Sashe 3
Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kai dai ka dawo zan je da kaina ni da nake da kafata meya haɗani da wani video? kudai kuje can kuyi tayin abinku." Kashe wayar yai sannan ya ɗan yi karamin tagumi, kodai yaran nan tahowa yai a ƙafa? Sai dai shi da ba makaho ko kurma ba taya zai kasa banbance ƙarar mota da ta mutum? Key ɗin motar dake hannunsa fa? Saman goshinsa ya shafa babu mai iya warware matsalar nan sai yaran nan wanda har yanzu yake kwance yana bacci, gashi an duba kaf babu sunanshi bare wani alamu na address ɗin shi. Ajiyar zuciya yai da badan masu asibitin an sanshi ba an kuma san shi wanene ba, da sai yasha tambayoyi kafin a karɓi yaron. Yana nan yana sakawa da warwarewa ya juyo takun Kabir wanda ko bai tambaya ba yasan wanene dan Kabir komai nashi mai ƙara ne baya taɓa abu a hankali. A bakin ƙofa yaga Alhaji Nuhu Danbatta yana shigowa yace.
"Zauna ka bani mukulin mashin ɗin ka naje na duba." Kallansa yai sannan ya kalli waje yace "Baba in na baka mashin ɗina ta ina zaka fara tukawa? Bafa kasan yanda ake jan mashin ba." Tsaki yai yace.
"Na iya mota shekara da shekaru sai wani ƙaramin abu mashin ne bazan iya ba? Ka ba ni ka matsa ko sai na makeka."
"Zan bada amma duk abinda ya samu mashin ɗina Kursum sai ta biyashi in kuwa ba haka ba na jibgeta wallahi." Mamakin jin furucin yasa Baban nashi sakin baki yana cewa.
"Tunda jaka ce ita dole ka jibgeta ai, kai wai sai yaushe zakai hankali ne? Matar da zaka aura ma baka darajata ba to wa zaka ga kima da mutunci?." Da Kabir ya fara dariya har sai da yaga Alhaji Nuhu Danbatta ya murtuke fuska alamun ba wasa ya daina yace.
"Baba kasan duk randa kace zaka aura min wannan ƴar ficikar to fa duniya zan shiga ni dama duniya bazata min wahalar shiga ba." Ƙwafa Alhaji Nuhu Danbatta yai, zai sake magana Kabir yai saurin mikamai gefen fitilar motar da wayarsa yace yana cewa.
"Duba ka gani wallahi babu komai sai wannan, sannan ga motarka nan inda ta gangara gefen titi." Ya ƙarasa maganar yana nuna mai video ɗin daya ɗauka. Mamaki ne ya ƙara bayyana a fuskar Alhaji Nuhu Danbatta dan har sai da ya ware idanunsa yana sake kalla, bai san sanda ya amshi wayar daga hannun Kabir ba yana cewa.
"Nan ne wajan kuwa wallahi, ga mota ta nan." Duk yanda yaso ya duba babu alamun motar saurayin da sukai gware dashi. A hankali ya sauƙe wayar daga hanunsa cike da mamaki yake kallan yaran nasa da alamu dai dole ya jira zuwa safiya ya sake duba gun nan. Sannan ba mai iya faɗan takamaimai meya faru dasu ba sai wannan yaran. Kabir ne ya matso kusa da saurayin yace.
"Baba wannan yaran da alamu ɓarawo ne biyo shi aka yi, kaga wannan takalmin? wallahi satoshi yai dan brand ɗin ma bana ƙasar nan bane, hauka ake da zai iya siyan New Balance? Sannan kaga wannan rigar daya saka? Sunanta hoddie sannan na brand din Nike ne kana gani kasan sata yai....." Tsakin da Alhaji Nuhu Danbatta yai shine ya sashi yin shiru, yana kallanshi cike da takaici yace.
"Kai haukan dake damunka kenan? In nashi ne kuma fa?" Ido KB ya zaro yace.
"In nashi ne Baba wallahi kazo musa gudu dan da alama iyayenshi masu kudi ne, tsaf za'a kulemu ni da kai." Kai kawai ya girgiza dan shirman Kabir karuwa yake ya rasa sanda yaran nan zaiyi hankali.
*****
Kursum da sauri ta shigo gidan dan sam bata iya daɗewa inta fita sakamakon halin da mahaifiyarta ke shiga. Tana shiga ta fara jiyo kukan mahaifiyar ta. A guje ta auna ciki har tana buge kafarta ta hago, sai dai bata bi takanshi ba ta shiga ciki tana hakki tare da ƙiran sunan Umma. Ganin bata ɗaki yasa ta fito. Ba kowa a tsakar gidan sai ɗakin Adda Yagana dake ɗauke da fitila kana juyo dariyarsu ita da kanenta. Cikin ɗakinsu Adda Yagana ta shiga da sauri ba ko sallama ta yaye labulen tana ƙiran.
"Umma! Umma!" Mamaki ne ya kamata ta tsaya turus ganin mahaifiyarta rakuɓe a gefe a tsugune jikinta sai kyarma yake tana kwashe gyaɗa dake zube a ƙasa. Kallansu Adda Yagana tai ta fara sauke idanta daga kan Raheena wacce ke cin gyaɗa marau marau, tace.
"Kallan uban me kike min? Da ido kamar na mayya." Sauke idanta kan Hasina tai wacce ta ɗauke idanta da saauri ta maidashi gefe. Kursum idanunta ta juya ta kalli Adda Yagana wacce itace babba cike da rawar murya tace "Adda Yagana ba Baba ya hana ku ƙiran ta ba? Karfa ku manta kanwar Baba ce ba bare bace bare ku ɗin ga sata a gaba kuna tsokana kuna dariya. Sannan ciwon nan Allah ne ya ɗaura mata wanda kuma baku wuce Allah ya ɗaura muku ba." Adda Yagana ta miƙe ta ƙaraso inda Kursum take duk da tsoron dake damunta baisa ta nuna ba, sai da ta zo inda take tasa yatsa ta dungure mata goshi tace.
