← Book details Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 27

Sashe 20

Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan la'asar Kabir ne zaune gaban Mai unguwa yana sanar dashi burin mahaifinsa, yayi mamaki sosai da mai unguwa ya kalleshi cikin kwanciyar hankali yace "Nayi mamaki da aka ce Ahmad zai aureta amma sanin halin Sameera yasa nai shiru. Ka sani ita da kawarta halinsu daya na kuma sansu in suka kafe a abu wani sa'in sai dai ai hakuri a sakar musu. Sai dai kana ganin hakan shine mafita?" Kabir ne yai murmushi kafin yace "Eh Kawu zan sanar da Ahmadu da kaina yai hakuri sai dai zan rokeshi in da hali karya bari mutane su sani. Mu kuma gobe in akazo daura auren mai makon a sa sunansa sai a sa sunana kaga Inna ko zatai fada an riga da anyi faɗan bazaiyi karfi ba." Kai ya jinjina cike da gamsuwa kafin yace "Sai dai akwai matsala daya, baka tunanin zata iya sa ka saketa?" Shiru yai yana tunanin abinda zai ce. Mai Unguwa ne yace "Abar ma maganar Ahmad dan shi akwai matsala ta bangarensa wanda ni kaina bansan menene ba, zaman nan da kaga nayi a waje baifi minti goma da barin nan ba." Kafin Kabir yai magana Mai unguwa ya cigaba "Ahmad ɗazu yazo yace inda hali a jinkirta auransa da Kursum akwai abinda yake tsoro, tunda ya tafi nake zaune anan nake tunanin menene wannan abin? dan iyayensa na san auran kuma kaf garin nan kowa yasan da san da yake mata." Cike da tsananin tashin hankali Kabir yake kallanshi yace "What? Meyasa? Ahmad da kansa? Yana santa meyasa?" Kai Mai Unguwa ya girgiza alamun rashin sani yace "Shine tambayar da nai mai amma yanda naga ya shigo a firgice haka naga ya fita ba tare da ya bani amsar komai ba." Kabir hankalinsa ya tashi, ya fara tunanin menene yake faruwa da Kursum ɗin!!

_Ni kaina tambayoyin dake kaina nake neman amsarsu sunyi yawa. Amma dai muje zuwa_.........

700 ne Kacal 🤌🏻
7065283730
Opay
khadija Abdullahi shehu.

Katin waya MTN ta 07065283730

Shaidar biya ta 07065283730 or +447894142004

Ayusher Ce🏌🏻‍♀️
RIBAR ƘAFA

NA

Wattpad :-AyusherMohd

Arewabook:- Ayushermuhd

ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️

Paid Book......

