← Book details Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 27

Sashe 27

Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Murmushi yai kawai. Ganin batada niyyar yin abinda ya sakata kawai yasa hannu ya ɗaga ta, ya cizge hijab ɗin jikin nata ya yar a nan falan. Wayyo Allah Kursum banda birgima babu abinda takeyi. Tana san kwacewa amma inaa hannunsa ɗaya yafi nata duka biyin. Bai sauke ta ba duk irin shure-shuren da takeyi sai cikin ɗakin shi ya shiga da ita, wanda bata sake jin tsoron Yazeed ba sai dataga wani tafkeken ɗaki da ko a mafarki bata taɓa tunanin akwai babban ɗaki mai girman haka ba. Innalillahi shikenan yanda ake labarin sai da mutum itama shi za’a mata dan wannan tabbas ɗan shan jini ne. Wasu kwalla ne taji sun fito mata, nan fa ta fara rokonshi akan ya taimaka ya maida ita gida. Cikin toilet ya shiga da ita ya maida toilet ɗin ya rufe da karfi. Ganin haka yasa gabanta ya fara dukan uku uku shikenan yau ita da duniya kuma sunyi sallama, gashi bata cimma burinta ko ɗaya. Hannayenta ta haɗe da sauri ta fara rokarsa bakin ta yana rawa, “Ya Nafi’u dan Allah ka yafe min nayi kuskuran auranka wallahi, Ni wallahi Allah ban sani ba dan Allah kar ka yankani, in kuma zaka yankani ka maida Umma dan Allah karka haɗa min da ita…..” Kuka ne ya kwace mata ganin yazo daf da ita yasa ta fara kiran. “Wayyo Allah nashiga uku Ya Kabir! Ya Kabir!!…….” Nan da nan wani mugun kishi ya turnike Yazeed, matsowa yai cikin sauri yake sa hannayenta ya matsesu da karfi tare da turata jikin tiles ɗin dake bangon toilet ɗin yana jin wani abu na sake taso mai. Ita kam Kursum tsoro ya gama firgitata jikinta banda karkarwa ba abinda yakeyi. Wannan ba Ya Nafi’un da ta sani bane. Bakinsa yaje kaiwa nata wanda hakan yasata saurin juyar da kanta gefe, har lokacin ko wani gaɓa ta jikinta rawa take saboda tsananin tsoro. Ganin yanda ta juya mai kai yasa ya sauke ajiyar zuciya. Nan da nan ta fara tunanin meke damunshi? Bayan ya ɗauka ya koyi hakuri akan ta? Shower ɗin dake jiki ya kai hannu ya zaro handle ɗin, ruwan dumi ya kuna ta runtse ido sam ɓata san a toilet take ba saboda addu’ar neman kariya ce kawai abinda takeyi. Ruwa kawai taji an sakar mata a jiki, wani irin numfashi taja ta sulale a ƙasa jikinta na wani irin rawa. Sai da yaga ta jike tas sannan yace “Sorry Sum-sum wallahi bansan zaki tsorata ba, kiyi hakuri bansan meke damuna ba.” Idanuwanta ta buɗe wanda sukai jaa hawaye na cikinsu fal bakinta na rawa tace “Ya Nafi’u na rokeka da Allah ka maida ni gidan da ka ɗakko mu…..” Kuka ne ya kwace mata, juyawa yai har yakai bakin ƙofa yace “Zan amso miki kayan sawa, sannan maganar gida ki sani har abada ke da gidan nan saboda ke matatace yanzu. Dan haka nan ne gidan ku na har abada.” Yana kaiwa nan ya fita ya barta a ciki. Itama fitowa tazo zatai dan ita toilet ɗin ma tsoro yake bata ta kasa tabbatar da cewa banɗaki ne. Ganin shatin half vest ɗin dake jikinta duk ya fito yasa ta shiga dube-dube Har ta hango towel ɗin dake toilet ɗin ta ɗauka ta fito har lokacin kuka take wiwi. Turus ta tsaya a ɗakin idanuwanta ta zaro tana jin faɗuwar gabanta na karuwa kai kace za’a ciro zuciyarta waje. Me take gani haka? Hotonta ne kafe a saitin dake kallan gadansa tana sanye da nikaf a fuskarta, ba sai ta tambaya ba hoton da sukai ne randa tai musabaqa. Baya tai saboda yanda jikinta yake cigaba da rawa bata san sanda ta faɗi ƙasa ba saboda tsananin tsoro. Hannayenta sam sun kasa aiki saboda tsananin tsoron daya bayyana a fuskarta. Sam kwakwalwarta ta kasa auna mata abinda ke faruwa. Gefen gadan ta kalla ganin wani hoton nata tai tsaye tana murmushi, yanzu kam hoton ta ɗaga nikaf ɗin fuskarta ta bayyana sai dai duk a ranar ne. Jikinta gaba ɗaya rawa yakeyi yanda kasan an kwara mata kankara a cikin jikinta a lokacin sanyi. Labulen ɗakin aka yaye, ganinta haka yasa ya taho da sauri, sai dai yanda ta fara jan jiki tana guje mai ne yasa shi tsayawa cak, sam ya manta da hoton a ɗakin sai da yaga tana bin hoton da kallo tsoronsa bayyane kiri-kiri a idanta.

Kayan ya ajiye akan gado yace “Ki sa kaya kiyi sallah muje ki gaida Magajiya itace mahaifiyar Dadyn mu.” Ko motsi ta kasa sai rawar jiki da take. Yai murmushi yana kallan hoton yace “Shi yasa nasan ke rabona ce kuma halal ɗina ce, babu wanda ya isa ya aureki kaf duniya dan a kanki zan iya mika mutum lahira, ke ɗin jinin jikina ce, daga randa na ɗau ra idona akanki. Uhmm abin mamaki sai gaki a gidan da naje dan zargin su sukai kidnapping ɗina. Bari kiji saboda ke na zauna dan ban taɓa tunanin zan ganki ba, shi yasa ke kaɗai nake kulawa kuma kece kikasa na zauna tsawon lokacin nan da nayi tare daku. Wallahi akanki My Sum-sum zan iya rabuwa da kowa. Da komai. Ki shirya yin rayuwa dani domin bana jin duk duniya akwai wanda ya isa ya raba mu bayan Allah.”

Ni kai na Ayusher jinai jikina ya fara rawa, yaushe ya santa? Sanda tai saukar ya haɗu da ita kenan? A’a a tv ya ganta? Gaba ɗaya fa kaina ya kule da wannan abin. Shin mutanen gidan zasu barta dashi? Cakwakiya tana gaba fa, ku hanzarta siya kundai san labarin nan zai bada ma’ana❤️❤️

Ayusher Ce🏌🏻‍♀️

Katin waya MTN ta 07065283730

Sai shaidar biya ta. 07065283730 or +44 7894 142004

Ayusher Ce🏌🏻‍♀️

700 ne Kacal 🤌🏻
7065283730
Opay
khadija Abdullahi shehu.

Katin waya MTN ta 07065283730

Shaidar biya ta 07065283730 or +447894142004

Ayusher Ce🏌🏻‍♀️
Chapter 27 · 0% Book details