← Book details Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 27

Sashe 26

Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kabir kuwa ya fita siyo wa Baba paracetamol dan kansa ke ciwo ya dawo ya tadda su Inna a tsakar gida, kana kallanta kasan cikin farin ciki take dan yana shigowa tace. "Kabir Allah baiyi zakuyi sallama ba yanzu Kursum aka ɗau keta anga dangin Nafi'u, kaga Allah ya taimake mu anyi auren nan da yanzu ina nan zai tafi shi kaɗai ya barni dasu. Yanzu kam sai dai fatan Allah yasa inya tafi da su ɗin karsu dawo dan bana fatan sake zama dasu." Maganin dake hanunsa ne suka sulale ƙasa dan gaba ɗaya bai yi tunanin jin wannan kalaman a gun Inna bad. Cikin rawar murya yace "Wanene ya ɗauke shi? sannan Inna dan bakya san yarinya kawai daga aure bakisan halayensa ba sai ki ɗau yarinya ki bashi? In ɗan fashi ne fa? Ai sai ku jira nazo na bishi muje tare naga gurin da zai ajiye su." Cikin fushi tace,

"Yoo in fashin ma yakeyi ya dameni ne? Kaga bansan iskanci dan Allah to ubanka ne yace su wuce dasu." Da sauri ya kalli ƙofar ɗakin Baba sannan ya juya waje da gudu. Baki ta taɓe tace "Wannan kuma matsalarka ce dan kuwa ko a mota ka fita bazaka cimmasu ba."

Kabir kam gudu kawai yake kamar zai tashi sama har ya isa bayan gari yana haki, sai dai sam babu alamun Kursum ko Yazeed. Jiyai numfashinsa na seizing saboda gudin dayai, can kuma sai gumi ta ko ina. Tsayawa yai ya riƙe cikinsa yana maida numfashi. Bakin cikinsa kawai shine ko numbersa Kursum bata sani ba yanzu in abu ya tashi tana san ta gudu wa zata nema? Ido ya runtse dan kuwa yasan Yazeed Shehu Kankarofi ba mutumin kirki bane, sai dai in har an sanshi a gari ai bazai yi wahalar sanin gidan shi ba kenan ko? Da wannan tunanin ya juya yana tafe kamar mara laka a jiki.

Tun suna tafiya tana kallan gari har bacci ya ɗauke Kursum dan kwanan nan bata samun baccin sosai saboda abubuwan dake faruwa. A hankali ya juyo ya ɗan zuba kata ido tare da sakin murmushi shi ya sani Kursum tashi ce bai taɓa tabbatar da hakan ba sai randa ya ganta. DPO ne ya katseshi da cewa "Yazeed kana ganin Magajiya zata aminta da maganar auranka?" Idansa har lokacin na kan Kursum yace "Sai ta zaɓa zamana a gida ko barin gidan." Ɗan waigowa DPO yai, ya san halin Yazeed tunda ya faɗi haka zai aikata. Maida kallanshi titi yai yace "Kana ganin yaran da sukai kidnapping ɗina kuɗi kawai sukeso?" Kai ya jinjina alamun eh kafin ya cigaba da cewa "Da halakaka suka so suyi da ko wuka ne sun caka maka kafin su bar ka." Saman goshinsa ya shafa bai amsa ba. Umma sai kara take a bayan mota tana irga motocin dake wucewa sai ta saki tafin jin daɗi. Haka tai tayi har suka shiga cikin garin Kano, basu tsaya a ko ina ba sai a ƙofar wani tangamemen gida anan cikin nasarawa Nassarawa GRA, gidan ko daga waje kazo wucewa sai ka tsaya ka kalleshi bare ka shiga ciki. Security ne a bakin ƙofar yana ganin motar DPO ya taso sai da ya leka ciki dan tabbatar da tsaro ya hangoshi. Ganin Yazeed a gefe ya juya da sauri ya buɗe ƙofar suka shiga sukai parking daga gefen manya-manyan motocin dake harabar gidan. Har zai kule gate sai ga motar su Ummy ta shigo, da sauri ya sake buɗe wa tare da tsayawa sai da suka shiga sannan ya rufe.