Shafi na Goma sha Biyu

A maimakon Kabir yai murna da abinda kunnensa suka jiye mai, Ji yai gaba daya jikinsa yayi sanyi, haka ya fito daga gidan kai tsaye majalisarsu ya nufa dan neman Ahmad sai dai baya nan. Dawowa yai ya nufi gidansu. Yaro ya tura ya kira masa shi, sai dai yaran ya dawo yace ance baya gidan. Fuskar Kabir dauke da mamaki yake bin gidan da kallo, kamar zai wuce sai kuma ya kara tura yaran nan ya kira masa Yayan Ahmad din. Baifi minti biyar da aika shi ba sai gashi ya fito, cike da farin ciki ya mikamai hannu suka gaisa yana cewa "Wai Kabiru dama kai ne? Ai da ka sani ka shigo ciki, gun Angon gobe ka zo kenan?" Sumar kansa ya shafa yana ɗan ƙasa da kai kafin yace "Eh na nemeshi ne ban samu ba shine nace bari nazo ko yana gida." Fuskarsa ɗauke da fara'a yace "Kasan ba zama tunda gobe aure tun safe da ya fita bai dawo ba, abinka da ba sabanba kuma baiyi tsammanin za'a bashi ita haka da sauki ba." Kallan Kabir yai sai kuma yace "Kila ai ka baroshi can dan bai wuce yana can gunta zance ba." Ajiyar zuciya Kabir yai ya dan gyara tsayuwarsa yace "Yaya ba dai wani abin ko?" Kallan sa yai alamun rashin fahimta kafin yace "Wani abin? Ba komai kardai zuwa yai yace sai ta tare a goben?" Hannunsa ya ɗan girgiza alamun a'a kafin yace "A'a bari na duba gidan." Yana tafe yana mamakin abinda ke faruwa ya sani Ahmad ya dade yanasan Kursum dan haka ba yajin akwai abinda zai hanashi auranta, da ace ba mai unguwa bane ya faɗa mai da bazai yadda ba. Har ya isa tunani bai bar ransa ba. A tsakar gida ya ga Inna kallo ɗaya zaka mata kasan ranta a ɓace yake. Ajiyar zuciya yai ɗan Inna kwanan nan ya rasa meke damunta, shiga yai ko karasawa ciki baiyi ba ta fara faɗa "In baya yin auran ai shi Malam Badaru nayi, aikin banza kawai ni wallahi shi yasa ko birgeni bayayi, sam bashida tunani bare nutsuwa ga fada kamar wani karen maguzawa." Jin kalaman Inna yasa ya shiga ciki da sauri. Kallan Inna yai cike da mamaki yace "Ahmad ɗin ne ya fasa auran?" Mayafinta dake hannunta ta yafa tace "Barni da ɗan banza, har da kanshi ya shigo cikin gidan nan yana sanar dani ya fasa, kaima wawa bansan ya akai kake kawance da soko irinshi ba." Yawun bakinsa ya haɗiye zaiyi magana ya hango Kursum riƙe da kaya da alama shanya ta gama kwashewa. Murmushi ta mai wanda tana gamashi hawaye suka biyo kuncinta. Juyawa tai ciki a hankali ya runtse idanunsa ya zai yi ya hanata zuwa gun Malam Badaru? dan inhar yasan za'a bashi Kursum basu isa su canza sunan ango ba dan kuwa shi ba kamar Ahmad bane. Har ta fita sai dai batafi minti hudu ba sai gata ta dawo tana tafe tana huci sam bata kula da mayafinta daya gama sauka daga kanta ba saboda tsananin ɓacin ran da take ciki. A waje taga Kabir yana ƙoƙarin fitowa daga ɗakin su da alamun gun Baba yake. Wani irin burki taja tana mai wani kallo kafin ta fara takowa fuskarta na wani irin canzawa, sai da ta zo dab da inda yake kawai ta ɗaga hannu kamar wacce zata mareshi. Hucci kawai take kamar wata kumurci ta nunashi da yatsa cikin kumfar baki tace "Haka tsohon ka ya baka shawara? Munafircin da kuke shirin min kenan? To wallahi bari kaji na faɗa maka, idan har ina numfashi bazaka auri yarinyar nan ba, in kuwa ka kuskura ka bijere min ka aureta na rantse da wanda numfashina ke hanunsa babu wanda ya isa ya hanani sai na tsine maka. Daga kuma ranar na rabu dakai kenan har abada." Gaba ɗaya mamaki ne ya bayyana a fuskar sa, ya akai taji? Kila gidan Mai Unguwa taje? Ji yai har kafafunsa na rawa, cikin rawar murya yace "Tsanar da kike mata har ya kai haka Inna? Yarinyar nan fa a gabanki ta taso, bakya tsausayinta? Taya......" Yatsunta ta nuna mai a fusace kafin tace "Kai kasani kaf yarana ba wanda nakeji dashi sama da kai, dan haka babu yanda za'ai na baka yarinyar da bansan asalinta ba, ba'a san dangin uwarta ba ba'asan yanda akai aka samu cikinta ba, yanda batada hankalin nan wayasan maza nawa ne sukai amfani da ita har aka samu cikinta? Wallahi kaf duniya babu wanda ya isa ya aurama ita. In kuma ka shirya yanke alaka dani bismillah." Tana kai nan ta shiga ciki, zuciyarta har bugawa take saboda tsananin ɓacin ran da take ciki. Alhaji Nuhu Danbatta dake zaune duk abinda ake yanaji kwalla kawai ke sake taruwar mai, ganin ta shigo yasa ya daure tare da zare mask ɗin dake hancinsa yace "Sameera dan Allah... dan Allah! Na rokeki da Allah ki bar Kabir ya kula da yarinyar nan, bakya tausayin halin da zata shiga?" Wata dariyar takaici Inna tai tace "Ni nasan kaine ka samai wannan abun a ransa kila shi yasa Allah ya dubi zuciyata yasa na sani da na tabbatar wani abin zaku kulla ban sani ba. Sai dai ina sake sanar daku ni dai wallahi bada yawu na ba kuma ba da jinina ba kaje can ka nemi wanda zaka bata, inba haka ba gobe Badaru ya aureta na baku nan da bayan magriba in ba haka ba zan sanar wa Malam Badaru ya fito ayi dashi." Tana kaiwa nan ta sake yafa mayafinta ta fita. Tana ganin Nafi’u zatai magana taga ya ɗauke kai cike da kuluwa ta cigaba da tafiya tana masifa. Yaron nan kwanan nan taga rashin kunya yake ji da ita, sallamarshi shima zatai haka kawai yanzu nauyin gida ya dawo kanta bazata bari wasu ƴan kalan dangi su hanata rayuwar jin daɗi ba.

