← Book details Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 27

Sashe 5

Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****Can cikin baccinta take mafarki yanda ake binta da gudu tana shiga cikin daji, gudu take iya karfinta sam bata kula da ciwukan dake jikinta ba bare katan cikin da take ɗauke dashi. Hakki kawai take tana cigaba da gudu, cak ta tsaya tare da kallan katan ramin dake gaban ta. Shikenan rayuwarta tazo karshe, hanka ta ɗaga kai wanda hakan yasa ta saki ihu mai tsananin ƙara wanda yasa Kursum dake wanki a tsakar gida ta auna ciki a guje. Mahaifiyarta ta gani hannunta ɗaure akan wuyanta tana shake kanta da hanayenta biyu, numfashinta da kyar da kyar yake fita, gashi idanuwanta a tamke gam. Hannunta ta shiga kwacewa tana kwallawa Hasina kira dasu Adda Yagana sai dai ba wanda ya fito. Cigaba da ƙoƙarin zare hannunta take daga wuyanta amma sam tayi saki sai kuma kakarin numfashi takeyi alamar dakyar take jawo numfashinta. Ihu take tana sake kwala musu ƙira. Hasina ce ta shigo da gudu nan suka cigaba da ƙoƙarin kwace hannun Umma, kuka kawai Kursum keyi tana "Umma ki taimaka ki saki wuyanki." Kamar wacce ake ƙara mata karfi da kyar suka samu suka raba hannayenta daga wuyan ta. Da sauri Kursum ta shige jikinta ta rungumeta tana wani irin kuka mai ratsa zuciya. Hasina dake tsaye tausayin Kursum duk ya kamata, sai dai tana tsoron kar Yayarta ta kamata anan. Shafa bayan Kursum tai kafin ta bar ɗakin cike da tausayi. A hankali Umma ta buɗe ido ganin Kursum na kuka sosai yasa ta rikice tare da riƙe fuskarta tace "Kur--summ nayi fitsari ne? Kiyi hakuri bazan kara....." Yanda Kursum ta sake matse ta ne yasata yin shiru. Sai dai har lokacin ta kasa daina cewa "Kiyi hakuri!" Daga waje ta jiyo muryar Kabir yana cewa "Kursum kina ina?" Tana hawaye tace "Ya KB shigo dan Allah." Yanda tai maganar ne yasa ya shiga da suri dan Kursum batasan ko labulen ɗakin su ya ɗaga tunda tace yazo tofa tabbas yasan ba lafiya. Cikin hanzari ya yaye labulen ya shiga hankalinsa a tashe, ganin yanda ta ƙanƙame Umma ne yasa shi zuwa inda suke yace "Kursum Lafiya? Meke faruwa?" Ya jero tambayoyin nan hankalinsa a tashe. Kallansa tai idanuwanta na hawaye sosai bakinta na rawa tace "Umma ce ta sake abinda tai kwanakin baya, nikam tsoro nakeji. Ya KB da ba kowa a kusa mutuwa zatai....." Kuka ne yaci karfinta wanda sam yasa bata kula da zamewar da ɗan kwalin kanta yai ba, gashinta da aka mata kalaba ya zubo. Kamar a mafarki taji ance "Are you okay?" Murya ce mai sanyi wacce ke tattare da tausasawa daga cikinta. Jin muryar tai har cikin kanta. Idanuwanta ta ɗago tare da saukesu akan saurayin dake tsaye jikin labule. Fuska ce da bata santa ba, bata kuma san daga ina yake ba. Idanuwanta akansa batai auni ba taga Kabir da sauri yayi kan saurayin ya turashi waje da karfi yace "Banda baka da lafiya da yau kasha duka, taya zaka shigo ɗakin budurwa ba izini?" Saurayin ya koma waje yaja gefe ya tsaya shi kuma ya koma ciki. Kursum har lokacin tana riƙe da hannayen Umma wacce numfashinta ya daidaita har lokacin tana hawaye tace "Umma mafarki kikai? Mafarkin menene yake wahalar dake nikam?"

