← Book details Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 27

Sashe 24

Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kabir cikin hanzari ya shiga ɗaki gun Alhaji Nuhu, wani irin kunci ne a fuskarsa wanda kallo ɗaya zaka mai ka fahimci haka. Inna ta idar da sallah kenan ya shigo ya zauna kusa da Baba yana maida numfashi kamar wanda yai gudu. Alhaji Nuhu Danbatta ya kalleshi jiki a sanyaye dan ya sani can ƙasan ransa yana san Kursum da alama kishi ne yake damunsa. Inna ce ta katse mai tunani da yin wani dogon tsaki kafin tace "Kasan Allah ka fita daga idona kaji na faɗa ma dan wannan halayen da kakeyi ya tabbatar min kana san Kursum." Ya za'ai ta gane abinda ke faruwa? Tambayar da yai wa kansa kenan kafin yace "Inna jiya waye ya faɗa miki maganar fasa auren Ahmad da Kursum?." Mikewa tai tsaye ta cire hijab tana mai wani kallo kafin tace "Wannan ba matsalar ka bace yarinya dai tayi aure dan haka ka shiga hankalinka." Tai maganar tana fita daga ɗakin. Shima mikewa yai ya fito dan abin na damunsa. A waje ya tsaya kusa da ita yace "Inna maganar aure na da Kursum fa?" Wani mugun kallo ta buga mai tace "Da ba dan Allah ya taimakeni Nafi'u ya faɗa min ba ai da munafurtata kaso kayi, soko kawai wanda har yanzu baisan ciwon kansa ba. Kai ko hauka kake aka ce ka auri Kursum sai ka aurata?" Jin bai amsa ba yasa ta waigo sai dai baya gun da alama yayi ɗakin su, cike da takaici ta girgiza kai ita yanzu Yagana take nema banda iskanci sai ta sulale ta bar gida wai ta maida auranta? Kwafa tai dan har gidan mijin sai taje taci mutumcinta.

Banko ƙofar ɗakin Kabir yai babu ko sallama yake kallan Yazeed Shehu Kankarofi wanda ke kishingiɗe da alama abu yake jira. Daga inda yake ya kalli Kabir ta gefen ido yace "Dama jiranka nake yi, zan wuce zan tafi da iyalina."

Wani murmushin takaici Kabir yai yace "Iyalinka? Tun Yaushe ka dawo hayyacinka ne? Ko dama can ba kai mantuwar komai ba ka bamu bakar wahala?" Kansa Yazeed ya kwantar jikin pillow yana kallan Kabir yace "Sai yaushe zaka koyi 1+1? Kai har yanzu baka iya maths ba ne?" Wani sauti Kabir yai da bakinsa yace "Kenan tun farko lafiyarka ƙalau ko?"

"Yes!" Kai tsaye Yazeed ya faɗa sai a lokacin ya mike tsaye yazo inda Kabir yake ya fara tafiya yana zagayeshi hannayensa cikin juna yace "Imagine kamar ni nasan anyi kidnapping ɗina ban farka ba kawai na gani a asibiti mutane na zaune kusa dani? Mutanen da ban taɓa gani ba? The only solution shine nai kamar bansan su waye ba dan nazo gidansu naga inda suke, nan ne zansa azo a kamasu su faɗi wanene ya turo su."

Kallan da Kabir yake mai yanzu kam ya koma na tsoro dan wannan ya wuce na mamaki.

Kafaɗa Yazeed Shehu ya ɗaga yace "Me zai faru bayan nazo?" Wani murmushin ya saki tare da shafar sumar kansa yace "Ina ganinta nasan matata ce ita, saboda ita na zauna a gidan nan haka kawai nake jin zan iya rayuwata da ita anan ba tare da na koma gun dangina ba. And you guys have the audacity kuce zaku mata auren da ba'a tambayeta tana so ko bata so ba? How? Kaf duniya babu wanda ya isa ya aurar mun mata dan halal ɗina ce ita."

Baki Kabir ya buɗe yana kallanshi cikin tsananin mamaki, gaba ɗaya jikinsa ya gama yin sanyi. Muryarsa na rawa yace "DPO ɗin ya akai yasan da kai?" Yatsa yasa a saman goshinsa ya ɗan buga kafin yace "A asibiti sanda akaje CT scan na faɗawa Dr ɗin ya hadaku dashi sannan nace yace ga abinda ke damuna, daga nan banaji kanada sauran tambaya dan DPO yaran gidan mu ne aka bashi mukamin, kaga kuwa maganar wasu iyaye da yace sunzo sun mutu duk plan ne saboda da naso zama kusa da ita. Amma da kai da mahaifiyarka kuka wargaza komai."

Cikin wani irin shock Kabir yake kallanshi kafin yace "You're really crazy baka cikin hayyacinka."

Komawa yai ya zauna yace "I am, dan tunda na taso duk wani abu da nakeso ba wanda ya isa ya hanani shi, sannan bana jin akwai abinda nakeso sama da ita wanda nakeji zan iya hakura da iyayena saboda ita."

