← Book details Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 27

Sashe 25

Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ɗaki kuwa Alhaji Nuhu Danbatta ne ya kalli Kursum tare da yi mata murmushi yace "Kiyi hakuri Kursum bamu kyauta miki ba, babu yanda za'ai ace auranki ne amma ba wanda ya damu da ra'ayinki da abinda kikeso." Kanta na ƙasa sai dai idanunta taji sun ciciko, alamu ya mata data matso, matsawa tai cikin sanyin murya yace "Kiyi hakuri na sani bamu miki adalci ba." Kai ta girgiza da sauri alamun a'a kafin tace "Duk abinda kai a kaina daidai ne ni nasani bazaka taɓa cutar damu ba." Kai ya jinjina cikin jin daɗin kalamanta kafin ya sauke ajiyar zuciya yace "Ni na sani ciwon nan ba na tashi bane, a hakan ma godiya nakewa Allah daya bani ikon aurar dake, na sani Nafi’u zai kula dake insha Allahu.” Ya sauke ajiyar zuciya yace “Kursum maganar da nakesan sanar dake.." Shiru yai da alama maganar na mai nauyi ne a bakinsa. Murmushi tai tare da maida kwallar datake ƙoƙarin sauka kan kuncinta tana cewa "Kai ba Yayan Umma bane ko?" Kallanta yai cike da tunani da mamakin da ya bayyana a fuskarsa, tari ne ya ɗan kamashi wanda hakan yasata saurin sa mai oxygen ɗin, ta sauke ajiyar zuciya ganin yana samun nutsuwa kafin tace "Na daɗe da sani Baba na kuma san Umma nada tsohon cikina ka tsinceta dan haka karka damu, lafiyarka ita kaɗai muke bukata yanzu.” Duk yanda yaso ya daure sai da hawaye suka gangaro mai taya yarinya da ita zata iya ɗaukan wannan abu mai girma haka ba tare da ta nuna ba? Mikewa tai ta fito jikinta duk a sanyaye. Kabir ta gani a tsaye da alama duk abinda sukace ya ji dan yanayinsa ya nuna hakan. Murmushi ta sakar mai ta wuce ciki.

****

Ummi ce ta kalli driver ɗinta dake tuki gani take kamar baya sauri, Salim dake zaune a ɗaya ɓangaren a gaban mota ne yace "Amma Ummi kina tunanin Yazeed bazai tona asirin ɓata yai ba inya dawo?" Waje ta kalla tace “Ta ina zai tona? Bayan ko rantsuwa bazanyi ba tunda ya daɗe a kauyen nan akwai abinda ya shirya, dan ko yace ya samu ciwon da ya kasa tashi, wato ya kakkarye ina da tabbacin ba wai yanzun nan ya warke ba, kuma ka manta sanda akai kidnapping ɗin nashi abokinsa me yace sunje yi?” Kai Salim ya jinjina alamun gamsuwa tare da ɗan waigowa gaba ɗaya tausayin Ummi yake dan duk ta rame a ƴan kwanakin nan. DPO Abdul suka gani a tsaye a jikin motarsa a daidai kwanar kauyen gudun magana yasa baisa kayan uniform na aiki ba, yana ganinsu ya ɗaga musu hannu alamun yana gun. Gangarawa sukai tare da yin parking, Ummi cikin sauri ta buɗe ƙofar tace “Abdul ina Yazeed ɗin?” Ajiyar zuciya yai yace “Ku jirani anan yanzu zan shiga na ɗauko shi.” Fuska ta tamke sosai tace “Kana nufin na tsaya a nan har sai ka dawo? Bazai yiwu ba kafata kafarka, in gidan da ya zauna sune sukai kidnapping dinshi fa?” Iska ya ɗan furzar yana kallan hanyar yace “Kiyi hakuri Ummi yace karna kuskura na shigo da kowa, ni kaɗai zanzo na ɗauke shi, kinsan halinshi.” Shiru tai sai dai maimakon tai magana komawa tai ta zauna tare da maida ƙofa ta rufe ba tare da tace komai ba. Salim ne ya kalleshi yace “Nima kenan kar naje?” A hankali ya ɗaga kai alamar eh, yana shiga mota yana cewa “Inyasan haka ne menene na sanar damu? ai sai Abdul ɗin ya ɗauko shi ya kawoshi.” DPO Abdul ganin sun zauna yasa ya ja motarshi ya gangara kauyen Fagwalawa lokacin magriba na shirin yi.

