Sashe 22
Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Wani abu ne ya tsayawa Kabir a makogaro wanda da kyar ya iya haɗiye shi kafin yace "Nafi'u bazan iya jira ba." Kai ya ɗan karkatar yana kallan gefe alamun hankalinsa baya kan Kabir ɗin kafin yace "Then?" Cike da mamakin yanda yake mai magana ba irin yadda yasan shi da ita ba yace "Kanaso nai magana anan ne?" Waigowa yai tare da ɗaga kafaɗa alamun bai dameshi ba yace "Duk abinda yai maka." Yana kaiwa nan ya ɗan kai hannu kafadarsa ya ɗan buga, nan da nan Kabir ya ƙara tunowa haka ya mai jiya. Janye kafadarsa yai zuciyarshi tana wani irin tafasa, zai yi magana yaga yayi gaba ya barshi anan. Da sauri ya juya shima dan tabbas sai yaji amsoshin tambayoyinsa kafin su isa gida. Ahmad ya kalla wanda shima idanunsa ke kan Nafi'u kana kallanshi zakasan shima cike yake da ɓacin rai. Gun Ahmad ya koma ya sa hannu ya fizgoshi suka koma can gefe yace "Uban wa yace ka fasa auranta? Sannan in zaka fasa dan me baka fara zuwa ka sanar dani ba?" Ahmad idanunsa ne suka kaɗa sosai ya tamke hannu tare da naushin ɗaya cikin ɗaya yace "Wallahi yau babu mai rabani da Nafi'un can, Allah ko zan rasa raina sai na karya shi." Tsaki Kabiru yai yace "Dalla yi min shiru ni yanzu kurin bakinka ya dameni ne? Me yasa ka fasa auranta? Shine tambayar da nake maka." Zama yai a gefen bishiyar da yake kusa da ita dabas yana jin wani zugi a ransa, sai dai ya sani ya riga da ya kwafsa. Hannun rigarsa ya saka ya share zufan dake zubo mai kamar wanda aka datsewa baki sam yaki magana. Ganin da gaske bazai yi magana ba yasa Kabir ya juya dan kuwa Nafi'u ne kawai zai bashi amsar tambayoyinsa. Yana komawa masallaci yaga duk an watse abinka da auran da ba wai saninsu sosai akai ba, gwara ma Kursum amma Nafi'u ko ince Yazeed Shehu Kankarofi wanene ya san shi? Kabir ganin baya gun yasa cikin bacin rai yai hanyar gida, yanzu ne kwakwalwarshi da tunaninshi ya dawo duk zaman da sukai ko me? Taya tun da can bai san sunan shi ba sai lokacin da za'a ɗaura mai aure? Kanshi gaba ɗaya sara mai yake saboda tunanin dake yawo a ciki. Ya akai Ahmad ya fasa auran Kursum ɗin? Ya akai Inna tasan Ahmad ya fasa auren Kursum? Ya akai Inna tasan yana shirin auranta? Jiri ne ya fara ɗibarshi dan abinda ke yawo a kanshi yayi yawa, dole yaje ya sanar da Kursum dan babu yanda za'ai yabar ƙanwar sa ta faɗa hannun wanda ba wanda yasan wanene shi. Ji yai an taɓa shi ta baya wanda taɓa shin da akai shine ya ɗan tareshi daga jirin da ya kama shi. Waigowa yai idanunsa suka sauka kan Nafi'u wanda ke tsaye. A hankali ya sakar mai murmushi yace "Looking for me?" "Eh looking for you kuma yanzu zansa ƴan gari su yi ma dukan da ko numfashi bazaka iya yi ba." Kai ya jinjina alamun 'to' kafin yace "Duk ba wannan ba, I need to call someone, zaman garin nan ya ishe ni." Mamakin yanda yai magana hankali akwance yasa Kabir sakin baki dan ko kwakwaran motsi ya kasa yi. Ganin haka yasa Yazeed Shehu Kankarofi ya kai hannu aljihun rigar Kabir ta gaba ya ɗauki wayar Kabirun, numbobi yai dialing cikin sauri aka ɗauka. Daga inda Kabir yake yana juyo muryar mai maganar wanda ya dinga jin kamar yasan muryar, yana ji daga cikin wayar bayan yayi gyaran murya akace "Yallabai." Bai amsa ba sai cewa yai "Ka samu wanda ya turo ai kidnapping dina?" Da sauri yace "No sir, kai hakuri muna nan muna bincike." Kai ya jinjina yace "Ka sanar da Ummi inda nake yanzu, na gaji ina san komawa gida a yau." Yana kaiwa nan ya kashe wayar ba tare da mai maganar ya cigaba da yi ba. Mikawa Kabir wayar yai wanda gaba daya ya sandare ko motsi ya kasa. Kallan inda yai dialing ɗin yai mamakinsa bai karu ba sai da yaga sunan DPO a jiki "Inalilahi wa ina ilaihi raji'un, meke faruwa?" Bakinshi na rawa yace "Kana san ce min dama can ba abinda ke damunka? Taya zakawa Babana haka? Mutumin da ko a cikin ciwon nan tunanin ka yake yi? Me muka yi maka?" Mika Yazeed yai tare da sa ɗaya hannu a aljihu yana kallan Kabir wanda kana ganinsa zakasan yana cikin shock dan wayarsa har yanzu ya kasa amsarta. Wayar ya maida mai cikin aljihu yana neman tafiya, cikin tsawa Kabir yace "Why? Me Babana ya maka? Kana nufin iyayen ma da aka ce naka sun rasu duk karya ne kenan? Domin idan ban manta ba da kunena Ummi naji ka ce wato mahaifiyarka." Taku biyu yai ya dawo inda Kabir yake kafin ya sakar mai murmushi yace "Option biyu zan baka ka zabi ɗaya, one ka ruga gida da gudu ka sanar da abinda ka sani da abinda kake tunani wanda in Baba ya ji ya ja mai wani abin, dan a yanda kake behaving banaji kasan how serious ciwonshi yake. Option two kuma." Ya mai alamar zip da hannunsa yace "Hankali a kwance zan bar kauyen nan, na kuma biyawa Baba babban asibiti a kula dashi." Ya ɗan sauke ajiyar zuciya tare da kallansa sai kuma ya fara tafiya. Kabir kasa magana yai karan farko daya tsinci hawaye na bin kumatunshi, jiyai yana ganin dishi-dishi, wato yaran nan gaba ɗaya raina musu hankali yai kenan duk zaman dayai a kauyen nan? But menene dalilinsa? Bari yaje ya sanar wa mai unguwa a raba auran nan basu yadda da shi ba..... Cak yaji tunaninshi ya ɗauke, wato abinda yasa ya bada sunanshi na asali aka ɗaura auran dan karma nan gaba azo mishi da wata maganar ko? Tunda yake bai taɓa shiga mugun shock ɗin daya tsinci kanshi yau ba, ko ciwon Baba bai kai shock ɗin daya shiga yau ba.