Yazeed Shehu Kankarofi ne ya ƙara so inda motarsu Ummy suke ya buɗe mata bayan kofar, idanunta ne suka ciciko da kwalla tace "Yazeed!" Murmushi ya yi mata ya ɗan ɗaura hannu ɗaya saman jikin motar yana cewa "Ummy na, I am really sorry zan sanar dake abinda ke faruwa." Hannu tasa ta share hawayenta tace "Bako mai ni farko na ɗauka tafiya kai, ganin baka kira ba ne duk kwanakin nan yasa tsoro ya kamani, ga wayarka ko an ƙira a kashe take." Kai ya jinjina mata yace "Muje ciki bayan nayi sallah zan zo na sanar dake." Cike da gamsuwa ta jinjina kai tace "Alhamdulillahi da Allah ya dawo mana dakai lafiya dan shi kaɗai muke bukata." Kai ya ɗaga dan yasan da gaske ta shiga wani hali gashi har rama tayi. Kallan Salim yai wanda ya miƙa mai hannu alamun su gaisa, kamar zai mika mai shima sai kuma ya fasa ya juya cikin motar DPO ya buɗe ƙofa. Umma ce ta fito tana zare ido sai kuma tahau tsalle tana cewa "Shikenan mun shigo Aljanna." Ummy ya kalla wacce ta saki baki tana kallan matar da a shekaru a kalla ta kusa arba'in amma tana ta tsalle kamar yar shekara biyar, kana kallanta zakasan batada lafiya. Daga inda yake yace "Ummy wannan Umma ce mahaifiyar matata." Idanu ta zaro cikin tsananin mamaki mara misaltuwa ji tai gabanta ya bada wani irin rass. Salim ma idanuwansa ne suka firfito yace "Matarka kuma?" Kai ya ɗaga alamun eh sannan ya cusa kanshi cikin motar. Hannu yasa ya ɗauko Kursum dake sharar bacci Kamar wata matacciya. Ummy kam jiri ne taji ya kamata, kanta ta rike tare da yin baya zata faɗi, da sauri Salim ya riketa. Yazeed ya kalli Umma yace "Taho mu shiga ciki!" Ba musu ta bishi tana tsale tana cewa "Ashe har mun mutu? Yeeee aljana daɗi wallahi." Bai tanka mata ba sai wucewa bangarenshi da yai. Masu aikin gidan kuwa tunda ya shigo riƙe da yarinya kowa ya saki baki, baibi takansu ba har ya isa part ɗinshi. Yasmeen na ciki ta sa turaren wuta tana ƙoƙarin fitowa gashi, tsalle tai tana neman rungumeshi idanunta suka sauka kan yarinyar dake jikinsa. Yanayinta ne ya canza sosai tace "Yaya who?"

Bai tanka taba sai zagayeta da yai ya shiga ciki. Kwantar da ita yaje yi kan kujera a hankali idanuwanta suka buɗe, da sauri ta zame daga jikinshi hakan yasa ta faɗa kan kujera gaba ɗaya. Gabaki ɗaya a tsorace take kallanshi. Hannu ya kai saitin fuskarta tai saurin matsawa hakan yasa ya ɗan maida hannun yace “Sum-sum kin tashi?” Gefenshi ta kalla a hankali ta fara bin falan da kallo. Wani tangamemen falo ne wanda a kalla zai kai kusan gidan Alhaji Nuhu girma, an malaleshi da kujeru na alfarma, daga can gefe kuma dining area ne, simple akai kwalliyar sai dai kallo ɗaya zaka mai kasan an kashe kuɗi. Idanuwanta ne suka firfito bakinta har rawa yake tace “Ya Nafi’u ina ka kawo ni?” Waigowa yai inda Yasmeen ke tsaye ta tsaya kamar wata gunki ya mata alama da ta fita sannan yace “Ki wuce da Umma part ɗin Ummi tai wanka ina zuwa.” Kamar zata musa mai sai dai ganin kallan da ya mata yasa ta juya tare da kallan matar da ya kira da Umma tana tafe tana mamakin iskanci irin na Ya Yazeed har ya kai haka? Shi kuwa kallan Kursum yai yace “Kin tashi? Muje ki samu kiyi wanka naga a girme bakifi Yasmeen ba sai na amso miki kayanta ki saka.” Yada take bin cikin idanuwanshi da kallo ne yasa yace mata “Menene?” Gefe tai da sauri tace “Kana san ce min nan gidanku ne? Ina kakar taka da aka ce batada lafiya? Sannan a iya sanina ance bakada kowa sai ita wannan budurwar wacece? Sannan mutanen dake jikin can su wanene?” Tai maganar cike da tsoro tana kallan family picture ɗin da ke manne a falan.
Chapter 26 · 0% Book details