Sashe 14
Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Gaba daya jikin Alhaji Nuhu ne ya dau rawa muryar Inna ce ta katseshi da take tambayarshi "Alhaji lafiya?" sai a lokacin ya dan dawo hayyacinsa, kallanta yai tare da bin wayarsa wacce ta tsuguna ta dauko mai da kallo, sai a lokacin ya tuna ashe bai ji sunan asibitin da suke ba, wayar ya amsa daga hannunta ya danna number DPO sai dai har ta katse bai dauka ba, kara kira yai nan ma har ta katse bai dauka ba, yawun bakinsa ya hadiya jiki a sanyaye yake kallan Naziru dake jingene jikin bango har lokacin, idanuwansa a rufe wanda yanzu kam yake tunani bacci ne ya daukeshi dan inba haka ba da yaji kiran da Inna keyi. Saman goshinsa ya dafa yai daki da sauri, bin bayanshi tai ya zauna a bakin gado tare da hade hannayensa guri daya yana matsasu, kusa dashi taje ta zauna tace "Menene? Ba iyayenshi bane?" Kallanta yai jiki a sanyaye dan har idanuwansa sun canza yace "Samira sun taho a hanya sukai hatsari." Salati ta saka cikin tsananin tashin hankali take kallansa tace "To yanzu ba iyayen nashi bane kenan ko me?" Kai ya girgiza alamun rashin sani kafin yace "Ina muka sani? Ni yanzu abinda naji a waya ma shine ya tadamin hankali, naji ana sanar da DPO amaganar rasuwarsu, Samira ya zamuyi? Dan dai adalilina iyayen yaran nan suka rasu dan da ban bigeshi a mota ya kamu da ciwon mantuwar nan ba da kila......"Da sauri ta dafa kafadarsa tace "Dan Allah kar kai irin wannan tunaninm sannan yaran nan da kake gani shi....." Da sauri ta maida kalam da take kokarin yi kallan tuhuma ya mata yace "Shima me?" Kai ta girgiza tace "Shima yasan ba da saninka bane, shekararka nawa kana tuka mota? Shi tsautsayi in Allah ya kawo fa ba yanda zakai." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Na sani Samira damuwata bazai gan da iyayensa ba, gashi yanzu inasan kaishi asibiti bansan wani asibitin suke ba." Wayar sa ya dauka ya kara kiran DPO sai dai yanzu wayar ma yaji a kashe gaba daya, ya zaiyi? Mikewa yai ya alleta yace ? Bai na daukeshi muje garin Kano in yaso a hanya zancigaba da gwada number shi ko Allah zaisa a dace" Shiru tadan yi na wasu dakiku kafin ta waigo gaba dayanta saitinshi tace "In kuma kaje har kuka gaji da jira baizo ba fa?" Ajiyar zuciya yai kafin yace "Amma kinsan rashin zuwan hankalina kawai zai tada, a ƙalla ko gawarsu ne ya gani." Yana kai nan ya miƙe dan hankalinshi sam baya jikinsa, Inna ta mike itama yana canza kaya ita kuma ta ɗau wayarshi ta ƙira Kabiru, yana ɗaki yana shan bacci, jin bai ɗauka ba yasa ta fito ta kalli Nafi'u dake bacci, ta maida idanta kan Umma tace "Ramla ƙira min Kabiru, in bacci yake ma kice ya tashi." Da gudu ta mike ta hau tsalle tana "Kabiru Kabiruruuu Kabiruuu." Yaye labulen sa yai yana sanye da gajeran wando ba ko vest babu a jikinsa, da alama yanzu ya tashi. Ihu tasa tace "Kato ba kaya." Labulen yasa ya ɗan rufe jikinsa kafin yace "To na kule ya akai?" Ta harareshi kafin tace "Kazo inji Inna yanzu-yanzu." Komawa ciki yai yana cewa "Ganinan zuwa kice Kursum ta samin ruwan zafi." "Kusum Kursum nan ta koma ƙasa tana ƙiran ta, sam ta manata ta sanar da ita zataje makaranta, idanuwansa ya buɗe jin ana ƙiran sunan Kursum ganin Umma ce yasa yace "Batanan Umma kizo ki zauna," Kuka tasa tana cigaba da kwallawa Kursum ƙira, kallanta Nafi'u ya shiga yi yana mamakin yanda akai mace babba haka take abu kamar karamar yarinya, basu fi minti biyu ba sai ga Alhaji Nuhu Danbatta ya fito sanye da manyan kaya, kalan Nafi'u yai wanda ke ƙoƙarin mekewa tsaye yace "Nafi'u ka ɗan hanzarta kai wanka kace Kabiru ya baka manyan kaya ka saka ka fito zamuje wani guri," yai maganar cikin sanyin murya. Bai tanka ba sai kawai hanyar sama dayai, Alhaji Nuhu Danbatta ya bishi da kallo jikinsa na ƙara sanyi yanzu in iyayenshi ne ya zaiyi? Zai ganesu? Yana nan tsaye har sai daya shiga ɗakin Kabiru gaba ɗaya tunani sun mai yawa. Adda Yagana ce ta fito taci uban gayu kai kace biki zata fita, haɗa idan da sukai da Alhaji Nuhu Danbatta ne yasa ta ja ta tsaya turus, tana kikifta ido, wani mugun kallo ya zabga mata yace "Ke wato idanki yayi karfi gaida iyayenki ma wahala yake miki ko?" Kanta ta sunkuyar kasa tana cewa "Baba ina kwana? Da safe bacci ne ya hanani tashi." Cike da takaici yace "Eh ai da a gidan mijin ki kike dole ki tashi ki shirya yaranki su tafi makaranta ko?" Baki ta turo tana ɗan magana kasa-kasa, yana kallan abinda takeyi ya kuma san rashin kunyarta ne yasa suka samu sabani da mijinta "Yanzu ina zakije?" Cikin ɗan kukuninta tace "Baba bikin kawata akeyi yau zata tare shine zanje na ɗau yaran muje." Wani kallo ya mata yace "Tunda kin isa ai ba sai kin tambayi uzuri ba kiyi abinda ya miki kawai." Yana kai nan ya shiga ciki ransa a ɓace, maimakon ta koma ciki fitarta tai tana cewa "Nidai ba yarinya bace, da girmana nasan abinda ya dace." Kabiru ne ya fara fitowa kafin Nafi'u, Inna ta kalleshi bayan sun gaisa tace "Kursum na makaranta kasha shayi gashinan ka wuce ka tuka mahaifinka garin kano." Kallanta yai baki a buɗe kafin yace "Da gaske ta tafi makaranta? Inna anya ba cin hanci Baba ya baki ba? Dan dai a iya sanina bazaki taɓa yi mata kara ba." Shafa kanta tai ta mike tsaye tana cewa "Kai dai ka sani." Har ta tafi ta dawo tace " Ga wannan ku riƙe in kun fita kwaci abinci." Ajiye cup ɗin tea ɗinsa yai ya zuba mata ido alamun zargi, kauda kai tai da sauri tace "Kai dai ka sani sai sa ido kamar wani mai aikin ɗan sanda." Tana kai nan tai ciki tanawa Alhaji Nuhu Danbatta magana akan ya fito sun shirya. Kabir kuwa mamaki ya kasa barin fuskarsa tabbas akwai abinda Inna take boyewa, wannan canjin nata bai yadda dashi ba. Nafi'u ne ya fito sanye da kayan Kabiru, nan da nan ya tamke fuska yace "Ba laifi kayan nawa ya fito dakai." Shi dai Nafi'u baice komai ba. Alhaji Nuhu Danbatta ne ya fito ganin Nafi'u cikin kayan Kabir na sallah yasashi murmushi yace "Kaga ka fito a babban mutum ɗin ka." Baki Kabir ya taɓe yace "Kayana dai ya fito dashi." Haka suka fito Baba ya zauna a baya, Kabir ya ja shi kuma Nafi'u ya zauna a gefensa suka wuce. A mota Kabir ne ke ta surutu ganin ba wanda ya kulashi yasa ya kuna karatun qur'ani a motar suna tafe yana bi, sun ɗan yi nisa kafin ya ɗan kalli Nafi'u ta gefen ido yace "Naji kayi karatun boko, na islamiyya fa? Ko baka iya ba?" Shiru yai wanda hakan yasa Alhaji Nuhu Danbatta kallansa ta baya, Kabir ne yai wata dariyar isgilanci yace "Ahaf ni dama nasan za'a rina dan ko yadda kake sallah ban yadda kana karanta wani abin arziki ba, ai ko ka manta abubuwa baici ace ka manta karatun islamiyya ba tunda karatun bokon ma na kanka." Shidai Nafiu shiru yamai dan bashi da niyya ko alamar kulashi. A bayan mota kuwa banda numbern DPO da yake ta gwadawa ba abinda Alhaji Nuhu Danbatta keyi, har wannan lokacin wayarsa a kashe take gashi sun shigo Kano. Nan police station sukaje sai dai an sanar dasu bayanan, kuma ba'asan wani asibitin yake ba. Haka suka fito suka zauna a waje har yamma babu shi babu labarinsa babu kuma wayar sa. Ganin magriba ta kawo kai yasa suka koma Danbatta. Shiru Alhaji Nuhu kawai yai yana tunani gashi kuɗin hannunsa da ya ara sun kare gashi bai san meke faruwa ba. A hanyarsu ta dawowa Nafi'u baccinsa yasha, suna isa gida ana kiran sallar magriba. Ihun oyoyo da Umma ke yi ne yasa Kursum fitowa daga kitchen dan girkin dare takeyi, tana fitowa idanunta suka sauka kan Nafi'u wanda ke sanye da manyan kaya, yana ganinta ya saki murmushi da sauri ya ƙarasa inda take yace "Kin dawo?" Kai ta ɗaga alamar eh cike da kunyar yanda ya nufota, mamaki ne ya kama Kabiru ya zabga mai wani kallo yace "Wato kai ɗan rainin hankali ko? A hanya inama maganar karatu kaki kulani amma yanzu kaga Kursum ka wani tafi da gudu. Kursum din zamanka take? Ko ƴar uwarka ce?" Zatai magana ya zabga mata wani kallo yace "Kafin yabar gidan nan islamiya zai fara, dan naga zaman gidan nan da yakeyi in ba nan aka kaishi ba akwai alamar tambaya." Wani kallo Nafi'u yamai wanda haka kawai Kabir yaji kallan har ransa, irin kallo ne na ɓacin rai da kwarjini wanda da alama shi kansa bai san yayi ba. Muryar Inna ce ta katsesu da cewa "Kursum zo ki wuce ki ƙarasa girki." Tai maganar tana kallan Kabir da Nafi'u. Da sauri ta kama hannun Umma. Fisge hannunta Umma tai ta juya tana cewa "Nafi'u ka siyomin alawa?" Kai ya girgiza alamar a'a, kafin yai ciki fuskarsa har lokacin ba wargi.