← Book details Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 27

Sashe 23

Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Agida kuwa Kursum wanka tai tasa atamfar sallar ta wanda Alhaji Nuhu Danbatta ya ɗinka mata. Haka kwai takejin gabanta na faɗuwa, ta kuma kasa ɗauke hankalinta daga jikin ƙofa. Tana nan a ɗaki yaran makocinsu ya shigo da gudu yasanar da ɗaurin auran, wani abu ne taji ya ratsata da sauri ta shige cikin bargo kamar mai bacci sai dai tana juyo Umma na tsalle tana tambayar yaran wai itama an mata auran? Inna ce ta fito, Umma tana ganinta ta fita waje tana tsalen tun kafin Inna ta hauta da faɗa. Komawa ciki Inna tai fuskarta shar da fara'a tana dariya ta kalli Alhaji Nuhu tace "Hankalinka sai ya kwanta aure dai an ɗaura sai mu fara nema musu ɗan gida su koma can." Idanunsa na kanta yace "Hankalinki dai ya kwanta, har yanzu a gurina Kursum bata kai a takura sai tai aure ba, kawai dai tunda kin damu sai fatan Allah ya bata zaman lafiya." Wani kallo ta mai yana kula da ita a hankali tunda ya fara ciwo raininta yake karuwa ko yanda takemai magana yanzu da kuma da ba ɗaya bane. Nafi'u ne ya shigo tana ganinshi ta saki dariya tana "Lale lale Ango Allah ya baku zaman lafiya." Bai amsa mata ba sai cewa dayai "Baba fa?" Ta nuna mai ciki kai tsaye ya shig ciki. Kusa dashi yaje nan Baba ya ɗaura hannu kansa ya fara mai addu'a. Ɗago wa yai yana murmushi sannan ya kama hannunsa yace "Nagode Nafi'u fatana Allah ya baku zaman lafiya, na sani wahala ce muka daura maka amma ina rokon ka taimaka ka kulamin da ita, yarinyar nan abar tausayi ce." Tari ne ya kwace mai wanda ya hanashi cigaba da maganar sa. Da sauri ya sa mai oxygen ɗin yana tunanin lalai yana buƙatar ganin babban likita tun kafin abin yaci jikinshi sosai. Cikin oxygen mask ɗin Alhaji Nuhu Ɗanbatta yace "Kaga Kursum ɗin?" Kai ya girgiza alamun a'a wanda hakan yasa ya jinjina mai kai alamun yaje ya ganta. Mikewa yai dan shi kanshi abinda yakeso kenan. Har yakai ƙofa ya waigo ya kalli Baba sannan yai murmushi ya fita. Wucewa yai ɗakin Kursum, har lokacin tana cikin bargo. Raheena ce ta ganshi cike da jin daɗin ta tace "Hmm su Ya Nafi'u ni dama tunda naga kana zaman waje har sai tazo ka rakata makaranta jikina ya fara bani akwai wani abin a tsakanin ku." Bai amsa mata maganar da take ba sai cewa yai "Tana ciki? Kice ta leko mu gaisa." Hasina ce ta fito tana ɗan tabe baki tace "Tunda ka zama mijinta ai sai ka shiga daga nan sai ku tattare kayanku, ni banga mai ka gani jikin Kur....." Wani kallo ta gani a idanuwan Yazeed wanda haka kawai taji shakkar kasa magana, da sauri ta koma ciki. Ƙofar ɗakin ya tsaya Rahina ta buɗe baki zatai magana taga kawai ya shiga. Kai ta jinjina ashe shima ba shida kunya? Kursum kuwa sam bataji motsin komai ba tunanin yanda lokaci ɗaya rayuwa ta canza mata take, wace rayuwa zasuyi ita da Umma? hannu taji a saman kanta, a ɗan tsorace ta ke yaye mayafin jikinta, ido ta zaro a zabure ta fara ƙoƙarin mikewa, gaba daya ta rikice dan tunda Allah ya halliceta yau ne ta taɓa ganin namiji dab da ita haka. Wata shakuwa ce ta kwace mata ba tare da tasan daga inda tazo ba, ta fara ƙoƙarin tashi ta ruga. Hannu yasa ya maida kafadarta ta kwanta a inda take, wani irin mugun faduwar gaba takeji da sauri ta maida bargon ta rufe fuskar ta. Wani sanyayen murmushi yai yana san sanar da ita ta shirya anjima zasu bar kauyen amma baisan hankalinta ya tashi, sunkuyowa yai dab da ita yace "Ina sako na?" Har lokacin fadawar gaba bai barta ba fuskarta na cikin bargon tace "Wanne?" Cikin dakushashiyar murya yace "Congratulation mana." Kunya ce ta kamata ta sake dukunkunewa, zatai magana sukaji an maida kofa da karfi an rufe alamun wani ya shigo ne ya rufe ƙofar. Kallan gun yai Kabir ne ya nufoshi kamar wani kumurci sai huci yake yana hura hanci, sai daya shigo tsakiyar ɗakin sannan yace "How dare you?" Yazeed Shehu Kankarofi ya miƙe tsaye yace "Ni ko kai?" Kabir zuciyarsa banda tafasa ba abinda take cike da kunar rai yace "Nama kasa gama tunanin abinda ka aikata mana, duk a wani dalili? Gaba ɗaya zuciyata ta kasa samun amsa, kai kuma sai raina min hankali kake." Tsaki yai ya tako inda yake tare da yin gaba sai da yaje daidai ƙofa yace "Don't do anything stupid, bakasan wanene ni ba." Yana kai nan yabar ɗakin. Kursum da ta mike zaune jin kalamansu yasa ta kalleshi cike da san sanin meke faruwa, ta sani sun saba samun matsala amma na yau kamar ya banbanta da ko da yaushe. Kabir ta gani yana mata wani kallo, juyawa yai shima yana maimaita kalaman da Yazeed Shehu Kankarofi ya mai wato in yana san abu? Kenan saboda Kursum yai? In har hakane lalai bashida hankali, taya mutum zai aikata hakan indai da cikaken hankalinsa?

