← Book details Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 27

Sashe 21

Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallan Nafi’u yake yana jiran yaji amsarsa, kai ya ɗaga ya ƙara riƙo shi yace “Insha Allahu bazan taɓa bari wani ya cuceta ba, zan kula da ita.” Hawaye ne ya kwacewa Alhaji Nuhu Danbatta kila raban auran nan ne yasa yaran nan yai hatsari har ya manta ko shi wanene dan ya cigaba da zama dasu. Share mai hawayen yai yace “Ka bari Baba yanda Kabir zai riketa nima haka zan riketa dan ina jinka kamar mahaifina.” Jinjina kai ya shiga yi cikin jin daɗin kalamansa yace “Nagode! Nagode Nafi’u Allah ya maka albarka.” Sai daya tabbatar hankalinsa yace kwanta sannan ya fito. Kabir ya kalla wanda ke tsaye hannayensa biyu a dunkule suke alamun tsananin dauriya da kunar rai, dan bai taɓa tunanin zaiji haushi in Kursum zatai aure ba sai dai haka kawai yakejin wani abu na taso mai. Kallan Nafi’u yai wanda shima kallanshi yakeyi cikin wata irin murya yace “Ko da wasa kasa kanwata kuka ina tabbatar maka wallahi sai na sa an raba auran.” Matsowa yai daf dashi mai makon ya mai magana sai ya ɗan daki kafadar sa da hannu yai ciki. Kabir wani irin yanayi yakeji sai dai ya sani laifin Inna ne duk ita taja mai wannan abin yana ji yana gani Kursum zata barshi. Juyawa yai ya fita daga gidan yana jin komai baya mai daɗi.

Kursum kuwa sai data gama tuwo tanayi tana share hawaye yanzu kam ta tabbatar Malam Badaru zata aura. Raheena ce ta shigo kitchen ɗin itama duk abinda ke faruwa bai mata daɗi tace “Kursum in kinyi aure ki tabbatar kin rokeshi ya barki kin yi exams duk wahalar da kika sha na karatun nan karya tashi a banza.” Murmushi ta sakar mata tace “In Allah yayi zai barni zanyi amma in ba haka ba babu komai ita rayuwa ai ba koda yaushe kake samun abinda kakeso ba.” Kallan tausayi ta mata tunda Kursum ta taso haka ta girma tana kula da mahaifiyarta dan in bazata manta ba tun da sukai wayau tasan ita ake sakawa gyara guri in Umma tsautsayi yasa rana ta kwace tayi abu a jikinta. Hasina ce ta shigo kitchen ɗin tace “Kije inji Baba.” Tai maganar tana kallan Kursum. Rufe miyar tai ta kashe wutar dan dama ta gama ta fito. A waje taga Umma na wasa wai rubutu take koya tunda Nafi’u ya koya mata rubuta 1 da 2 shikenan ta ishesu da rubuce-rubuce. A zaune ta ganshi yana jan carbi zama tai a kasa ta gaisheshi fuskarta a sake sosai dan bataso ya kawo wani abin a ransa. Cikin muryarsa yace “Allah ya miki albarka.” A hankali tace “Ameeen Baba!” Ya ɗan hadiyi miyan bakinsa yace “Ahmad ya fasa auranki wanda bansan dalilinsa nayin hakan ba. To nayi tunanin Kabir sai dai kinga yayanki ne shi, to ni bana sanki da Malam Badaru shi yasa na yiwa Nafi’u magana ɗan na tabbatar shi zai baki kulawar da Kabir zai baki.” Ɗago wa tai da sauri haka kawai ta samu zuciyarta da samun wata irin nutsuwa wanda ita kanta batasan ya akai ta tsinci kanta a hakan ba. Ajiyar zuciya ta sauke wanda sam batasan ta fito fili ba. Ganin haka yasa Baba yaji zuciyarshi ta sake kwanciya, ya sake tabbatarwa hakan shine daidai. Kanta na ƙasa tace “Duk yanda kai Baba ni duk ɗaya ne.” Cikin jin daɗi yace “Tashi keje Allah ya miki albarka.” Ta sake cewa

“Ameen." Sannan ta tashi

Tana fitowa ta sake sauke ajiyar zuciya tare da riƙe gefen zuciyarta. Haka kawai ta samu kanta da duba tsakar gidan ko zata ganshi sai dai babu shi. Ɗaki ta wuce ta zauna a bakin ɗan gadansu tana sake sauke ajiyar zuciya ta rasa meke damunta, ido ta lumshe kawai tana saukewa.

