← Book details Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 27

Sashe 11

Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A waje kuwa Nafi'u sai daya nunawa Kursum yanda zata gane, anan ne ya fahimci lalai batasan abubuwa dayawa ba, ko dai ba'a koya mata ba ko kuma ba ta karatu, Umma tana zaune gefensu sai tsale take tana maimaita karatun da sukeyi. Ganin yamma tayi yasa Kursum tace "Bari nai sallah nasa girki, nagode sosai, kaima ka tashi kai sallah." Hanayensa ya haɗe, ya ɗan furzar da wata iska dake bakinsa kafin yace "Yanzu?" Kai ta jinjina tace "Eh, la'asar tayi anjima za'ai magriba kaga sai isha'i a kwanta." Umma da sauri ta matso tace "Nafi’u kayi maza kai sallah, kafin Kursum tace Allah zai kona mara sallah a wuta, wuta balbal balbal." Hannu Kursum tasa ta riko Umma kafin tace "Umma!" Kallanta yai wanda haka kawai yakeji yanasan kallan fuskarta, tsarguwa tai da yanda yake binta da kallo, dagowa yai suka hada ido, wani irin kallo ta tsinta a idanunsa wanda shi kanshi da alama bai ma san yanayi ba. Kauda kanta tai da sauri ta kama hannun Umma suka bar gun. Tana zaune tana girki su Hasina da Rahina suka tafi islamiyya, Alhamdulila bata damu ba duk kuwa da tanasan zuwa yin muraja'a. Kursum hafizar qur'ani ce dan kuwa tayi saukar hadda shekara ɗaya daya wuce, taje musabaka inda ta wakilci garin Danbatta anan tazo na ɗaya ta wakilci garin Kano anan taci na uku bayan ta dawo ne kuma bata sake zuwa wata musabaqar ba sai dai a zuwanta na karshe ta samu alkairi dayawa anan ne Alhaji Nuhu Danbatta ya sai mata gona ita da mahaifiyarta da kuɗin, ta rokeshi akan ya biyawa su Hasina kudin makaranta, kin yadda yai anan ne Inna ta amsa taje ta biya wanda wannan ne mafarin samun matsalar Inna da Baba. Kursum na gama girki ta wuce ɗaki ta ɗau qur'anin ta ta fara muraja'a wanda a koda yaushe shine ke sa mata nutsuwa. Bayan sallar magriba ta fito dan ta wanke kwanukan da aka ci abinci, ta fito sanye da hijab ɗinta ƙarami mai santsi wanda take zaman gida dashi, kwanuka ta ɗauka wanda taji ansa hannu an amshi kwanukan dake hannunta, kallansa tai a hankali kafin cikin sanyin murya tace "Ya Nafi'u ka bari zan ɗauka da kaina." Bai tanka mata ba sai da yakai inda take ajiyewa, ja yai ya zauna a gefe yana kallanta. Cike da mamaki take binshi da kallo tace "Ka koma ciki dan Allah." Kai ya girgiza a hankali, zama tai a gefen tana wanke wanken, duk a takure take jin ta bare tana ganin kamar idanshi na kanta, gashi ko magana bai yi ba tunda ya zauna. Wani irin faduwar gaba takeji, a tare sukace "Nace!" Murmushi ta saki tace "Kace me?" Sumar kansa ya shafa kafin yace "Karatun qur'anin da kike yau bakiyi da ƙarfi ba meyasa?" Kallansa tai tana ƙoƙarin ajiye plate ɗin data dauraye a hankali tace "Naga gidan da mutane ne bana san na takura ma kowa." "A ina kika iya karatu haka?" Ya tambayeta idansa na kanta, musmushi tai tace "Islamiya? A kalla dai wannan karan ka yaba karatuna ba kamar na boko ba." Shiru ya ɗan yi zata sake magana taji yace "Ban taɓa jin karatu mai da ɗin naki ba." Jin kalmar tasa tai ta ratsa ko ina na jikinta, a hankali ta kalleshi kafin ta maida kanta ƙasa da sauri, kasa magana tai dan wani irin faduwa gabanta ke cigaba dayi, sunfi minti biyar ba wand yai magana dan har ta dauka bazaice komai ba sai taji yace "Banci abinci bama yanzu ni ba nasan wannan abinda kukecin." Idanunta ta maida kanshi da sauri kafin tace "Tuwo wai? Bari na tambayi Baba ko za'a siyoma kayan tea ni babu kudi a hanuna wallahi." Ajiyar zuciya yai kafin yace "Akwai wahala rasa abinda mutum zaici." Idunuwansa ta ɗan kalla tare da waigo wa sosai tace "Ka tuno wani abin ne?" Kai ya girgiza a hankali alamun a'a kafin ya sauke ajiyar zuciya yace "So annoying ko?" Kai ta girgiza alamun a'a, tanayi ta mike tana kwara ruwan ɗaurayar dan ta wanke gurin. Umma ce ta fito tana hamma da alama farkawa tai daga baccin da takeyi da sauri tace "Umma kin tashi ne?" Kai ta ɗaga mata alamar eh sai ta wuce bandaki. Juyawa tai ta fara tafiya kafin tace "Zan nemi Ya Kb muga ko zai taho da madara da milo." Kai ya ɗaga yana kallanta har sai da ta shiga ɗaki. Yana waigawa suka hada ido da Inna wacce ke tsaye tana kallanshi hannayenta a harɗe, mikewa yai yana ƙoƙarin wucewa ɗakin Kabiru rai a ɓace tace "Kai baka iya gaisuwa bane?" Dawowa yai sai dai baice komai ba, mamaki ne ya kamata wanda yasata ware idanuwa tace "Ka tabbatar baka tuna abinda ya faru da kai ba? Wanene kai? Sunan ka? Ko sunan iyayenka?" Kansa ya maida kasa ya girgiza kai a hankali kafin yace "Kuyi hakuri." Ajiyar zuciya tai ai dai gobe iyayenshi zasu zo, ita da zasu taimaka ma da ya auri Kursum su bar mata gida dan yanda yake kallanta da shishige mata tabbas tasan da biyu. Kursum bayan tayi sallar isha'i Kabir ta ƙira a wayar Hasina sai dai masifa ya hau ta dashi akan bazai siyo ba in bazai ci tuwo ba ya mutu da yunwa. Haka kawai yake jin tsanar yaran shi sam bai mai ba, da wani dogon hancinsa kamar na mayu, ya ƙarasa maganar yana jan tsaki.