KANO......

Mace ce wacce batafi kimanin shekaru hamsin ba tana kwance akan makeken gadanta wanda a kalla yayi ƙaramin gidan wani mai rufin asirin, dan kuwa duk girman gadan a cikin tafkeken ɗakin ba komai bane ba, daga gefen ɗakin ma ƙaramin falo ne wanda ke ɗauke da saitin kujeru da tv. Sannan ɗaya ɓangaren wata doguwar kujera ce irin ta hutawar nan, daga gabanta kuma ɗan ƙaramin round table ne ɗauke da kujeru biyu. Yarinya ce zaune kusa da ita tana matsa mata ƙafa. A hankali ta janye kafarta ta kalleta tace “Tashi kije ki kira min Yasmeen.” Mikewa budurwar ƴar tai jiki a sanyaye tace “Ummi ki fito kici abincin.”

Murmushi tai ta ɗan mike zaune kaɗan wanda hakan ya bani ikon kallan tufafin jikinta da kamaninta. Kallo ɗaya zaka mata kasan mai kyau ce ba wai haske ba a’a kyau na bakar fata mai diri. Fatar ta a mulmule take alamun hutu da kwanciyar hankali sun zauna a jikinta. Yarinyar ya kalla tace “Basira karki damu bana jin yunwa ne.” Juyawa yarinyar tai ta fita wanda hakan yasa Ummi kallan ƙofar, tana ƙoƙarin maida kanta kan gadan taji wayarta na ringing. Ɗauka tai da sauri ganin kaninta ne. Cikin sauri tace “Salim ya ake ciki? Har yanzu ko?” Daga can ɓangaren wanda ta kira da Salim yace “Kiyi hakuri Ummi….” Cikin tsawa ta katseshi tace “Bana san wani hakurinka na banza, menene matsayin muka min da aka baka? Aure na kake so ya mutu na dawo gida mu zauna ko? Kafi kowa sanin duk sanda Senate yasan abinda ya faru daga ni har kai bazamu zauna a gidan nan ba, nayi karyar Yazeed ya tafi wata ƙasar karka manta daga sanda ya tabbatar karya mu keyi shikenan komai da muka daɗe muna yi zai ruguje.” Ajiyar zuciya yai shikanshi kwanan nan ko nutsuwa bashida ita, yana ƙoƙarin magana tai saurin cewa “Mun samu mun ɓoye har wannan lokacin inhar tsautsayi yasa Magajiya ta sani kadai san magana ta kare.” Zufar dake keto mai ya share tare da sauke ajiyar zuciya yace “Ummi ga DPO ɗin yana ƙira bari muji.” Ɗan ƙaramin tsaki tai tunda Yazeed ya ɓata har yau bata da nutsuwa ta sani kiris zai iya sawa rayuwarta data ƴan uwanta su tarwatse. Kafafuwanta ta zuro tare da dafa kanta dake sarawa, yau a yanda aka sa bikinshi da yarinyar abokin Senate saura sati biyu kenan kuma ta musu alkawari zai dawo kafin nan a cewarta ai duk inda ya shiga kafin nan za’a ganshi. Ido ta runtse ta sani darajar Yazeed kaɗai takeci a gidan nan, dan haka in har wani abin ya sameshi shikenan ita kuma.

Ƙiran Salim ta gani da sauri ta ɗaga tace “Ya ake ciki?” Muryarsa har tana hardewa yace “Ummi an ganshi! An ganshi anan wani kauye dake Danbatta.” Da sauri ta sauka daga kan gadan tace “Gani nan zuwa, kai maza ka shirya kaima ka fito.” Mayafinta kawai ta sa ta dau jaka, tana ƙoƙarin fita sai ga Yasmeen, cikin sauri tace “Yasmeen zanje na dawo!” Bata ko jira amsarta ba ta kule ɗakin ta ta fito, zuciyarta bugawa kawai take tana fatan Allah yasa ba wani abin yaje ya sha ba ya ja mai wani ciwon dan da hankalinshi ba yanda za’ai ya kai kwanaki haka bai dawo gida ba…..

(Wani abu yasha? Yazeed Shehu Kankarofi shine cikakken sunanshi kenan? Yayi ciwon mantuwa? Ya warke ne? Me ya zaunar dashi a kauyen? Nidai Ayusher na zama ƴar kallo)

Littafin nan na kuɗi ne, ki biya ɗari 700 ta 7065283730 Opay khadija Abdullahi shehu.

Katin waya MTN ta 07065283730 Shaidar biya ta 07065283730 or +447894142004

Ayusher Ce🏌🏻‍♀️

Katin waya MTN ta 07065283730

Sai shaidar biya ta. 07065283730 or +44 7894 142004

Ayusher Ce🏌🏻‍♀️

700 ne Kacal 🤌🏻
7065283730
Opay
khadija Abdullahi shehu.

Katin waya MTN ta 07065283730

Shaidar biya ta 07065283730 or +447894142004

Ayusher Ce🏌🏻‍♀️
RIBAR ƘAFA

NA

Wattpad :-AyusherMohd

Arewabook:- Ayushermuhd

ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️

Paid Book

Littafin nan na kuɗi ne, ki biya ɗari 700 ta 7065283730

Opay

khadija Abdullahi shehu.

Shafi na Goma Sha Huɗu
Chapter 23 · 0% Book details