Inna dab da magriba ta dawo jin labarin nan a bakin Alhaji Nuhu yafi komai yi mata daɗi. Cike jin daɗi ta saki guɗa tace “Haba ko kaifa yanzu ne kai magan kaga sai su nemi ɗan gurin su a wajen gari su zauna babu takura babu takurarwa, a kalla kowa ya zauna lafiya.” Inna wannan labarin ba ƙaramin daɗi yai mata ba, cike da jin daɗi ta taimaka mai yaci abinci. Har Allah Allah take gobe ta yi a ɗaura auran nan, dan ita kam da kanta zataje ta nema musu gida, kayan ɗaki kuma tunda dukansu ba gata garesu ba ai ko tabarmarta ta ɗauka ta saka musu ai ya ishesu. Da wannan farin cikin tai bacci.

Kursum kuwa har tasa Umma bacci tana kallan ƙofa, Nafi’u bazai zo bane? Yau ko wuridin da take tsakanin Magriba da Isha’i kasawa tai saboda hankalinta dake kansa. Ganin da gaske bazaizo ba yasa ta mike ta fito waje dan tai fitsari ta kwanta. Tana buɗe ƙofa ta ganshi jingine da jikin bangon ɗakin, juyawa taje yi saboda wata irin kunyarsa data zo mata. A hankali taji yace “Ina zaki bayan nemanki nake?” Bata juyo ba sai dai ta tsaya inda take, cike da kunya tace “Meyasa baka kwankwasa ba?”

“Banasan na tashi Umma ne nasan tai bacci, kuma ni banasan na ƙiraki kar naje su Raheena suji.” Murmushi tai tace,

“To in ban fito bafa?”

“Hmm kila na tafi.” Shiru suka ɗan yi kafin yace “Aurena dake kin amince? Bana san takura miki, sai nakeji kamar ban cancanceki ba, har yanzu ko dangina….” Da sauri tace “Nima haka ai.” Tai maganar tana juyowa.

“Ka manta nima haka? banida kowa sai Umma, bamu san komai game da ita ba, Baba yace Kanwarsa ce amma ni nasan ba haka ba ne dan Inna tasha yi mana gori wanda in aka duba tanada gaskiya.” Cike da tausayi yake kallanta, ganin haka yasa ta sunkuyar dakai, murmushi yai yace.

“Sai nakejin abin kamar a mafarki.” Fuskarta ta ɗan rufe alamun kunya, murmushi yai yana binta da kallo. Haka suka ɗan yi hirarsu kafin ya shiga ɗaki. Kabir yana ganinshi ya juya mai baya cike da takaici yace “Wallahi ina sake sanar maka ko ka dawo hayyacinka ka wulakanta min kanwa zaka gamu dani.”

Yanzun ma bai kulashi ba sai kwanciya dayai. Sai da yaja bargo sai yace “Inkasan kana santa tun farko da ka nuna.” Zabura Kabir yai cike da takaici sai dai ganin Nafi’u ya rufe ido alamun bacci yasa ya kasa magana. Kwafa yai ya koma ya kwanta.

