Sashe 17
Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
700 ne Kacal 🤌🏻
7065283730
Opay
khadija Abdullahi shehu.
Katin waya MTN ta 07065283730
Shaidar biya ta 07065283730 or +447894142004
Ayusher Ce🏌🏻♀️
*RIBAR ƘAFA*
NA
*Wattpad :-AyusherMohd*
*Arewabook:- Ayushermuhd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀️*
Paid Book
Shafi na Goma
Kuka kawai suke a cikin ɗakin, dan Alhaji Nuhu Danbatta har lokacin baisan inda kanshi yake ba. Nafi’u ne ya biyo bayan Dr da gudu yana cewa "Dan tsaya!" Ja yai ya tsaya daga inda yake ya waigo yana kallanshi harya ƙaraso, wani yanayi ne a fuskarsa mai wuyar fassarawa sai dai kwarjini da rashin wargi ya bayyana akan fuskar. Cikin wata murya yace "A matsayin ka na Dr in bakasan aikinka ba ko kuma ba kada experience akan abu, shin ba hakkinka ba ne ka nemi wanda ya sani ya taimaka maka?" Da mamaki Dr ya kalli Nafi'u yace "Me kake nufi? Kai likita ne?" Ran Nafi'u a matukar ɓace yace "Bansani ba, amma haka kawai jikina na bani baka gama sanin aikinka ba, bansan a ina naji ba amma am sure akwai solution akan problem ɗin nan dan haka immediately ka ƙira manyanka ka tambayesu, ko ka tura mu wani asibitin." Dr ne yake kallanshi sai dai haka kawai yakejin shakkar mu sa mai dan kuwa yasan ciwon mantuwa ke damun mutumin da suka kawo, amma da alama yaron nan yasan wani abin a baya kar ya zake da magana azo a samu matsala. Ajiyar zuciya yai yace "Ai nima bawai nace mutuwa zaiyi immediately ba, mun yi iya yin mu ne muke so mu jira abinda Allah zaiyi inhar ya wuce yau bai mutu ba alamu ne na samun nasara." Wani murmushi ne yazowa Nafi'u wanda shi kansa baisan yayi ba kafin yace "A hannunka rai yake?" Da sauri Kabir ya dafashi ta baya alamun yai shiru sannan ya kalli Likitan yace "Sorry hankalinsa ne ya tashi." Kallan Nafi'u Likitan ya sakeyi wani abu yake gani a idanunsa wanda bazaice gasu ba, sai dai haka kawai yasha jinin jikinsa. Hannunsa yasa a cikin aljihunsa kafin yace "Zan ƙira consultant din mu na sanar dashi case ɗin." Juyawa kawai Nafi'u yai ba tare da ya tanka masa ba. Ɗakin kuwa shiru yai banda kuka da jan majina ba abinda ke tashi. Alhaji Nuhu Danbatta kuwa yana kwance idanuwansa a rufe har lokacin. Inna ce ta kalli Kabir dake tsaye a gefe ta mai alama da yayi abinda ta sakashi? Gaba ɗaya mamakin Inna ya hanashi magana, taya zata birkece lokaci ɗaya? Shi dai ya tabbatar ba halinta bane wannan tabbas tsorata tai da abinda ke faruwa da Baba shi yasa take haka. Bai ce komai ba, sai yi yai kamar bai gane abinda ta ke nufi ba. Sai wajen ƙarfe ɗaya na dare Alhaji Nuhu Danbatta yaja wani dogon numfashi tare da buɗe idanunsa a hankali. Idanuwansa ne suka sauka akan mutanen dake kewaye dashi, Inna, Raheena, Hasina da Kursum. Kabir na daga gefe idanuwansa har yanzu basu dawo daidai ba. Shi kuma Nafi'u na can wajen ƙofa. Ita kuwa Yagana tana kwance a gefe tana zabga uban bacci. Cike da kulawa Raheena tace "Baba!" Kuka ne ya kwace mata. Ido ya lumshe ya sake buɗe wa bayan ya saukesu akan Khursum. Ya zai yi da tausayin yarinyar nan? Maida idon yai ya rufe nan wani baccin ya sake ɗauke shi. Cikin kuka Hasina tace "Inna karfa ya wuce gun baccin nan!" Gaba ɗaya Inna ta firgice afuska garau take amma yanda ta kasa zaune ta kasa tsaye kaɗai zaka kalla kasan akwai abinda ke damunta. Dr ne ya shigo wajen ƙarfe biyu ɗauke da wasu takardu, daga gefen dakin yana shiga suka hada ido da Nafi'u ya kauda kai tare da maidashi kan Kabir yace "In ba laifi ka matso akwai abinda zanma bayani." Bai musa ba ya taho, Nafi'u dake gefe ya kauda kai kamar bazai kula ba sai jiyai Kabir yace "Nafi'u matso mana." Ya sani ba wani jituwa bane tsakaninsu amma bazai musa ba saboda san da yakewa mahaifinsa ba da yanda ya damu da halin da yake ciki. Nan Dr ya shiga yi musu bayanin abinda consultant din yace sannan magunguna da karin ruwan daya bada amai, sai daya gama sannan yace "Baza'a mai aiki ba dan in har aka taba inda lungs da zuciyarshi take to fa zai iya mutuwa. Sannan kamar yanda na fada muku wannan aikin bazai fara ba har