Washegari Alhaji Nuhu Danbatta tun safe ya tashi yana sauraren ƙiran DPO, kayan tea ya siyo akasha tea da bread, yana zaune a tsakar gida sai ga Kursum ta fito sanye da kayan makaranta a jikinta, farare ne sai kasan an musu ratsin green yasha karin gugar da tayi a kasan katifa, mamaki ne ya kamashi dan ji yai ya kasa amsa gaisuwar da takemai sai cewa tai "Ya akai kika canza shawara?" Kai ta girgiza a hankali tana tsugune tace "Bansan dalili ba haka kawai Inna tace na tashi na tafi makaranta." Bai san sanda yace "Samiran?" Kai ta ɗaga alamar eh kafin tace "Nagode sosai Baba insha Allahu bazan baka kunya ba." Mamaki har lokacin bai bar fuskarsa ba yace "Masha Allah, ki tashi kije karkiyi latti." Mikewa tai ta fita da sauri shima ya tashi ya shiga gida, Nafi'u ya gani a waje shi da Umma tana zaune shi kuma yana gefenta ya lumshe idanuwansa kamar mai bacci, cikin ɗan daga murya amma ta farin ciki ya fara cewa "Samirah! Samirah kina ina?" Fitowa tai tana cewa "Kai fa Malam inaji da kai ka radamin sunan nan da ina cikin wani hali saboda damuna da kira." Fuskarsa a sake yace "Kai matarnan Allah ya miki albarka, ya ƙara miki lafiya." Tasan me yake nufi hakan yasa ta kalli Umma tace "A kalla yau ta samu abokin wasa." Murmushi ne sosai a fuskarsa zaiyi magana sai ga waya ta shigo, kallansa tai cikin maganar raɗa tace "DPO ne?" Kai ya ɗaga sannan ya ka ra wayar a kunnensa tare da yi sallama. Daga can DPO yaji yana salati "Inalilahi wa ina ilaihi raji'un Alhaji Nuhu muna nan asibitin hatsari iyayen da sukace Nafi'u ɗan su ne sukai da matar da mijin, gamunan a asibiti amma banaji zasuyi rai." Hankali a tashe ya fara salati dan gaba ɗaya jiyai jikinsa ya ɗau rawa yace "Kuna ina? Bari nazo zan taho dashi inalilahi." DPO cikin sanyin murya yace "Kada kai tuki ko ka hau motar haya a wannan yanayin, ka bari muji daga garesu, tsautsayine ya afka dan na sanar musu akan su jirani muzo tare amma suka kasa hakura, sai dai sun taho da hotunan yaran kuma tun yana ƙarami duk akwai pictures dinsu tare." Alhaji Nuhu Danbatta na ƙoƙarin magana yaji muryar wani yana cewa "I am sorry to say amma Allah ya dauki ransu." Wayar hannunsa ce ta sulale kasa "Inalilahi wa ina ilaihi raji'un, meke faruwa? Gaba ɗaya ji yai kansa ya kulle.

