Sashe 16
Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan kwana biyu. Yau garin ruwa ake yi sosai. Shiru garin yayi tsit sai karar ruwa dake sauka saman kwano da kan ciyayi da kadawar iska kawai kake ji. Can cikin baccinsa yake jin wani abu na rike mai gabobin jikinsa, numfashinsa ne yake alamun daukewa, dan kuwa dakyar yake iya jawoshi. Hannu ya kai dakyar ya fara taba Inna dake ta sharar bacci kusa dashi, sam bata jishi ba. Da kyar ya iya jan kafafunsa zuwa ƙasa tare dakai hannu inda maganinshi yake. Faɗowa yai a ƙasa wani irin gumi ne yake tsatsabomai, jikinshi gaba ɗaya ya mai nauyi kamar wanda aka danne shi. Jan jiki ya fara yi dakyar ya sa mu ya kamo maganin, sai dai kafin ya dauka ya fadi anan gurin ya dinga murkususu har sai da ciwon ya lafa mai, wani nananuyan bacci ne yai gaba dashi a wajan. Har akai sallar asuba bai farka ba. Nafi'u yayi mamakin ganin Baban bai fito ba, dan kullum tare suke fita ya tsaya suyi karatu sai ya dawo ciki. Shi kuma Nafi'u sai ya jira Kursum, dan yanzu kullum tare suke tafiya makaranta da ita. Rahina ta ma daina jiranta dan ta kula ko ta jirata ma daga baya sai tayi gaba ta barsu ita kanta tana mamakin yanda akai shakuwa ta shiga tsakaninsu haka. Kofar ɗakin yaje yanasan kwankwasawa kuma baisan ya tashesu, har yayi gaba yaji zuciyarshi taƙi kwanciya. Dawowa yai jiki a sanyaye yace "Baba! Baba kana nan?" Shiru babu alamun amsa ya sake ƙira nan ma shiru. Hannu yasa ya ɗan kwankwasa ƙofar a hankali. Inna dake kwance itace ta farka ganinta ita kaɗai a kan gado yasa tace "Malam wannan kuma neman magana ne? haka kawai dan zaka tasheni sallah ba sai kayi tallata makota ba ah to." Nafi'u na waje ya dai ji ana magana amma baisan me ake cewa ba, wanda shi kuma hakan yasa hankalinshi kwanciya. juyawa yai zai tafi ita kuma Inna ta sauko daga kan gado, jin tayi tuntube da abu yasa ta kunna haskan karamar touch light ɗinta. Ihun da ta zabga ne yasa Nafi'u dawowa da gudu. Sake zabga ihu tai tana kwallawa Kabiru ƙira cike da tashin hankali. A guje Nafi'u ya shiga ciki ganin Alhaji Nuhu Danbatta a ƙasa yasa hankalinshi yai mugun tashi. Da gudu ya ƙarasa inda yake ya dagoshi sai dai sam babu motsi a tattare dashi. Maidashi yai kawai yasa hannayensa biyu a kirjin Alhaji Nuhun ya hadasu ya fara danna mai yana ɗan bada lokaci yana daga wuyanshi tare da sauraran numfashin. Ihun da Inna keyi ne ya tashi su Kursum da Umma sukai saurin fitowa dasu Raheena. Hankalinsu ba karamin tashi yai ba ganin Nafi'u nata kokarin dawo da numfashin Baba wanda ke kwance kamar gawa. Ihu Umma ta fara tana "Wayyo Baba ya mutu wayyo Baba!" Tana yi tana bubuga ƙafa kan kace me makota sun shigo gidan. Hankalin kowa ya tashi dan Alhaji Nuhu Danbatta mutumin kirki ne. Nafi'u banda gumi ba abinda yake yi. Sai da yai na minti ashirin dan har jikinshi ya bashi shikenan sai sukaji anja wani irin numfashi. Jikinsa na rawa ya kalli wani makocinsu yace "Mota mu tafi asibiti."
