← Book details Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 27

Sashe 19

Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da rana tsaka Inna ta dawo ta zauna tana sanar da Alhaji Nuhu Danbatta maganar auran Kursum da Ahmad wanda za'ai. Kai ya shiga girgiza mata cikin rawar murya yace "Sameera dan Allah!" Mikewa tai dan bama tasan jin me zai fada ta fito waje tana kwallawa Yagana ƙira. Bata fi minti biyu ba sai ga ta ta fito tana turo baki. Wani kallo Inna ta mata tace "Kayan ɗakin ki da aka kwaso na duba banga katifa ba tana ina?" Cike da kunkuni tace "Na ɗauka na maida gidan, yarana sunce katifar da suke kwana ta tsufa. Sannan ni fa Inna kayana baza a bawa Kursum ba dan gaskiya komawa ɗakina zanyi." Tsaki Inna taja tace "Komawa zakiyi ina? Baki da hankali ne ko baki san me saki uku yake nufi ba a aure?" Kai ta kauda cike da gatsine tace "Nifa ba saki uku ya min ba, biyu ne kune kuka maidashi uku dan haka ni gidana zan koma taje can ta samu kayan ɗakinta." Mamaki ne ya bayyana a fuskar Inna tace "Ni zaki kalla kice saki biyu ne? To zan iya tuna miki in ma kin manta sanda akai sakin, karki mai damu mahaukata mana." Fara tafiya tai tana cewa "Koma dai menene aurena komawa zan kuma Allah ba wanda ya isa ya hanani. Haka kawai kuce uku bayan biyu ne." Tana magana tana ɗan tafiya, jin an daka mata tsawa da sauri ta waigo, ganin Kabir yasa ta tamke fuska tace "Ni ba Yayarka bace kake min magana haka?" Ransa a mugun ɓace yace "Inna sa'arki ce da zaki dinga mata magana haka?" Cike da faɗa tace "In ba sa'a ta bace a matsayinta na uwa sai tai abinda ya dace. Kuma Mansur ne na faɗa ba abinda zai rabani dashi kayana ne kuma hakkinane bazan bawa wata ba in tai zuciya ubanta ya mata." Tana kaiwa nan ta wuce ciki tana kallan Kursum daga gefe can alamun taji me akai amma ko a jikinta tai gaba. Inna ta bita da kallo kafin ta kalli Kabir tace "Ai Kursum ba dole ne sai an kaita da gado ba ko katifa muka siya aka lailayeshi ai zata zauna. Ita kuwa Uwarta kaga ko a ina ne kwanciya zatai, tayi sa'a ma gidan nasu gidan yawa ne kaga baza'a rasa inda za'a dan sakaya ta ba in dare yayi." Gaba ɗaya mamakin kalaman Inna yakeyi har ta gama tabar gun bai iya tanka mata ba. Sai a lokacin ya sake tabbatarwa dole ne ya auri Kursum dan idan Inna ya gama rufewa. Ɗaki ya wuce jikinshi duk ansanyaye, Nafi'u na zaune shinkafar rana ce a gabansa dan tunda Kursum ta fahimci ba komai yake ci ba intai girki da rana sai ta ɗiba ta ajiye mai. Kabir ransa a ɓace ya shigo wani kallo yawa Nafi'u kamar wanda ke jiran wani abu yace "Kursum baiwarka ce da kullum sai kasa ta ɗumama kunu ta dumama maka abincin rana?" Ko kallan inda yake Nafi'u baiyi ba sai ma rufe kwanan abincin dayai ya wanke hannu ya kwanta. Sunyi shiru a dakin kamar masu bacci, wanda a zahiri dukansu idansu biyu. Cikin wata murya Kabir yace "Nafi'u kana ganin auran da babu soyayya a ciki yana iya lasting?" Hannunsa na saman goshinsa yace "40%" Ajiyar zuciya yai yace "Kuma kana ganin yarinyar zata so shi?" Shiru ya ɗan yi kafin yace "50%" Dan karamin tsaki Kabir yai yace "Yaran fa?" Yanzu kam hannunsa ya sauke yana kallanshi yace "10%" Cike da takaici Kabir ya mike zaune yace "Kaifa ba'a shawara dakai banda iskanci wani irin bada amsa ne wannan?" Bai tanka mai ba sai juya mai baya dayai ya kulle idonsa. Kai Kabir ya girgiza ya kwanta, kalaman Baba ne kawai suke sake dawomai, tabbas bazai bar Kursum ta auri Ahmad ba, dan ko shi da yake abokinsa suna abokantaka ne dan fafar da suke tazo daya amma sam bashi da hali na gari. To amma shi ta ina zai fara zama da Kursum a matsayin mata? Inna fa? Ya zaiyi da fishinta? Da wannan tunanin ya dinga juyi har bacci yai gaba dashi. Nafi'u kuwa kasa bacci yai ya rasa meke damunsa. Fita daga dakin yake san yi amma haushin Kursum na rashin sanin ciwon kanta yasa baisan fitar. Haka dukansu sukai ta sakawa da warwarewa har bacci yai gaba dasu.