Hasina ta dawo kenan daga kai sakon ɓacin ran Inna gun Yagana taganshi, nan ya sanar da ita yanasan magana ne da Alhaji Nuhu Danbatta. Jikinta a sanyaye ta sanar dashi bashi da lafiya dan ko ƙofar ɗaki bai iya fita, nan tace ya shigo tunda dai ya sanshi dan Babanta mai mutane ne bare wannan da yai shigan mutunci. Inna sanda yazo bata gidan dan ta shiga gidan Mai Unguwa ta amso kuɗin sadaki. Kai tsaye ɗakin ta nuna mai lokacin yana kishingiɗe bacci yakesan yi amma tunani sun hanashi. Jin sallama yasa ya amsa yana kallan Hasina wacce ta nuna mai gefe. Ido ya zaro yace “DPO kai ne?” Shiga yai yana murmushi tare da mikamai hannu, nan suka gaisa cike da jin daɗin ganinshi yace “Shiru-shiru babu kai ba labarinka.” Dariya yai yace “Aiki ne ya taso min amma garin yaya hakan ya faru dakai?” Baba ya bashi labari yana cewa “Raban Nafi’u zai taimakeni ne Allah ya kawoshi.” Murmushi yai yace “Zuwa nai ma na daukeshi dan Allah yayi munga kakaninsa kuma kakar batada lafiya tana buƙatar shi kusa da ita.” Cike da jin daɗi marar misaltuwa yace “Kai Alhamdulila Hasina kwalawa Yayanki Nafi’u kira.” Da gudu ta ruga tana ƙiranshi ba dadewa sai gashi nan Baba ya sanar dashi, kallan Baban yai yace “Baba inhar zan tafi sai dai na wuce da matata.” Kallan DPO yai yace “Dazu aka ɗaura mai aure kana ganin zata amince?” Kai ya jinjina yace “A yanda na ganta ba abinda zai hanata amincewa dan ta fika jin jiki, barsu suje tare inyaso in zama ya gansu sai su zo su yima sallama.” Cikin gamsuwa yace “Hakan yayi amma akwai matsala dan mahaifiyarta bazata yadda da ɗau keta ba.” Yazeed cikin sauri yace “Nima bazan barta ba Baba.” Wannan kalmar tasa hankalin Alhaji Nuhu sake kwanciya, ya ƙara kallan Hasina yace “Yi maza ki kira Samira.” Da gudu ta ruga, shi kuma ya kalli DPO yace “Baza’a iya jira zuwa gobe ba? Ko sallama batai da kowa ba.”

“Kamar yanda na faɗama zata iya rasuwa yau dan haka ina ganin a barsu suje daga baya sai su dawo suyi sallamar.” Jin haka yasa Baba yace “Nafi'u kuyi hakuri kuje kaji? Yanzu kaje kasa Kursum ta shirya.”

