Sashe 4
Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Ya kamata ka tashi kuwa? Ka koma ka kwanta naje na kira Nurses su dubaka kaga an maka dinki a gefen kanka. Sannan kwana kai a kwance." Bai musa ba ya koma sai dai zama yai a bakin gado yana shafa inda yake jin shi kamar a tamke a saman kansa. Alhaji Nuhu Danbatta da sauri ya fita waje bai dade ba sai gashi ya dawo tare da nurses biyu. Nan suka umarceshi ya koma gado suka sa karamar fitila suka haska idanshi tare da bashi umarni akan ya kalli gefe da gefe, suka tambayeshi in ana jin ciwo yace a'a. Nurse din tasashi daga hannu da kafarsa komai yai cike da nutsuwa. Ajiyar zuciya tai tace.
"Ya sunanka?" Kallan Alhaji Nuhu Danbatta yai wanda shima kallanshi yake, da mamaki ta sake maimaita tambayarta sai dai kamar ɗazu kallan Alhaji Nuhu Danbatta ga sake yi. Ganin haka yasa Alhaji Nuhu ya matso yace.
"Sunanka aka ce, ya su nan ka?"
Kai ya girgiza yana sake kallanshi sai kuma ya fara alamun tunani. Wani azababen ciwon kai ne ya shige shi dan baisan sanda ya saki wata kara ba. Kabir dake bacci ne ya ɗiko ƙasa a tsorace ya mike yana kallansu. Nurse ɗin dake kusa dashi tace.
"Karka damu koma ka kwanta zuwa anjima." Tai maganar tana yiwa Alhaji Nuhu Danbatta magana akan a kyaleshi. Tare suka fito nan suka kalleshi ɗaya tace.
"Zan ƙira Dr na sanar mai probably suyi requesting CT scan...." Ajiyar zuciya yai yace.
"Me kenan?" Nurse ɗin tace.
"Kamar X Ray yake amma shi computer tana daukan hoton duka jiki ne har zuwa kwakwalwa." Kai ya jinjina alamun gamsuwa. Nan suka juya. A hankali ya juya ciki yana zuwa ya tadda Kabir akan saurayin yana cewa "Satowa kai ko? Ahaf ai wallahi nasan a rina." Rai a mugun ɓace yace.
"Bakada hankali ne? Yaran dake kwance bashida lafiya shine zaka din ga yiwa tambayoyin banza da wofi." Shi kuma saurayin sai murmushi kawai yakeyi kai kace wani abin farin ciki ne ya sameshi, idanshi na kansu amma bakinshi ya kasa rufuwa. Ba jimawa Dr ya turo aka sanar da Alhaji Nuhu Danbatta akan zasuje Kano ai CT scan dan basuda machine din anan cikin Ɗanbatta. Kallan Kabir yai ya sauke ajiyar zuciya ya kalli saurayin dake ta kallansu yana murmushi yace.
"Ka sanar Kano?" Murmushi ya sake yana cewa,
"Sunana?" Kabir ya sheke da dariya yace.
"Kai wawa gari fa Kano ake nufi, a can kake ne? In mukaje zaka gane gidanku?" Kallan Alhaji Nuhu yai yana cigaba da murmushi yace.
"Kanina ne ko Yayana?" A tare suka sauke ajiyar zuciya Alhaji Nuhu Danbatta ya matso yace.
"Zan gwada ƙiran ka da sunaye duk wanda kaji yayi kama da naka ka ɗaga kai." Kabir ya matso shima yana cewa.
"Baba wallahi kasan yanda za'ai mu maida yaran nan kaga abinda zamu je yi Aminu Kano wallahi ni nasan kudi za'aci da yawa, kuma ina mukaga kudin?" Bai amsa mai ba ya fara cewa.
"Muhammad? Ahmad? Kabiru? Nazifi? Salmanu?" Haka ya dinga ƙiran sunaye banda kallansa ba abinda saurayin nan keyi har kuma yanzu murmushi yake. Kabiru ya zabga mai harara yace.
"Sai wani murmushi kake kamar wani wawa, kaga Baba share maganar sunan nan muje Kano kawai mu ajiyeshi a police station haka kawai bazamu ɗauki ɓarawo mu kaishi gidan mu ba."
Shi kanshi Alhaji Nuhu Danbatta ya gamsu da ajiye saurayin a police station in yaso sa nemi yaran wanene su maida shi ba wai dan ɓarawo ko rashinsa ba sai dan yana tausayin halin da iyayensa zasu shiga na rashinsa.
(Ni kaina na kasa gane meke faruwa? Muje zuwa🤸🏻♂️)
Littafin nan na kuɗi ne, ki biya ɗari 700 ta
7065283730
Opay
khadija Abdullahi shehu.
Katin waya MTN ta 07065283730
Shaidar biya ta 07065283730 or +447894142004
Bonanza ki biya 500 daga yau zuwa 12th ga wannan watan kunsani ni da ku 5&6🥰
Ayusher Ce🏌🏻♀️
*RIBAR ƘAFA*
NA
Wattpad :-AyusherMohd
Arewabook:- Ayushermuhd
ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀️
Page 3
Wani Dr ne ya sake shigowa sai dai duk yanda yake mai tambayoyi yaran ya kasa gane me yake nufi. Kallanshi kawai yake yana kallan Baba dake tsaye ya dafa kai, dan har wani ciwon kai ya kamashi ganin abubuwa daga jiya zuwa yau sunata faruwa. Bayan Dr ya gama bincikensa nan ya basu takarda akan suje Aminu Kano ayi CT scan wanda anan ne za'a tabbatar da hakikanin meke damun memory ɗin shi. Alhaji Nuhu Ɗanbatta ne ya bishi da kallo zuciyarshi cike da tausayin yaran dan baifi sa'an Kabiru ba. Ya tabbatar iyayensa na nan na nemansa, dan duk girman nan idan ka nemi mutum ka rasa dole ka shiga tashin hankali. Murmushi kawai saurayin ke mai wanda ke sake karya mai zuciya. Cike da tausayi yace. "Muje gida kaci abinci sai mu wuce Kano ɗin ko?"