"Gani kikai munsata a gaba muna dariya? Kwakwalwarta ce kamar ta yara dan ita ta shigo da kanta cikin ɗakin saboda tsoron kin tafi kin barta, shine ta takure gefe kamar tsaka mu kuma sai mu kasa dariya. Saboda haka in kinsan bakyaso ta zama haka ki fita da ita mana inda zakin?"
Wani abune ya tsayawa Kursum ta kalleta tare da maida abinda ya taso mata sannan ta matsa inda mahaifiyarta take ba tare da ta bata amsa ba, rungumota tai tare da mikar da ita tsaye tace.
"Umma kinji ciwo?" Kai ta girgiza tare da kikifta ido tana kama rigar Kursum tana cewa "Kursum ki rakani nai fitsari." Da sauri tace "Muje!" Tana sake riƙeta taga ashe tayi fitsayin a tsugunen da take. Adda Yagana ce ta taho da sauri tace.
"Badai fitsari tamin a ɗaki ba? Kut na rantse da Allah bazai yiwu ba." Raheena ta taso da sauri tana tafa hannu cikin nuna al'ajabi. Wani kallo Kursum ta musu tace.
"Zan wanke mata jiki n dawo na gyara muku gun aidai bada saninta bane tayi." Tai maganar tare da jan Umma suka bar ɗakin. Bandaki sukai tana tayata gyara jiki tana cewa "Umma ya akai kikai fitsari a jiki bayan yanzu bakyayi?" Kai ta girgiza tace.
"Kiyi hakuri Kursum wallahi bansan nayi ba, bazan ƙara ba kiyi hakuri, zasu dakeki ne saboda nayi?" Idanunwanta ne suka ciciko tace.
"Ba haka nake nufi ba Umma sannan dan Allah ki daina bani hakuri." Haka ta cigaba da gyara mata jiki hawaye sai sake zubo mata yake. Tare suka fito suka shiga suka kwanta Addu'oi suka fara yi tare tana yi Umma na maimaitawa har suka gama sannan suka shafa. Shigewa jikin Kursum tai kan kace me? Bacci yayi gaba da ita. A hankali Kursum tasa hannu ta zare ta daga jikinta sannan ta wuce ɗakin Adda Yagana dauke da roba da ruwa da kuma omo da tsuma, ta dade ta wanke gun suna kallanta har sai data gama. Raheena tai tsaki tace.
"Gida ba yara amma kullum cikin zarnin fitsari wannan abin kunya dame yai kama? Muda gidan uban mu an hanamu watayawa." Kursum ta kalleta tace.
"Sai dai in kune kuke fitsarin ku tunda dai raban da haka ya faru ta ɓangaren ta an daɗe. Sannan maganar gidan uba kuma Raheena sai ki sanar da Baba tunda shine yake kawo mu." A fusace Raheena ta mike tayo kanta tana hucci tana kumfar baki take cewa.
"Ni kike fadawa haka? Dan ubanki ni sa'arki ce? Ni zaki ɗinga yiwa magana haka? Wallahi har yau ban yadda ke da uwarki jinin Baba bane dan kuwa kaf garin nan ba wanda yasan da labarin haihuwarta, can dai ya tsintoku ya taimaka muku."
"Gwara mu dai kokonto ne dai jininsa ne, ku kuma fa?" Tana faɗa ta fara tafiya, jawo rigarta akai ta baya kafin tai aune taji an sakar mata wani mari, kuncinta ta rike da sauri ta kalli Adda Yagana wacce ke kumfar baki tace.
"Kina san cewa mu ba yaran shi bane dan abu ta kazar ubanki?"
Hannunta rike da kunci batai magana ba ta juya zata sake tafiya ta sakar mata wani wawan dundu wanda sai data durkusa. Miƙewa tai ta kalleta tai kwafa ta wuce, har takai ƙofar fita ta kallesu ta kalli ragowar ruwan dake hannunta cike da dakewa ta ɗaga ta watso ciki iya karfinta sannan ta ruga a guje tai ɗakin su tana shiga tasa makuli sai kawai ta saki dariya. Tace,
"Ko banza na rama, ke kuma Hasina zamu haɗu a makaranta zaki san ni kika wa haka."
Adda Yagana da Raheena wani ihu suka saka suna karkade kayan jikinsu da gudu suka fito sai kuma suka tadda ta kulle ƙofar. Kwafa sukai tanaji tana cewa.
"Zaki fito ai ko wallahi sai kin gane kurenki yar banza tsigi tsila kafa kamar an sumar da akuya." Daga cikin ɗakin tace.
"In ma kaza aka sumar ahaka nake san kaina in kinyi zuciya ki koma gidan mijinki." Ai kamar ta sake ingizo Adda Yagana nan ta dinga dura mata ashar Kursum komawa tai ta ɗauko assignment ɗinta ta zauna ta farayi, har ta gaji tai shiru..
***
A asibiti kuwa bacci ne ya kwashe Kabiru Nuhu Danbatta da Alhaji Nuhu Danbatta a wajan da suke, abinka da wanda suka gaji bacci sukai sosai. Can cikin bacci Alhaji Nuhu Danbatta yaji murya ana mai magana ƙasa kasa, idanunsa ya bude, sai dai abinda ya gani ne yasashi yin yar ƙaramar zabura, yaron ɗazu ne tsaye a gabanshi yana taɓa shi. Hamdalla yai tare da kallan yaron yace.