7065283730
Opay
khadija Abdullahi shehu.

Katin waya MTN ta 07065283730

Shaidar biya ta 07065283730 or +447894142004

Bonanza ki biya 500 daga yau zuwa 12th ga wannan watan kunsani ni da ku 5&6🥰

Ayusher Ce🏌🏻‍♀️
RIBAR ƘAFA

NA

Wattpad :-AyusherMohd

Arewabook:- Ayushermuhd

ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️

*Gaisuwa tare da jinjina da fatan alkairi gareku ɗaukacin masoyana a duk inda kuke, ina mika sakon gaisuwa gareku, dafatan kowa yana lafiya. Musulmai da suka rigamu gidan gaskiya Allah ya jikansu, mu da muke da rai Allah ya sa mu gama da duniya lafiya, masu ciki Allah ya saukesu lafiya, wadanda ke neman haihuwa Allah ya basu. Masu neman aikin yi Allah ya taimakesu yasa su samu. Ƙasar mu Nigeria Allah ya shiga lamarin ta ya kawo mana gyara Ameen suma Ameen.*

Oh ina fatan me karatu yayi saurin cewa Ameen..... lol duk da nasan ke ko kai ka fada..........

SHAFI NA FARKO

Duk abinda ke faruwa a wannan lokacin kwakwalwarshi naji sai dai idanuwansa sun kasa buɗe wa sosai, dakyar ya iya ɗan motsa idanshi na hagu wanda yake jin nauyinshi sosai. Mutane biyu ya gani suna janshi a ƙasa, ga wani azababen ciwon kai dake damunshi wanda yake ji kamar yasa ihu ba sai an fada ba harda jan da suke mai a ƙasa yasa yake ƙarajin kan nashi kamar zai faɗo kasa. Shin ko dai mutuwa yai? Ko Mala'iku ne ke janshi? Tambayar da ya yiwa kansa kenan, sai dai sam ba shi da amsar da zai bawa kansa, abu ɗaya yake tunawa abinda ya shaka a handkerchief last kafin ya farka cikin wannan yanayin da ya ganshi a ciki. Kamar a mafarki yaji ana cewa "Eh mun ɗauko shi, noo ba wannan maganar ku bamu kuɗin da kukace zaku bamu kafin mu fita, dan wallahi sai munga alert zamu bar nan." Sai kuma yaji ance "Kai Malan karfa ka raina mana hankali, bama san hauka dan Allah! Kasan saida ran mu da muka yi akan aikin nan? Ka dai san wannan ba irin aikin da muka saba bane ba ko?" Daga nan bai sake jin komai ba saboda wani bacci dayai gaba dashi.
Chapter 11 · 0% Book details