Da gudu saurayin ya fita shi kuma ya fara kokarin sashi a baya. Nan aka taimaka mai aka fito dashi. Motar makocin aka sakashi har zai rufe ƙofa idanuwansa suka sauka kan Kursum wacce ke rike da Umma tana ta birgema akan sai ta bisu. Kallo daya zaka mata kasan bata cikin hayyacinta. Har zai rufe kofar motar Inna ta rike tace "Ku jira an tafi a taso Kabiru ai dai ba yanda za'ai a tafi asibiti babu jininshi ko?"
Basu musa ba suka dakata. Da gudu Kabiru ya fito yana gyara wando dan bacci yake Hasina ta tashe shi, haka suka shiga aka ja motar suka tafi. Hankalinshi ba karamin tashi yai ba ganin mahaifinsa baisan halin da ake ciki ba, jikinsa kawai rawa yake banda addu'a babu abinda yake furtawa. Nan asibitin kusa dasu aka kaishi dan tun kafin su iso mai unguwarsu ya kira ya sanar da ciwon Alhaji Nuhu shi yasa suna zuwa aka shiga dashi ciki. Suna nan a zaune su Inna suka karaso suma dukansu a motar shugaban makarantar islamiyan Alhaji Nuhu Danbattan. Duk kowa yayi jugum-jugum zuciyar kowa a tsorace take da abinda ke faruwa.
Nafi'u ganin Kursum bata cikin asibitin yasa ya kalli Raheena wacce ta mai alama da waje da kanta dan tana kallan yanda ya kalleta ta gane me yake san ji. Mikewa yai ya fito waje, tana zaune a gefe ta takure gaba daya ta rasa tunanin me zatai. Allah shine gatansu Alhaji Nuhu shine gatansu inhar wani abu ya sameshi shikenan ita kuma rayuwarsu ta tagayyara dan kaf duniya basu da kowa daya wuce shi. Ya zasuyi? Kamar daga sama taji ance "Allahuma ajirni fi masibati wa akhlifni kairan minha!" Dagowa tai idanuwanta suka sauka kan Nafi'u wanda yake tsaye yana kallanta. Kamar wacce aka taɓa sai jitai ta fashe da kukan da take ta kokarin ɓoye wa. Hawaye ne kawai ke zubo mata kamar wanda ake turo su. Zama yai gefenta kadan hannu yasa aljihu sai dai jin babu komai a ciki yasa ya fito da su. A hankali yai gyaran murya yace "Umma fa?"
Bayan hannunta tasa ta share hawayen cikin maganar kuka tace "Tana makotan mu, Ya Nafi'u kana ganin Baba zai tashi kuwa?"
Ɗan kallanta yai kaɗan ya buɗe baki zai magana ya juyo muryar Inna na fada daga gefe, da alama batasan suna gun ba. Cike da fada take cewa "Bakada hankali ne da zakace a saida gonar da ita kadai muke dashi a biya kudin asibiti? Ka wuce ka sanar da mai gari halin da ake ciki shi yasan yanda zai yi a tara mana kudin asibiti ai mahaifinka suna ganin girmansa amma ba wai mu saida abinda yake rikemu ba. Kai fa kafi kowa sanin da noman gonar nan muke rayuwa." Kabir da mamaki yace "Baba ne fa baida lafiya, dama a wannan halin har za'ai tunanin wani abun duniya ne? Babu wanda zan roka abinda muke dashi duk a tattaro a bashi kulawa."
A fusace Inna ta kalleshi tace "Kana tunanin da san raina na fadi hakan? Ko nice a kwance a gadan asibiti bazan bari ku kwashe abinda zai rekeku ku kula dani ba." Sai kuma tai shiru kamar mai nazari kafin tace "A sa gonar Kursum a kasuwa, hakkinta ne ta kawo tata gonar a saida dan kuwa tafi kowa sanin da abin mu take amfani. Dan haka tamu gonar itace mai rike da ita da uwarta."
Mamakin kalaman Inna gaba daya ya hanashi magana bata jira mai zai ce ba ta juya ta barshi a gun. Ko motsi ya kasa dan bai taɓa kawo jin haka daga gareta ba. Muryar Kursum ce ta katseshi, tana tsaye daga gefe tace "Ya Kabir ka sashi a kasuwar, Inna babba ce ta fimu sanin dalilinta na yin hakan."
