Sashe 8
Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
Duk tafiyar da sukeyi Kabir banda kunkuni da zabgawa saurayin harara ba abinda yakeyi, kusa da saurayin nan Kabiru ya kuma matsawa, a tsorace saurayin ya tsaya cak. Sai da Kabiru ya kalli inda Baba yake yaga yana kokarin tare musu napep, ya juya yace da saurayin nan "Kai natacce ko? Duk inda zamu sai ka bimu, Allah zanyi maganinka dan baka isa ka dinga shiga rayuwar Babana ba ɓarawo kawai, zaka yi bayanin yadda kai ka baro gidan ku." Alhaji Nuhu ya kallesu yace suzo su shiga napep ɗin. Kabiru ya shige yana cije lebe, saurayin ya shiga suka sashi tsakiya "Dalla malam kana matse ni ko kai zaka biya kuɗin?" Ya faɗa tare da bangaje kafaɗar saurayin. Ko kallanshi baiyi ba, ran Alhaji Nuhu Danbatta ne ya baci yace "Kasan Allah Kabiru ranka zai ɓac," yai maganar yanamai wani kallo. Suna tafiya Kabir cike da takaici yana gyara zama yace "Wai Baba ko suna bazamu sa mai ba? Ni fa na gaji da mai magana kamar wani kurma." Ka kirashi Muhammadu ai dai daga yau ne zuwa gobe kila." Baki ya taɓe ya kalleshi daga sama har kasa, ya kalli takalmin slippers ɗinsa daya bashi wanda shine ya ɓata kwalliyar dayai yace " Wallahi a'a Baba wannan katan mara gaskiya zamu ƙira shi da haka? Kawai mu ƙira shi da Kasimu ko Garzali."Kafadar saurayin Baba ya dafa kafin yace "Bama san muna tafiya ba tare da munsan abinda zamu ƙira ka dashi ba, zan ƙira ka da sunaye se ka zabi ɗaya." Bai jira amsar sa ba yace "Muhammad? Khalid?" Ganin sun iso Ƴan Kaba yasa suka sauka daga napep din. Da sauri Kabiru yace " Kai Nafi'u wuce muje." Alhaji Nuhu Danbatta murmushi yai ganin saurayin yabi bayanshi sam neman maganar Kabir baya karewa, wanda bai sanshi ba bazai taɓa ɗauka yanada saukin kai ba, dan inya samu wanda ya raina tofa akwai matsala, kafin su shiga mota suka sai ruwa da awara suka shiga mota lokacin anata ƙiran sallar magriba. Suna shiga cikin mota ruwan dake hannunsa kawai yasha ya fara bacci, sun yi sa'a motar bata dade ba suka cika aka ɗau hanya. Kabiru ya kalli Baba cikin maganar raɗa saboda mutane yace "Nidai inata faɗa maka wallahi yaran nan sam banyadda dashi ba, kana ganin yanda yake abubuwa zaka tabbatar wani shahararen mugu ne, nifa ko wannan mantuwar da yace yayi ban yarda ba karya yakeyi." Alhaji Nuhu Danbatta idansa na kanshi yace "To naji ace karya yakeyi menene ribarsa? kuɗi ne da mu da zai sata? ko kuwa me?" Kabir ya kalleshi yanata bacci abinsa yace "Baba bakasan yanda duniya ta canza bane yanzu ba gaskiya sam ba abinda bazai yi karya dan ya samu ba in ba haka ba menene zaisa yaiwa Kursum magana ita kadai?" Wani sanyayen murmushi yai dama yana mamakin ya akai yanzu yafi takurawa yaran akan sanda suna asibti, yace "In kasan kishi kake sai ka shirya kuyi aure mana ni haryanzu banga me kake kunya ba." Da sauri ya gyara zamansa yace "Nifa Baba ko a kafa ka ɗau ra min Kursum sai na yadda ita na gudu dan babu abinda zaisa na aureta gwara na shiga duniya." Kai kawai ya girgiza ya ɗan fara matsa hannunshi yana tunani, wato ita Inna tayi yaji sam bata da shirin dawowa ko? wai ita a dole an ɓata mata rai. Shiru yai yana