Mikewa yai ya fito ya nufi dakinta, tana zaune tana karatun Qur’ani sallama yai hakan yasa ta sallame sannan ta amsa tare da mikewa ta fito, yau sai yake ganin ta sake yi mai kyau, murmushi ne ya kwace mai yace “Kakata ce take san ganina kizo muje Keda Umma ku ganta.” Kanta ta sunkuyar tace “Hakan ya kamata?” Kai ya jinjina yace “Bazan iya tafiya ba sai dake dan kuwa ke matatace.” Kamar zata musa sai taga ya girgiza kai alamun a’a “Kaya fa? Zamu kwana ne?” Shiru ya ɗan yi sai kuma yace “Ba sai kin kwaso komai ba ki taho haka kawai.” Kai ta ɗaga ta koma dan ta shirya. Hijab ɗin Umma ta ɗauko da takalmi, suna fitowa Inna na dawowa, jin wannan labarin ba ƙaramin da ɗi ya yi mata ba nan ta rakosu har mota suka shiga tana addu’a a ranta Allah yasa sun tafi kenan har abada……

(Labari yanzu zai canza salo, ga dai Yazeed Shehu Kankarofi ga kuma Kursum Shu’aib Danbatta, anya tasan wanda take aure kuwa? Wace irin rayuwa zatai a garin da bata sani ba? Gidan da batasani ba? Hmmm case na gaba dan bakuji komai ba)

Katin waya MTN ta 07065283730

Sai shaidar biya ta. 07065283730 or +44 7894 142004

Ayusher Ce🏌🏻‍♀️

700 ne Kacal 🤌🏻
7065283730
Opay
khadija Abdullahi shehu.

Katin waya MTN ta 07065283730

Shaidar biya ta 07065283730 or +447894142004

Ayusher Ce🏌🏻‍♀️
*RIBAR ƘAFA*

NA

Wattpad :-AyusherMohd

Arewabook:- Ayushermuhd

ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️

*LAST FREE PAGES*

*700Naira Only…*

Paid Book

Shafi na Goma Sha Biyar

Tunda suka ɗau hanya Umma ke ta murna tana kale-kale da tafa hannuwa takeyi, dan raban da ta shiga mota ta daɗe. Daga ɗan nesa kaɗan DPO ya hango motar su Ummy kallan Yazeed Shehu Kankarofi dake zaune gefen mota yai yace "Ga motar su." Ɗan kallan inda motar take yai yace "Biyoni?" DPO ya ɗan saci kallansa, cikin rawar murya yace. "Wal..." Da sauri Yazeed ya ɗaga masa hannu yace, "Karka damu ka wuce kawai sa biyo mu." Bai san sanda ya sake ɗan kallanshi ba. Yazeed ya maida kanshi jikin kujera, fargabarsa ɗaya in Kursum ta gasu Ummy da babbar mota fa? In tace ya akai basu shigo ba suka tsaya a nan fa? Sannan bashida tabbas ma akan Kabir bai faɗa mata iyayensa sun rasu ba, dan haka babu abinda zai tsayar dashi anan, koma menene inya kaita gidanshi ayi. Salim cikin tsananin takaici yabi motar DPO da kallo yace "Ummy basu da niyyar tsayawa fa." Kallan motar tai tare da sauke ajiyar zuciya tace "Indai yana nan lfy bakomai mu bishi dalilin hakan ma yayi ƙoƙari daya sanar dani har muka taho dan da zai iya tahowa da kansa ba tare da mun sani ba, kaga tunda yace a sanar dani alamu ne na yasan me yakeyi." Dogon tsaki Salim yaja yace "Wallahi ku kuke ƙara ɓata yaran nan shi yasa baya ganin uban kowa da gashi, in har ku bai darajaku ba wa zai daraja?" Gyaran murya tai tare da mai alama da yai shiru. Ƙofar da ya buɗe yake shan iska ya jawo da ƙarfi dan har sai da tace "Kai Salim!" Bai amsa mata ba saboda baƙin cikin yadda suke yiwa Yazeed tamkar shine a saman su. Nan driver yaja suka tafi. Tunda suka fara bin motar su Yazeed babu wanda kewa wani magana dan Ummy ta kula ran Salim a ɓace yake shi yasa ta ɗau waya ta sanar da Yasmeen akan tasa a gyara mai ɓangarenshi kafin su iso.
Chapter 25 · 0% Book details