"Mafarki? A'a yunwa nakeji." Hannaunta ta kamo suka fito daga ɗakin. Lokacin Kabir na ƙoƙarin shiga. Baya sukai yace "Komai lafiya?" Ta kalli Umma tace "Yunwa takeji yanzu zan bata abinci." Idanshi na kanta yace "Makarantar yau bakije ba?" Ta ɗan saki murmushi tana maida ɗanwalin kanta tana cewa "Baka nan Baba bayanan in na fita dawa zan barta? sannan yanzu kalli abinda ya faru, in tsautsayi ya afka ba kowa me zai biyo baya?" Bai amsa ba sai komawa waje da yai itama ta fito. Sake tsayawa tai ganin saurayin ɗazu tsaye jikin bango, daga sama har kasa ta kalleshi zata gaidashi taji Umma tace "Kaima ka yadda takalmin ka ko? To Allah yasa kar Kursum tama faɗa." Sai a lokacin suka kalli kafarshi, sam Kabir ya manta warin takalminshi ɗaya tun a asibiti babu. Mamaki ne ya kama Kursum tana ɗagowa suka haɗa ido, da sauri ta kauda kai ta maida kan Umma tana cewa "Umma wani faɗa kuma?" Bata amsa taba ta tafi gunshi da sauri tace "Ya sunanka?" Idansa ya sauke kan Kabir sanna ya kalli Kursum cike da mamaki take binshi ganin kamar bai san sunanshi ba. Umma tai caraf harda tsallenta ta nunashi da yatsa tace "Hooo oah na sani sunan ka Yakubu ko ko ba kanin Kabiru ba ne?”

Kabiru ya matso da sauri yace “Umma me kike cewa? Kin manta Kabiru ya rasu? Kurum wai ba yunwa Umma…….”

Kasa ƙarasa magana sukai ganin saurayin nan ya sulale ya faɗi. Hankali a tashi sukai kanshi. Kabir yace Kursum ta shimfida tabarma ta ɗauko pillow. Da gudu tai abinda aka sakata nan ya kwantar dashi. Kursum kuma na mai fifita da mafici. Idanuwansa ya shiga buɗewa a hankali ya saukesu kan Kursum. Murmushi ya sakar mata sannan ya kalli Kabir bai ce komai ba sai idanunsa da yake ƙoƙarin maidawa ya kulle. Cikin karfi Kabir yace. “Yaran nan nauyi kamar buhun shinkafa.”

Daga cikin ɗaki kuwa Yagana ce ta kalli Raheena da Hasina tace “Kunsan Allah muje mu dawo da Inna nifa ba yanda za’ai wata kanwar miji da ban yadda da ita ba tazo ta koreni daga gidana.” Ajiyar zuciya Raheena tai tace “Nifa banga laifinta ba babu yanda za’ai ya dinga fifita kanwarsa akanta, yanzu da ta tafi hutu gidan Yaya Bashir ba gashi har kiba tayi ba.”

“Mu kuma haka zamuyi ta zama a gidan batanan? Ni da gidan mu sai na dinga jina kamar taimako na ake a gidan ma wallahi. Haka kawai an takure mu daki ɗaya su an basu ɗaki harda bandaki a ciki.” Hasina ta faɗa tana yatsina fuska. Tsaki Yagana taja mai tattare da sauti tace “Ni takaicina Baba ko damar magana baya bamu a gidan nan kamar ba yaransa ba.” Kallan junansu sukai sannan suka mike suka fito yau dole su sanar mai akan ya yiwa Yaya Bashir magana a dawo musu da Inna gida. ita Yagana dama bazawara ce su kuma matan biyu ƴan mata ne.

Yanda sukaga Kursum ta haɗa gawayi tana ƙoƙarin ɗau ra ruwan zafi ne yasa Yagana tunzura. A fusace ta ɗau kwanan sha ta tafi kindimo ruwa a cikin randa tai kanta zuciyarta na wani irin zafi. Tana zuwa ta kwarawa gawayin nan ruwa wanda har sai da ruwan ya taɓa jikin Kursum. A tsorace ta mike dan abu ne datajishi sama ta ka. Baya tai da sauri ruwan dake tukunyar ya jirkice shima ya zube. idanuwanta ta sauke kan wutar sannan ta ɗago ta kalleta tace “Adda Yagana me kikeyi haka?”