tunani menene mafita ? Dan kuwa gidan nan bazai yiwu ba in ba Inna dan yasan wahalaa kawai za'ai ta ba Kursum a kuma hanata karatunta. Da ɗin bacci ne ya debi saurayin ya kwantar da kansa kan kafadar Baba, cike da takaici Kabiru ya maido da kanshi kan kafadarsa yana cewa "Duk anzo an yiwa Babana tsaye, gaskiya Baba ka dena janyo mana mutane." KB yai magana yana maida fuskarsa titi. "To ubana." Alhaji Nuhu ya faɗa yana shafa kan saurayin cikin tausayi. Sun isa Danbatta suka sauka daga cikin mota, Kabir suna sauka yaga abokinsa da sauri ya kwalla mai ƙira "Lawan !" Dawowa yai ya kalli Alhaji Nuhu yace "Baba ka hau ya kaika zan nemi wani ya kawomu." Kallansa yai cike da zargi kafin yace "Zan wuce nida Nafi'u kai sai ka ƙaraso." Yana nan tsaye Lawan ya ɗauke su a mashin nan suka gangara kauyensu. Suna shiga ciki ba kowa a waje sallamarsa kawai Umma taji tarugu da gudu tana "Baba oyoyo!" Har ta ƙaraso yana kallanta cike da tausayi mace babba amma in tana abu kamar ƴar shekara biyar. Rungumeshi taje yi yai saurin cewa " Ramlah me na faɗa miki?" Ja tai ta tsaya sai kuma ta kalli saurayin tace "Yakubu ya akai ka zama babba?" Alhaji Nuhu Danbatta ya kalleshi kafin yace "Sunanshi Nafi'u." Kai ta jinina alamun to kafin tace "Nafi'u angon Nafisa zakai wasa dani?" Kallanta yai kafin ya kalli Baba wanda yai murmushi yace "Ya gaji gashi baiyi sallah ba ki bari sai gobe kinji?" Baki ta turo ta juya ciki kamar zatai kuka, kallanshi yai yace "Nafi'u ka samu kai sallah kafin Kabir ya dawo." Ya ƙarasa maganar yana nunamai bandakinsu na tsakar gida, kallan toilet din yai nan Baba yai ciki shikuma ya nufi toilet din. Yana ƙoƙarin shiga ya juyo karatun Qur'anin dake tashi daga bayan ɗakin, tsayawa yai cak yana saurare, wata nutsuwa ce take ratsashi tun daga tafin kafafunsa zuwa tsakiyar kansa, a hankali ya fara bi zuwa inda karatun ke fitowa, jikin kofar ɗakin Kursum yaja ya tsaya hannu yasa kamar zai ɗaga labulen sai kuma ya fasa, komawa yai ya jingina da ɗakin yana cigaba da ji, idanunsa a lumshe wani sanyi da daɗi na ratsa ilahirin jikinsa, yafi minti biyar a gun kafin yaji motsi alamun za'a fito da sauri ya juya har kafafunsa na hardewa ya nufi toilet ɗin da aka nuna mai, shiga yai ya kalli toilet ɗin tas sai dai ya kasa tantance a ina yake, baiga inda za'ai fitsari ba bare ruwan da zaiyi amfani dashi, abinda ya fara tambayar kansa shine wanene kai? Ya akai bakasan komai ba? Kallan sama yai kawai ya hango tsaka, uban kara ya dana ya fito a guje yana zabga ihu irin ihun nan da ba'a tsayawa. Mutanen gidan a guje suka fito har su Adda Yagana, Baba dake sallah ma sallamewa yai ya fito dan ihun da ake alamu ne na babban abu. Gaba ɗaya tsayawa sukai a bakin toilet ganin yana nuna musu ciki, kalla sukai sudai basuga komai ba, Raheena cike da takaici tace "Badai saboda tsakar can kake mana ihu ba? Kana katan saurayi bazaka kashe ta ba ga tsintsiya nan?" Nafi'u ya kalli Baba cike da tsoro, Kursum kallansa tai mamaki ya kamata tace "Sai dai kai amfani da bandakin ɗakin Baba dan wannan ba'a rasasu da tsaka ko kadangare." A hankali yace "To." Da sauri Baba ya kalleshi yace "Nafi'u