Da sauri Kabiru ya matso yace "Baba motarka fa sai an duba lafiyarta, sannan bamu da kuɗin biyan na motar haya. Kawai ka ajiye shi a titin nan ka zare mai ido kace ya kama gabanshi ko ka kaishi police station ɗin garin nan."
Takaici sam ya hana Alhaji Nuhu Ɗanbatta magana, ya rasa wani irin kwakwalwa Kabir keda ita. Ganin bazai kulashi ba yasa ya koma inda yaran yake ya ɗan bangaji kafadarsa yace "Muna zuwa gida zaka cire kayanka ka bani su, kai kuma kasa nawa ai ko banza ka dai biya mu aikin wahalar da muka yi maka."
Kai kawai ya ɗaga alamar to yana sake murmushi. Sun fara tafiya saurayin ya fara jin jiri wanda hakan yasa shi yin baya kamar zai faɗi. Da sauri Kabir yasa hannu biyu ya tareshi yace "Kalau kake?" Jin haka yasa Alhaji Nuhu Ɗanbatta matsowa kusa dashi hankali a tashe. Hannu yasa ya riƙe shi ya jashi gefe tare da nuna mai waje ya zauna akan mashin ɗin Kabir, jikinsa sam ba ƙarfi ya zauna sai dai har a lokacin sama sama yake fitar da numfashi. Sai yanzu ya gane meyasa Dr yace a barshi ya huta, in so samu ne a kawo motar da zasu je Kano da ita bakin asibitin sai a saka shi a cikin motar da wheelchair. To amma shi ya zai yi? Ba kuɗi a hannunsa bare mota, gashi wayarsa tun jiya ta mutu. Amma in sukaje gida bazai rasa mutanen unguwa wani da zai taimaka mai da bashi ba. Sun daɗe a zaune kafin komai ya daidaita. Alhaji Nuhu Danbatta ya kalli Kabir yace "Ka wuce dashi gida amma dan Allah kayi tuki a hankali kar kaje kanshi yai ciwo. Ni kuma zan san yanda zanyi na ƙaraso." Kan titi ya kalla wanda motoci tsila-tsila ne ke wucewa suma a guje yace. "In muka wuce ya zakai ka dawo?"
"Kai dai ka wuce nima yanzu zan ƙaraso, ka kuma tafi dashi a hankali kana ganin bashi da lafiya.” Ganin Baba bai bashi damar magana ba yasa ya hau suka tafi suka nufi kauyen FAGWALAWA dake karkashin hukumar Ɗanbatta. Suna tafe a mashin saurayin na kallan kauyuka galala kai kace a lokacin ya fara ganin kauye haka.
Alhaji Nuhu Ɗanbatta ya ɗan fara tafiya da ƙafa, yana tafe yana tunanin abinda ya kamata yai, addu'a kawai yakeyi akan Allah ya kawo mai mafita. Ko dai motarsa zai sa a kasuwa? Wayarsa ba chaji da yanzu ya samu ya sanar da mutanensa wani ya taimaka mai da rancan kuɗi. Kamar daga sama yaji ance "Baba baka tafi ba? Ina Kabirun?" Waigawa yai ga mamakinsa Dr ne, juyowa yai gaba ɗayansa, yace "Yanzu nake neman abin hawa, Kabir ya tafi gida da mara lafiyan, ni kuma inaso na leƙa inda akai hatsarin akwai abinda nakesan dubawa kafin na wuce." Kallansa yai ya kuma kalli agoggonsa yace "Bari na yiwa masinja na magana yana da mashin sai ya maida kai ni kaɗai ne yau anan in na fita kaika wani abu zai iya faruwa azo kuma babu likita." Godiya sosai Alhaji Nuhu Ɗanbatta yai dan in yace a'a to fa ba yanda zai yi ya koma gida balle harya samu damar wucewa Kano, gashi har sha ɗaya na safe tayi. Godiya ya sake yiwa Dr har yayi gaba ya waigo yace “Baba kai mutumin kirki ne kowa zaima wannan shaidar sai dai karka takura kanka akan abinda bakada halin yi. Yaran nan ka sa a nemi danginshi suje su nema mai magani domin daga ganinsa kasan bawai talaka bane bare kace ba yanda iyayensa zasuyi.” Kai ya jinjina sannan yace “Nagode sosai Allah ya saka muku da alkairi.” Yana tsaye Dr ya koma ko minti biyar da shiga baiyi ba sai ga wani masinjan ya fito. Nan ya ɗau Alhaji Nuhu Ɗanbatta suka wuce. Inda akai hatsarin suka fara zuwa sam babu alamun hatsari agun sai bishiyar da motarsa ta buga wanda ya sake tabbatar mai da hatsarin nan anan gun sukai. Ba yanda ya iya haka suka wuce yana nuna mai hanya sai dai sam hankalinsa ya kasa kwanciya, ko dai sace motar akai?