Gaba ɗaya yau ta tashi ba kuzari a jikinta, ruwan zafi ta dafa ta kawowa Ya Kabir yai wa Alhaji Nuhu wanka ya gyara shi. A gun wankan ne yake sanar mai zaije ya samu mai gari ya sanar dashi abinda ke faruwa dan shine kadai mafita, dan kuwa in har Inna taji to fa wannan abu bazai taɓa yiwuwa ba su sun sani. Alhaji Nuhu Danbatta har kwalla yai yana rike hannun Kabir ya sani tuncan Kabir yaran kirki ne shi dai a barshi da rawar kai, amma kaf cikin yaransa ba wanda ya kaishi tausayi da sanin darajar mutum. Kursum tana shanyar kayan data wanke ta fara jiyo nishi mai karfi daga cikin dakin su. Da gudu ta ajiye bokitin ta shiga dakin, Umma ce dake kwance alamun bacci amma kuma kuka takeyi, kuka sosai tana murza hannunta alamun neman yafiya. Kursum hankali a tashe ta karasa ta rungumeta tana mata addu'a. Umma kam babu abinda take cewa sai "A'a banda Kursum na tuba, na tuba...." Wannan kalmar kaɗai take faɗa har sai da bacci yai gaba da ita tana ta shafa mata baya tana mata addu'a. Ganin tayi bacci yasa ta fito a hankali, idanuwanta duk sunyi jaa kwanan nan duk ta rame saboda abubuwan dake faruwa dan ko makarantar ma ta daina zuwa gaba daya ta hakura da karatun, rayuwar yi take kawai. Hannu takai zata ɗau ki kayan ta ƙarasa shanyawa ta hangoshi yana tahowa. Kallansa tai tana tuno kalamansa na jiya, to ita ya zatai? Baki ta buɗe zata gaisheshi kawai taga ya dauke kai kamar bai ganta ba. Da kallo tabishi tanaji kamar ta saki kuka, meyasa bazai fahimci abinda ke damunta ba? Hawaye ne taji sun gangaro mata. Shareshi tai ta cigaba da shanyarta.
Dangin Ahmad sunje gun mai unguwa an tambayar mai aure anan mai unguwa ya bada ita ya kuma sanar da tunda gobe juma'a a ɗau ra auran bayan massalaci sai a tare duk sanda aka shirya, wannan labarin ba ƙaramin da ɗi yaiwa Inna ba sanda aka sanar da ita. Ahmad ana sanar mai ya taho da sauri gidan dan ya sanar da ita. A kofar gida yaga Nafi'u. Umma data fito tana ganin Ahmad ta juya da gudu tana sanar wa Kursum akan zuwanshi. Inna kam gaba ɗaya murnar auran nan take sam bata kula da sanda Yagana ta turo aka kwashe mata kayanta jiya da daddare ba. Tana hango Umma tana kwallawa Kursum ƙira ta saki wani murmushi dan tabbas yau hankalinta ya sake kwanciya. Da kanta ta fito inda Kursum ke gyaran dawar da za'ai tuwo tace "Ajiye kije kiga Ahmad a yanzu shi da mijinki babu maraba, dan haka tun yanzu ki fara jin maganarsa. Ajiyewa tai ba tare da tace komai ba ta koma ɗaki ta zura hijab ɗinta ta fito. Sai dai me? Babu kowa a wajen sai Nafi'u dake zaune yana karatun qur'ani. Mamaki ne ya kamata dan tabbas Umma tace mata yana nan. Kallan Nafi'u tai tace "Ya Nafi'u bakon da yazo fa?" Wani kallo ya mata yace "Ki duba da kanki, ni bansan wani bako ba." Iskar bakinta ta ɗan furzar tana kallanshi tana jin daɗin yanda yanzu bashida aikin yi idan ba karatun qur'ani ba in dai baya komai. Juyawa tai ciki, Inna na ganinta tace "Me kikeyi har kin dawo?" Kai ta girgiza kafin tace "Babu kowa a wajen kila wani abun ya taso ne yaje ya dawo.” Cike da jin dadi Inna tace "Ai naga ƙoƙarin sa ma na zuwa shi da za'a aura masa ke gobe ai da ya jira." Gaban Kursum ne yai wani irin mugun faduwa, da sauri ta kalli Inna hankalinta a matukar tashe tace "Gobe?" Nan da nan Inna ta tamke fuska tana gyara zaman dankwallinta tana cewa "In haka ne kinada matsala ne? Ko kuwa cewa zaki ba'a isa ba?" Kanta ta sunkuyar kasa tace "A'a bance ba." Tai maganar kanta na kasa. Inna taja tsaki tana kwallawa Raheena kira. Jiki a sanyaye Kursum ta juya ta shiga ciki. Fadawa kan ƙaramin gadansu tai kawai ta fashe da wani irin kuka, bawai tanada zaɓi bane amma a kalla ko yaya ne a nuna mata rayuwarta ce. Ta dade tana kuka kafin ta daure ta fito ta cigaba da aikinta.
Chapter 19 · 0% Book details