ashe kana magana? Dan me ba ka yi to?" Shiru yai mamaki ya sake kamashi ya tabbatar ba kunnensa bane ya jiyemai, kenan Kabir gaskiya ya faɗa. Da mamaki ya kara cewa "Nafi'u komai lafiya?" Ajiyar zuciya yai kamar mai neman jawo numfashi kafin yace "Eh!" Jin haka yasa Alhaji Nuhu Danbatta sakin murmushi wanda har sai da hakoransa suka bayyana yace "Taho muje ɗakina kai acan." Adda Yagana tana tsaye har sukai ciki taja wani dogon tsaki tace "Shi kenan wani marayan ya ƙara samun gidan zama kuma da alama wannan ɗan rainin hankaline ma wato mu ko kallo bamu isheshi ba." Ƙwafa tai ta juya tana cewa "Gida sai kace gidan marayu shikenan kai da gidan ubanka sai ka zama dan kallo." Sai da sukai sallah sannan Baba ya kalli Nafi'u yace "Nafi'u zaka iya tuna sunan ka da garin da kazo?" Shiru yai alamun tunani kafin ya ɗau ra haununsa a saman kansa ya rike kamar yana san tuno wani abu, wani azababen ciwon kai ne ya saukar mai da sauri ya runtse ido ya fara bubuga kansa da karfi, hanunsa na hagu Aljai Nuhu Danbattta ya saka da sauri ya rike hannunsa yace "Ya isa haka nan, komai a yishi a hankali, ka jira kaci abinci sai ka kwanta dan banaji tun jiya kaci wani abu." Kwallawa Hasina ƙira yai bayan ya fita tsakar gida, sai gata tazo da sauri yace "Me kuka dafa? Bakon nan yunwa yakeji." Shiru tai kafin tace "Ɗazu Kursum tayi tuwo sai dai shi za'a kawo mai." Kallanta yai cike da takaici kafin yace "Wato Kursum tayi tuwo ke kina kawarta kuma yar uwarta amma sam bakisan me ya dace ba, tunda Yagana ta samu matsala agidanta ta dawo nan nake kallan take-takenki, kema burin bin sahunsu kike?" Da sauri tace "A'a Baba ko da safe da ba ka nan Umma tai mafarki nine naje gun ta wallahi ba haka bane." Jin maganar mafarki yasa yanayin fuskarsa ya canza zuwa damuwa a hankali yace "Yau ɗin?" Ta ɗaga kai alamun eh sannan tace "Wuyanta ta rike kamar zata kashe kanta." Hankalin Baba ba ƙaramin taashi yai ba ya kalleta yace "Sako tuwon ki ƙira min Kursum." Juyawa tai batai ko minti biyar ba sai ga Kursum tana tafe Umma na binta a baya riƙe da hijabin jikinta. tsugunawa tai Baba ya zauna akan tabarma yace "Kursum meyasa baki sanar dani Ramlatu abin ta ya tashi yau ba?" Kanta na ƙasa tace "Baba kai da ba lafiya ba sannan yau ana ganinka ansan da abinda ke damunka shiyasa, kuma naga itama tun daga nan ba abinda ya biyo baya." Tausayin Umma ne ya kamashi kafin ya kalli Kursum yace "Ta faɗa miki mafarkin menene?" Kai ta girgiza alamun a'a kafin tace "Kawai dai wuyanta ta shake wanda da yazo da karar kwana killa shikenan da ta wuce..." ta ƙarasa maganar cikin rawar murya. Shiru yai zaiyi magana tace "Baba shine nakeso ma na rokeka dan Allah makarantar nan tawa a hakura da ita nikam kula da Umma yafimin karatu." Tausayinta ne ya kamashi sai dai bazai iya bari ta ajiye karatu ba, tana bukatar ta kula da mahaifiyarta, in shi ajalinsa yazo wanene zai taimaka musu? Wannan dalilin yasa yakesan Kabir ya aureta a kalla yasan bazasu wulakanta ba. Sannan...." Katse zuciyarsa yai daga tunanin abinda takesan yi yace "Ajin karshe kike jarabawa ce kawai ta rage miki kina ganin zubar da karatun nan bai zama asara