guri." Balki jiki a sanyaye tace "Wayyo Inna zamuyi rashinki zamuji gidan shiru." Tana dariya tasa takalminta, haka Balki ta rakata har waje sai data shiga mota ta dawo." Jagwab jagwab din da motar akori kurar takeyi ne yasa tace "Wannan tukin dai kamar da gayya kake yinsa sai jijigamu kakeyi." Hannunsa ya kalla wanda ke ciwo har lokacin wanda shi yasa yake tafiya haka, ya maida hankali kan titi yace "Akwai yaro Nafi'u dake zaune a gida....."Ko bari ya ƙarasa batai ba cike da masifa tace "Babu shi a lissafin alƙawarin da mukai da kai kuma babu dalilin da zaisa ya zauna a gidana." Ajiyar zuciya yai kafin yace "Ba yaro bane saurayi ne sannan hatsari mukai nine na kadeshi kinga kuwa hakkinshi na wuyana, abu na gaba Kursum bata iya zuwa makaranta wanda ke kinsan abinda kikai bai kamata ba." Hannu ta ɗaga mai da sauri kafin tace "Ajiyeni na koma inda na fito bazai yiwu dan munyi alkawari da kai komai ka ɗin ga laftamin ba da sunan alƙawarin ba, a maganar mu da kai sam babu maganar kula da Ramlatu har Kursum tai karatu, babu maganar hanani fita da hidimomina saboda ita, babu maganar sake yin raino bayan ni yarana sun girma. Alhaji kayi hakuri amma wallahi ni dai bazan sake zama da Ramlah dan Kursum taje makaranta ba, inhar kasan ba yanda zakai sai ku zaɓa wala Allah ta ajiye karatu ko ka sama mata mai aikin da zai zauna da ita." Mamakin kalaman nan ne suka dameshi sai dai ya sani iya ƙoƙarin itama tayi kuma dole ya duba lamarinta. Jiki a sanyaye yace "Kursum na tunanin ajiye karatun amma ni ina ganin hakan bai kamata ba, dan Allah Samira kiyi hakuri ki barta ta ƙarasa jarabawarta tunda dai ta kusa."
Chapter 9 · 0% Book details