sai munga ya kwana da ransa, kuyi hakuri in kalmar ta muku zafi amma a matsayina na likita dole ne na sanar daku, ko ya warke yanzu sai dai ya din ga amfani da oxygen a gida wanda a kullum sai ya shaki na awa hudu zuwa shida, wannan ne kaɗai zai taimakawa lungs dinsa su dinga kai iskar numfashi zuwa zuciyarsa, rayuwar da yai da bazai sake iya yinta ba dan tafiya mai nisa ma bazai iya yi da kansa ba duk inda ya taka da kansa to fa karya wuce taku goma." Gaba ɗaya jikin mutanen ɗakin yai mugun sanyi. Kabir da Nafi'u yakewa bayani amma da yake suna ɗakin duk sunji me ake cewa, banda kukan su da ya karu ba abinda ke tashi. Alwala Kursum tai kawai ta fara sallah, ganin haka yasa Raheena da Hasina ma suka hau sahu. Addu'a suke sosai. Kursum rayuwarta kawai data Ummanta take hangowa. A duniyar nan babu Baba tasan shikenan ita da farin ciki sai kuma a lahira. Har sallar asuba tana kan sallaya tana sallah da adduo'i su Raheena bacci ne ya ɗauke su, su kuma su Nafi'u sun fita daga ɗakin. Mikewa tai dan ta duba yanayin Baba, Inna dake zaune kusa dashi ce ta kalleta tace "Nasa a saida gonarki banaji kinada ikon ajiye ta bayan wanda yasha wahalarki na kwance." Ta ƙarasa maganar tana mata wani irin kallo. Murmushin yake Kursum tai tace "Inna duk abinda na mallaka a duniyar nan nashi ne." Tsaki Inna tai ranta a ɓace tace "Babu ma abinda kika mallaka banda ita gonar sai kuma gangar jikinki, inhar aka sallamemu ki fito da miji a miki aure dan bazai yiwu ina fama da mara lafiya ina kuma fama dake da uwarki ba, dan kuwa babu ko kaffara mijina ba Yayan ta bane ba, ya dage ne kawai na barshi amma har Goggo tabar duniya bata taɓa bani labarin ta haifi wata mara lafiya ba. Sannan duk su ukun na sansu kafin su rasu, wacce ke da rai ma na santa dan dai Allah baiyi zata zauna anan arewa bane." Bata jira amsar ta ba ta cigaba da cewa. "Babu dalilin da zaisa mu ciagba da kula da ku bayan ba wani taimakawa kuke ba, wanda mukai da ma ya isa Allah ya bada lada. Dan haka ki tabbatar kin wa wanda yake sanki magana ya fito idan yaso kayan ɗakin Yagana sai mu kai miki ai ko banza kin samu na fita kunya." Kai kawai ta ɗaga alamar to dan kuka ne yake neman kwace mata. Da sauri ta shiga toilet din dake gefen ɗakin da yake ba a ciki yake ba, ta kule kawai ta fashe da wani irin kuka. Ta sani hakan zata faru, amma batasan tun yanzu zata fara ganin canji haka ba. Alhaji Nuhu dake kwance hawaye ne ya gangaro ta gefen idansa dan ko motsi bayayi.
Kabir haka yaje aka bada jinginar gonar Kursum wanda taci a musabaqa a ka biya kudin asibiti. Alhaji Nuhu Danbatta mutum ne da ake ganin mutuncinsa, haka mutane suka tara kudi aka hada musu, sun biya kudin asibiti da kudin oxygen din da zai dinga amfani dashi duk an siyo daga Kano. Cikin ikon Allah haka yai kwana biyar a asibiti mutumin da aka zata mutuwa zaiyi sai gashi ya kai kwanakin nan yana numfashi. Sai dai babu ci, ruwa ma da kyar yake hadiya. Duba da yanayin kudin da ake ci na zaman asibitin yasa Inna ta dage sai an sallamesu. Nafi'u sam baya kulata dan haka ko data dage sai an sallamesu bai tanka ba. Shi kuwa likita ya basu takardar sallama suka bar asibitin a ranar da ya cika sati ɗaya. An haɗa musu magunguna da cilinder na oxygen da nasal cannula ɗin. Haka suka kwaso Alhaji Nuhu rai a hannun Allah magana inta wuce guda biyu uku baya iyawa. Kursum kam tunda Inna ta korota daga asibiti ta dawo ba'a sake barinta ta koma ba, ita take zama a gida tana abinci ana zuwa a ɗauka. Ummanta kam wasanta kawai takeyi dan wani sa'in in taga ƙofa a buɗe ma fitarta take har sai Kursum ta fita ta nemota. Wannan abu na damunta dan ranar can ta ganta bayan gari tana wasa da yara, gaba ɗaya kwanan nan sai take ganin kamar ciwon Umma ma karuwa yakeyi, duk ta rame ta canza, nutsuwarta daya in Nafi'u ya dawo da daddare dan da kanshi zai sata a gaba ya taimaka mata tai karatu, ya zauna da Umma har sai bacci ya zo mata ita kuma tana aikin gida sannan ya koma asibiti. Zata iya cewa wannan sati ɗayan yana daga cikin kwanakin data shiga matsi a rayuwarta.