ba?" Ta girgiza kai cikin sanyin murya tace "Bai zama ba Baba a hankali in Allah yayi zan koma sai na koma, kuma yanzu ko na gama karatun ba dama ma na cigaba saboda Umma kuma banaso Inna ta sake fishi saboda barinta." Shiru yai shidai tausayin yarinyar nan na damunshi, bai san me zaice ba yanzu hakan yasa yace "Tashi kije Allah ya miki albarka, amma ko a gida ne zaki iya katatu kiyi jarabawar kk." Miƙewa tai bayan tace Ameen, Hasina ce ta ƙaraso ɗauke da tiren abinci ta shiga ta ajiye Nafi'u na zaune ya sa hannunsa saman goshinsa alamun tunani itadai ta ajiye tana binshi da kallo, bai kalleta ba har tabar ɗakin, Baba ne ya shigo jikinsa duk ya gama yin sanyi, ganin Nafi'u a kishingide ya zauna daga gefe yace "Ka tashi kaci abinci." Zama yai sai dai yana buɗe tuwon yaji zuciyarshi na tashi, da sauri ya maida murfin samirar ya kule ya kalli Baba ya girgiza kai a hankali, mamaki ne ɗauke a fuskar Alhaji Nuhu yace "Ko madara za'a siyo a hadama tea?" Jin kalmar tea yasa yace "Eh Baba." Nan ya dau waya ya kira Kabiru yace ya taho da madara da bread yana fada ya kashe wayar dan bai san shirman Kabiru da mitarsa wacce bata karewa. Can sai ga Kabiru ya dawo, Baba da kanshi ya kira Raheena yace ta kuna risho a dafa ruwan zafi, nan aka dafa yasa aka hadamai tea, Kabiru takaici da mamaki sam ya hanash mamaki, bai sake shan mamaki ba sai dayaga yaran nan ya juye madarar sachet din da aka siyo duka a kofi daya, baki ya bude yace "Kai bakada hankaline, wannan madarar da ita dukan mu zamu iya shan shayi shine...." Ka tashi ka fita ko sai ranka ya baci?" Baba yai maganar cike da bacin rai, haka ya tashi ya fita ransa a matukar bace. Yana gama shan shayin yai isha'i sai bacci, dakyar Baba ya iya tashinsa sallar asuba yanayi kuwa ya koma bacci, har ya shirya ya fita gun gyarar motarsa bai tashi ba. Karfe sha biyu ya farka jikinsa fduk ba karfi ga wata yunwa data tasomai, bandaki yaje yanasan wanka amma babu ruwa, fitowa yai dan yasan ya ake wanka a gidan, a zaune yaga Kursum tana rubutu, Umma kumatana kwance a gefenta tana wasa da robar ruwan hannunta, kallan takardun dake gaban Kursum yai wanda ta maida hankali sosai tana san sanin yanda akai, dan jiya bayan maganar da sukai da Baba da ta kwanta tayi tunani dole tai karatu da kanta tunda WAEC ne inyaso in an fara exams sai taje tai exams din. Ajiyar zuciya tai ganin ta kasa gane abinda tambayar take nufi gashi dama makarantar kauye ba wani karatun arziki ake koya musu ba. Rufe littafin tai ta ajiye a gefe, hannu yakai ya dauka, wanda hakan yasa tabi hannun da kallo zuwa fuskarsa, budewa yai shafin dayaga tana dubawa, ya dade yana kallon littafin ita kuma da take zaune tana kallanshi kafin yace duka a ciki biyu kikai daidai, spellings din ma ba daidai bane sannan amsarma ba daidai bane." Kallan mamaki tamai tace "Ka iya karatu?" Tambayar ya maimaitawa kansa kafin ya mika mata littafin, sai taga yana neman komawa ciki, da sauri tace "Kayi makaranta ne?" Kai ya girgiza alamun rashin sani yace "Ban san ko nayi ba amma kawai jikina yaban ba daidai bane, sannan yanda kika rubuta physiology ba haka bane p-h-s-i-o-g-y ne."