Washegari tun da safe Inna da kanta ta bada kuɗi aka tuka tuwo da yawa miyar taushe aka mika wa maƙota wanda suma da rana suka shigo da yake an dauka Nafi’un ɗan uwansu ne kowa sai ya dinga murna. Kabir yayi mamaki har lokacin baiga Ahmad ba, karin takaicinsa yanda Nafi’u ya ɗau ɗin kinsa dayai sabo kawai ya zura, haka sukaje masallaci aka zazzauna bayan sallar azahar dauke da goron da Mai unguwa ya siya da kuma dubu goma wanda Baba yasa Kabiru ya amso a makaranta ashirin akaso amma saboda babu kuɗi dole sai goman aka taho da ita. Kabiru har ya zauna a masallacin aka aiko wai Ahmad na nemansa a waje. Da sauri ya miƙe ya fita Nafi’u dake gefe yabishi da kallo.

Bayan anyi addu’a mai unguwa ya kalli Liman wanda yake wakilin Nafi’u kamar yanda suka tsara bayan anyi addu’oi da bayanai yace “Nafi’u ya dau nauyin auran?” Nafi’u dake gefen Liman ya matso yace “Liman sunan yankan nawa Yazeed Shehu Kankarofi." Ba tare da wani tunani ba suka gyara sunan nan aka ɗaura auran Kursum Shu’aib Danbatta da Yazeed Shehu Kankarofi akan sadaki dubu goma lakadan. Dan Kursum Alhaji Nuhu ne ya bata sunan mahaifinsa dan mutanen kar suyi magana.

Kabir ne ya kalli Ahmad wanda gaba ɗaya ya kasa magana kamar wanda yake tsoro. Wani kallo ya mai yace “Malam in bazakai magana ba ina da abinyi.” Zai juya kenan yaga ana fitowa daga massalaci muryar wani daga cikin mutanen yaji yace “Nikam Kankarofi wani gari ne?” Bai gama gane me suke faɗa ba sai dayaji muryar wani yace “Ango Yazeed nikam sunan ya min daɗi, amma da Yazeed menene na samaka Nafi’u?” Da sauri Kabir ya kalli mutanen gun ya hanzarta gurin dan san sanin meke faruwa. Yana ƙarasawa gun idanun Nafi’u na kanshi. Wani murmushi ya sakar mai wanda yasa Kabir tsayawa a gun turus yanasan sanin ma’anarsa kafin ya gama tantance abinda ke faruwa idanun Nafi’u na kansa yace “Wani mara lissafi ne ya sa min!” Dariya wanda yai tambayar yai yace “Yazeed Shehu Kankarofi nikam ina nasan sunan nan, kila sunan ne ya min daɗi.” Takawa baya Kabir yai idanunsa har lokacin na kan Nafi’u kwakwalwarsa ta kasa mai bayanin abinda ke faruwa.

(Dani dakai Kabiru duk jirgi ɗaya ya kwaso mu ni kaina gaba ɗaya kan ya kulle.)

Littafin nan na kuɗi ne, ki biya ɗari 700 ta 7065283730

Opay

khadija Abdullahi shehu

Katin waya MTN ta 07065283730

Sai shaidar biya ta. 07065283730 or +44 7894 142004

Ayusher Ce🏌🏻‍♀️

700 ne Kacal 🤌🏻
7065283730
Opay
khadija Abdullahi shehu.

Katin waya MTN ta 07065283730

Shaidar biya ta 07065283730 or +447894142004

Ayusher Ce🏌🏻‍♀️
RIBAR ƘAFA

NA

Wattpad :-AyusherMohd

Arewabook:- Ayushermuhd

ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️

Paid Book

Shafi na Goma Sha Uku

Gaba daya Kabir ya kasa nutsuwa ya saita tunaninsa akan abinda ke faruwa, yaushe Nafi'u ya zama Yazeed? Sannan wannan kallan da murmushin da yake yi mai na menene? Ji yai kwakwalwarsa na saƙa masa abubuwa dayawa wanda ya rasa amsoshinsu. Gun Nafi'u yai cikin sauri cike da zargi da tsoron abinda zai juyo. A hankali yace "Ina san magana da kai." Kallansa yai ya jinjina kai alamar to sannan yace "Amma ka biyoni gida ina bukatar sanar da Kursum an daura auran mu."
Chapter 21 · 0% Book details