Nafi’u ciki ya shiga ganin Kabiru a waje yasa yasan akwai matsala, kamar zai kulashi sai kuma ya fara neman yin ɗakin su. Muryar Kabiru yaji yace “Nafi’u zo ka taimaka ka duba Baba, banasan shiga dan nasan yana cikin wani hali.” Dawowa yai da sauri ya shiga ciki da sallama. Alhaji Nuhu Danbatta ya gani a ƙasa, da sauri ya shiga ciki taya akai ya faɗo daga kan gadan? Cikin hanzari ya fara taimakamai sai da yaga ya kwanta sannan ya mai da mai oxygen ɗin, kallan catheter ɗin yai wato abin jawo fitsari, ya kalli Baba yace “Ina ganin ya kamata suzo su cire abin nan kar ya jawo maka infection.” Kai ya ɗaga cikin dakushashiyar murya yace “Ina ji a jikina lokacina ya kusa zuwa karshe, gashi har yanzu bakasan asalinka da dangin ka ba.”

Jikin Nafi’u ne yai sanyi ya kama hannunsa yace “Baba a yanda nake rayuwa daku bani da matsala sai dai na gode muku Allah ya saka da alkairi.” Idanunsa Alhaji Nuhu Danbatta ya kalla wani abu ne yazo mai da sauri ya kara matse hannun Nafi’u yace “Nafi’u na taɓa cutar dakai?” Da sauri ya girgiza kai alamun a’a. Ya sauke ajiyar zuciya yace “Kursum fa? Ta taɓa cutar dakai?” Cikin sauri ya girgiza kai yace “Ko da wasa.” Kai ya ɗaga cikin jin daɗin da ya bayyana a fuskarshi yace “Iyayenka sun rasu wanda nake sa ran kafin kasan danginka zaka zauna a nan, inda hali islamiya ta zan nemi su baka aiki a ciki tunda kai kasan abubuwan birni, dan Allah ka taimakeni ka auri Kursum yanda na riƙe ka da zuciya ɗaya ka rike min ita dai zuciya ɗaya.” Shiru yai saboda hakkin da yakeyi dan indai yana magana numfashinsa canzawa yake. Bayan shi Nafi’u ya shiga shafawa kafin ya sauke ajiyar zuciya yace “Nasan Umma zata zama takura a gareku, amma kuyi hakuri ka taimakeni ka kula da ita dan Allah.”
Chapter 20 · 0% Book details