Kasa magana Kabir yai dan tabbas yau ya yadda Yazeed bashi da hankali. Bai jira amsarsa ba yace "Idan har kai kuskuran sanar da Baba abinda ke faruwa ka sani zuciyarshi bugawa zatai, at least deep down banasan abu ya sameshi, daga nan ƙasar har wata ƙasar zan iya kaishi a dubashi wannan karan threats ne in kune yaji gangan jiki ya tsira." Yana kaiwa nan yazo daf da Kabir ya dafashi yace "Anjima DPO zaizo ya ɗauke mu da iyalaina, koda wasa karka nuna wani abin, wannan shine sharaɗina in na tafi duk abinda kaga dama kai wannan matsalarka ce." Kafin Kabir yai wani abu ya sa hannu ya ɗau wayarsa, har ya fita daga ɗakin bai dawo hayyacinsa ba, ji yake kamar abinda ya faru yanzun nan a mafarki ne. Yazeed ko dai baisan bashi da hankali bane? Dan wannan abinda ya faru dashi da mahaukaci a gurinshi duk ɗaya ne.

Yazeed Shehu Kankarofi kuwa yana fita daga gidan ya sauke wani ajiyar zuciya Kabir bai sanshi bane a tsarin shi ko menene yake so to fa dole sai ya sameshi ko ta wani hali ne kuwa, yaso dauketa tuntuni sai dai ganin yanda takesan Alhaji Nuhu da shima yanda yake santa ya ji zai iya zama a inda take har sai lokacin komawarshi yayi. Shi bai damu da kowa ba indai har abinda yakeso ya biya to bashida matsala da abinda ɗayan ɓangaren yake fuskanta. Wayar Kabir ya kira kai tsaye ya kira numbern Dr Sultan wanda babban likita ne anan Aminu Kano teaching Hospital tare sukai karatu dashi a ƙasar New york sai dai  sai da yaje final year yaji shi ya gaji da karatun kawai ya ajiye ya dawo gida, haka mahaifinsa yai ta faɗa ya gaji dan shi ko a jikin shi. Wayar ya kalla sai data kusa katsewa ya ɗauka bakinsa ɗauke da sallama. Cikin faɗa Yazeed yace "Kai dai har yanzu wannan banzan habit ɗin naka bazai barka ba, kana likita baza'a kiraka ka ɗauka immediately ba?" Sultan jin muryar Yazeed yasa ya mike tsaye cikin tashin hankali yace "Yazeed Shehu Kankarofi kaine? Kasan neman da Ummy ke maka kuwa?" Tsaki yai yace "Wannan ba shine a gabana ba akwai patient da zan turo gurinka, please duk wani abu da suke bukata ka tabbatar kayi musu, sannan ka nema musu gidan da zasu dan zauna kafin ya samu sauki." Kai ya jinjina yace "Wannan ba matsala bane amma......" Katse wayar yai ba tare da ya saurari mai zaice ba, murmushi yai yana mamakin yanda a ƴan kwanakin daya zauna anan bai nuna halayensa ba, duk da wani sa'in idanuwansa na rikeɗewa su nemi canza wa sai dai yayi ƙoƙari ya kuma daure baiyi ba. Hannu ɗaya yasa a aljihu yana auno kalaman Inna akan Kursum dole zai hukuntata sai dai zai jira Baba ya warke dan bazai yafe mata ba. 

Tunda Kursum ta fito yaji ya kasa magana, wannan abinda ke faruwa har yanzu ya kasa yarda. Kallan mamaki ta mai tace "Ya KB menene?" Idanunsa na kanta sai dai ya rasa ta ina zai fara magana. Inna ce ta kwalla mata kira wanda hakan yasa tabar inda yake ta nufi gunta, fuskarsa ya shafa yana tunanin abin yi dan gaba ɗaya kanshi ya kulle. Inna ganinshi tai ya biyo Kursum nan da nan ta haɗe rai ta sa Kursum ta shiga gun Alhaji Nuhu dake nemanta. Tana shiga ta maida kallanta kanshi tace "Ko kunya bakaji ka wani taho zolalo-zolalo, kasan Allah Kabir ka fita idona na rufe." Abu ne yazo mai rai yace indai har Yazeed zai kula da ita yana ganin shine mafita dan shi ya sani Inna bazata taɓa barinsa ya aureta ba. Sannan kuma da Malam Badaru ya aureta yana ganin gwara Yazeed ɗin in har zai iya tunanin barin danginsa saboda ita to tabbas zai kula da ita ɗin. Inna ce ta katse mai tunani da cewa "Nafi'un da kake gani dama can yana santa, ko ka ɗauka haka kawai na barta ta koma makaranta? Shi yai alkawarin zama da Umma akan na barta dan haka inma kana burin ya saketa ka aura ne ka cire shirman nan a ranka." Kai ya jinjina alamar to dan ya gama tsaida zuciyarshi. 
Chapter 24 · 0% Book details