← Book details Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 27

Sashe 12

Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Kwakwalwarshi ce ta sake dawowa hayyacinta sai dai wannan karan gudu kawai ake a cikin motar, gudu ake kamar za'a bar garin. Horn aka fara yi da ƙarfi ta bayan su, nan danan mutanen dake cikin motar hankalinsu ya tashi, tsoro da furgice duk ya kamasu, suka ƙara sa gudun motar yanaji guy ɗin ɗazu wanda ya gane muryarshi yana cewa "Munshiga uku ba dai har an san munyi kidnapping ɗinshi ba?" Ɗayan da gaba ɗaya tsoro ya rutsashi yace "Wallahi ina da mahaifiya marar lafiya, shiyasa ni bansan gangancin da yasa ka ɗau aikin nan ba kadai san dama bazamu tsira ba," ya cigaba da magana cikin rawar murya "Ka gangara gefen titi mu ajiye motar mu nufi daji kawai gwara mu tsira da ran mu sannan ya dai bamu rabin kudin?" Ɗayan yace "Eh, ya turo." Nan suka sa gudu. Sai da suka ɗan yiwa masu bin nasu nisa sannan suka gangara gefen titi, motar kawai suka ajiye suka auna a guje kai kace zaki ne ya biyosu, dan suna gudu harda faduwa suna gudu suna faɗa dan ɗayan yaso su sace motar.

Saurayin nan kuwa dakyar ya mike ya iya motsa hanayensa, nan ya fara tattaro duk wani ƙarfi da yasan yana dashi, motar sa ce dan kuwa ya ganeta. Kai ya shiga girgizawa wanda ke mai nauyi kamar an ɗaura masa dutse, yana dafa jikin kujera a haka dakyar ya zauna a gun driver, kansa ke sake sarawa gashi ko gani sosai bayayi sai dai da ya bari mutanen nan su sace shi gwara yaja motarshi yabar wajan. Kunna motar yai ya jata zuwa kan titi, ko gama hawa kan titin bai yi ba yaji ana juyashi, tun yana san sanin meke faruwa har yaji ya hakura sakamakon ɗauke komai da akai daga cikin kwakwalwarshi.

Jikin bishiyar dake gefen titi ɗayar motar da sukai gware ta bugu nan fa itacen dake bayan motar kur-kurar suka hau zubowa ƙasa. Dattijon dake zaune cikin mota ne ya rike wuyansa da ya bugu yana ƙoƙarin fitowa bakinshi banda "Inalilahi wanina ilaihi raji'un," babu abinda yake fita.

Ba Ƙaramin tashin hankali ya fuskanta ba ganin yanda motar data kuno kai ta gangara, kafafunsa ne suka shiga karkarwa a haka ya ɗin ga jan ƙafar shi har sai da yazo inda motar ta ke. Ihu ya saka da karfi ganin saurayi a kwance cikin jini, ya dinga salati yana ƙoƙarin buɗe ƙofar. Wayarsa ya ɗauko ƙirar nokia jikinsa na rawa ya ƙira waya sai dai harta katse ba'a ɗauka ba. Tsaki ne ya fito daga bakinsa dan dama yasan indai shashashan yaran can ne ba ɗauka zai yi ba. Yana tsaka da ƙoƙarin buɗe ƙofa sai ga wata mota ta taho, ganin halin da suke ciki yasa tai parking nan suka taimaka aka buɗe ƙofar aka ciro yaran wanda gefen kansa keta zubar da jini. Hankali a tashe suka nufi asibiti dan kuwa tsoro bazai bar mutumin nan ya iya jan motar nan tasa ba. Saboda gabaki ɗaya a ruɗe yake.

Har suka shiga asibitin yana sake gwada wayarsa ko Allah zaisa wannan mashiriricin yaron ya ɗau wayar. Suna shiga mutanen asibitin suka fara gaidashi sai dai ganin halin da yake ciki yasa hankalin nurses ɗin ya tashi. Hankali a tashe suke tambayar shi inda yake mai ciwo, ya kalli nurse ɗin hankalinsa a tashe yace "Accidents mukai ga mara lafiyan nan." Da sauri suka kalli baya dan sai a lokacin sukaga samarin dake rike da saurayin da aka shigo dashi jini na ɗiga daga gefen kansa da hannunsa. A guje suka turo gadon aka ɗora shi tare da yin ciki dashi. Dattijon ya kalli samarin da suka temaka masa yai musu godiya sannan suka tafi suka barshi domin Dattijon garinsu yana kusa kuma duk mutane sun sanshi dattijon kirki ne sosai. Addu'a kawai dattijon nan keyi dan gaba ɗaya jikinshi rawa yake, fatanshi kawai Allah ya tashi kafaɗun yaran nan. Wayarsa ya sake ɗauka a karo na ba adadi ya ƙara ƙiran wayar yaran da yaketa nema tun ɗazu. Kamar daga sama yaji an ɗauka sai jiyai ance "Baba ina kwana bacci nake yi."
Chapter 12 · 0% Book details