“Na ɗauka na sanar miki duk abinda zaki dafa a gidan nan ki sanar min sai na baki izini tukun zakiyi?” Kursum ta kalleta tace.

“Amma ko haka ne sai ki kashemin wuta?”

“An kashe uban me zakiyi? Jiya dana miki magana kika shige ɗaki kin ɗauka kinsha ne? Dan me zamu cigaba da zama da ke da uwarki cikin takura? Ita ba hankali ba ke kuma kamar aljana?” Zata cigaba da magana sukaji muryar Kabir yana cewa “Yanda kika kashe wutar nan Hasina da Raheena haka zaku zauna ku haɗata dan kaf cikin ku ba mai matsawa har sai an haɗa wutar nan.”

Sam basu kula dashi ba juyowa sukai bangarensa inda yake tsaye, Umma na makale a bayanshi jikinta sai kyarma yake, idanunsu ne ya sauka kan saurayin dake kwance wanda basusan wanene ba. Baba daya shigo kenan ya saki murmushi shi yasa duk shiriritar Kabiru yasan zai kula da Kursum yarintace kawai ke damunshi wanda yake da tabbacin nan gaba kaɗan zai daina. Gyaran muryar da Alhaji Nuhu Ɗanbatta yai ne yasa suka kalleshi. Wata irin shakuwa ce ta kwacewa Yagana tana yi tana zaro ido....

7065283730
Opay
khadija Abdullahi shehu.

Katin waya MTN ta 07065283730

Shaidar biya ta 07065283730 or +447894142004

Bonanza ki biya 500 daga yau zuwa 12th ga wannan watan kunsani ni da ku 5&6🥰

Ayusher Ce🏌🏻‍♀️
*RIBAR ƘAFA*

NA

Wattpad :-AyusherMohd

Arewabook:- Ayushermuhd

ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️

Paid Book

Shafi na Huɗu

Adda Yagana zatai magana Kabir yai saurin cewa "Ke yayatace ba dake nake ba amma su wallahi na isa dasu kuma na faɗa babu mai tashi daga gurin nan har sai sun hura wutar nan, su kuma dafa tea ɗin, duk wani iskanci da kukeyi ai dan kunga Adda ta dawo gida ne dan da kaf cikin ku ba mai takurawa Kursum to wallahi duk iskancin ku na gaji dashi." Kallan juna sukai Hasina ita har tanta bataso kawai dai ba yanda zatai ne, da sauri ta fara ƙoƙarin kwashe gawayin Kursum ta matso tana ƙoƙarin taimaka mata, kallan da Kabir ya mata ne yasa ta ajiye tukunyar tana kallanshi, inyaso zama serious bazaka taɓa cewa shine mai shiririta ba. Alhaji Nuhu Danbatta ne ya ƙarasa shigowa ciki hannunsa ya makale a baya yana kallan saurayin dake kwance, kanshi ya nufa su kuma suna ganinshi suka fara kifi-kifi da ido, bai tanka musu ba  sai dai ya amsa gaisuwar da Kursum keyi kafin ya wuce inda yaran yake, da sauri Kabir ya koma gun ya ɗan sunkoyo yace "Baba kaga yaran nan mu maida shi gun danginshi kar ya mutu a hanun mu."

Alhaji Nuhu yasa hannu kan kafadarsa ya ɗan taɓa shi sai dai bai tashi ba, juyi yai ya cigaba da bacci, kallansa yai yace "Bacci yake kamar ko?"

Kabir ya girgiza kai alamun takaici yace "Baba yaran nan fa akwai mystery a tattare dashi."

"Mas me? Kaga ni bansan guntun turancinka me kake nufi?"

Waigawa yai ganin yan mata ba kallansu suke ba yace "Ban yadda dashi ba, ko dai barawo ne ko kuma aljani." Tsaki Alhaji Nuhu Danbatta yai yace "Tashi ka goyashi ka sashi a ɗakin ka inya tashi sai mu wuce."

Ido ya zaro ya waiga yace "Kursum ɗazu wannan buhun shinkafar dana zo jawoshi kan tabirma bayana bai kusa balewa ba?"
Chapter 5 · 0% Book details