Waigowa yai idanunsa sunyi jaa ita kanta Kursum bata taɓa ganinshi cikin yanayin nan ba. Kabir mutum ne mai barkwanci da tsokana. Murmushin yake ta sakar mai tace "Ka kira Mai unguwa bazasu rasa wanda zai siya ba." Tana kai nan ta sake yin murmushi sai ta shiga ciki.
Nafi'u yabi bayanta suka bar Kabir a tsaye. Wata iska mai zafi ya furzar daga bakinsa. Kiran Mai unguwa yai yana sakawa a ransa tabbas jinginar gonar zai bada wanda zaiyi kokarin hada kudin ya maida musu. Shi kam bai taɓa jin haushin rashin aikin yinsa ba sai yau dan kuwa da ace yanada abinyi bazai rasa wani abin ba. Sunfi awa biyu a waje ana jiran fitowar Alhaji Nuhu Danbatta kafin a fito dashi. Kallo ɗaya zaka mai kasan da matsala dan kuwa garkame yake da abun taimakawa numfashi wato Oxygen, sannan idanunwansa a rufe suke kamar wanda baya cikin hayyacinsa. Da gudu suka bisu har aka shiga dashi wani ɗaki. Dr ya kalli Nafi'u kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya maida kallanshi kan su Inna gaba dayansu kowa yayi tsuru-tsuru a ɗakin, ya sauke ajiyar zuciya yana kallan Alhaji Nuhu Danbatta dake kwance kafin yace "In Kabiru ya shigo ya sameni a office."
Har zai fita Inna tace "Ba Kabiru kadai ba mu kanmu muna san sanin meke faruwa, bawan Allahn nan meya sameshi? Dakyar numfashinsa ya dawo dan har mun cire rai lokacin."
Waigowa yai gaba dayansa ya kalli Inna yace "Shi yasa dole a godewa Allah a kuma godema yaran sa ya mai CPR dan da tun lokacin sai dai kuma wani ba shi ba." Inna ce tai saurin cewa “To meke faruwa? Ciwon ba na tashi bane?”
Gaba ɗaya kallanta akai su kansu su Raheena sai da jikinsu yai sanyi. Shin meke damun Inna ne? Anya ba tsorata tai da abinda ke faruwa ta fara sakin baki haka ba?
Dr ganin yanda tai magana yasa ya kalli Alhaji Nuhu Danbatta wanda ke kwance rai a hannun Allah, dan duk da oxygen din da yake shaka numfashinsa bai daidaita ba. Yana kallanshi yana cewa “Pulmonary edema yake dashi, wanda ruwa ne yake taruwa a lungs to in ruwan ya taru dayawa sai ya haifar da raunin numfashi a indda ruwan ke toshe hanyoyin dake ba jijiya iskar da zata fitar. Sai dai a nashi case din da alama ya dade yana fuskantar kananan alamomi bai kawo wani abu bane har sai da ciwon yaci jikinsa.”
“Inalilahi wa ina ilaihi raji'un." Abinda kawai mutanen ɗakin ke faɗa kenan. Kabir dake tsaye a bakin kofa jikinsa nan da nan ya fara futar da gumi, taya mutumin dake da lafiya jiya daddare yau za’a sanar da irin wannan cuta a kansa?
Dr ne ya taho inda yake ya mai alama daya fito. Suna fita daga ɗakin ya kalleshi zuciyarsa a karaye yace “Sai dai kuyi hakuri amma da kyar in zai iya tashi, ciwon nan ya dade yana cinsa babu wani magani da yake sha? Dan nayi mamakin yanda akai bai fuskanci komai ba.”
Hawaye ne ke zubowa daga idanun Kabir bakinsa na rawa yace “Sai dai na hausa amma bai yadda da maganin asibiti ba.”
Kai ya jinjina yace “Kabir ku tsaya a kansa lokacinsa tafiya suke.”