Sashe 10
Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallansa tai tace "Ni a matsayin me ka ɗauke ni?" Bai kalleta ba har lokacin idanshi nakan titi, murmushin ya ke tai tace "Babu yanda za'ai ace ni baka duba matsalata dana yarana sai na Kursum, Yagana ko karatu ai baka barta tayi ba, kayi hakuri amma wallahi bazan iya ba, ka aurar da ita inyaso mijinta ya sama mata mai aiki ta karasa a can, da bata isa aure ba amma yanzu ta isa ai." Ajiyar zuciya yai dan sam baisan me zaice ba a zancan, ta sani sarai zancen bai mai da ɗi ba sai dai ba yanda ta iya itama ta daina bari a cuceta ah to. Haka suka dinga tafiya motar ba wanda yake wa wani magana har suka isa garin Danbatta.
Nafi'u ne a zaune a jikin bangon dakin Kursum yayi shiru yana sauraran karatun Qur'anin da takeyi, kira'ar da takeyi tana ratsa duk wata gaɓa dake jikinsa, Raheena ce ta fito daga ɗaki ɗauke da bokiti, mamaki ne ya kamata ta saki bokitin ƙasa cike da masifa tace "Uban me kake anan?" Mikewa Nafi'u yai ya shafa sumar kansa baiyi magana ba sai ɗakin Kursum daya nuna. Wata harara ta galla mai tace "Kai kwarto ne hala?"
Bai fahimceta ba sai kallanta kawai da yakeyi, Umma ce ta fito ɗauke da robar ruwan wasanta, ganin Nafi'u yasa ta ƙarasa gunsa ta harari Raheena tace "Raheena in kika dakeshi sai na fadawa Kursum."
Hannunta ta dunkule saboda takaici juyawa tai ciki tana balbalin masifa yau ta tabbatar yaran nan kwarto ne haka kawai yazo ya tsaya a wajen ɗakin su salan su fito ba kaya ya kallesu.
Umma kuwa hannun Nafi'u ta kama tana ƙoƙarin shiga dashi cikin ɗakin da sauri ya kwace hannunsa ya koma ɗakin Kabiru da gudu dan tabbas yasan Kabiru ya ganshi kila yau har dukansa zaiyi. Umma ta biyoshi tana tambayarsa "Wasan ojiyo ji zamuyi?" A hankali ya girgiza kai alamar a'a kafin yace "Yunwa," yai maganar yana taba cikinsa, da gudu ta ruga tana kwallawa Kursum ƙira, jin yanda Umma ke ƙiran ta yasa ta rufe qura'nin ta fito, a kusa da ɗakin su ta ganta, ta riƙeta tana cewa "Umma sai kin faɗi ko?" Tsalle ta fara tana cewa " Nafi'u yunwa yakeji." Kallan gefen su tai inda yake tsaye jikin bango, a hankali ta fara takowa, idanunsa ya sauke kan kafafunta wanda duk taku daya da takeyi ya samu kansa da kallansa har ta karaso inda yake. A hankali cikin sanyin maganarta tace "Baka ci abinci ba?" Bai amsa ba sai dai kansa da ya daga alamar eh, ajiyar zuciya tai kafin tace"Ka zauna bari na duba kitchen ɗin." Tai maganar tana shiga kitchen, ya akai dumamen da aka aika musu da Kabiru ya cinye shi kadai? Kai Ya KB akwai neman magana. ruwan zafi ta ɗau ra ta dama ragowar gasarar da suke dashi ta dauko bread ta fito. Anan inda ta barshi yake, nan ta ajiyemai ya kai hannu ya amsa ya hankali ya fara ci yana binta da kallo a hankali, mikewa tai zata wuce cikin sauri ya riko rigarta ta baya. Mamaki ne ya kamata ta waiga fuskarta ɗauke da mamaki tace "Me kakeyi hakan?" Bakinshi na dan in in na yace "Ban faɗa miki amsar dazu ba." Idanunta na kanshi sai dai ta zare rigarta daga hannunshi tace "Kayi makaranta ne?" Kai ya girgiza kafin yace "Bansani ba amma na san amsoshin duka." Murmushi tai a hankali kafin tace "In ka gama cin abincin zanzo sai ka koyamin." Murmushi ne ya bayyana a fuskarsa dan har sai da hakoransa suka fito ya jinjina kai da sauri yace "Umm Hmm" Har zata koma ciki suka ji sallamar Baba da sauri suka dawo cike da murna, Umma kuwa tuni ta hau tsalle tana "Baba oyoyo ya siyomana biskit" Inna ce ta ƙaraso ciki wanda hakan yasa Umma in shiru ta koma gefen Kursum, wani kallo ta mata tace "Na ɗauka kinji faɗan dana miki na hanaki tsalle?" Da sauri Kursum ta ƙarasa ta amshi kayan hannunta, kallan saurayin dake zaune yana kallansu yana cin abinci tai, bashi da alamar tashi bare ya mata magana. Yana daga zaune ganin kallan da takemai yasa ya maida kallanshi gun Baba wanda ya mai murmushi yave "Nafi'u ku gaisa matata tace uwar yarana." Kai ya ɗaga alamar to ya maida kansa ƙasa ya cigaba da cin abinci. Da mamaki Inna ta kalli Baba kamar zatai magana sai ta fasa, ɗaki tai shima yabi bayanta tana shiga tace "Wannan katan saurayin zaka ajiye cikin gidan mu? Munada yan mata a ciki? Alhaji wai ce maka akai haryanzu duniyar nan irin ta da ce?" Zama yai bakin gado yace "To ina kikeso na kaishi? Na faɗa miki yanda mukai da ɗan sandan kinga dole mu sake jiransu." Hannayenta ta hade tace "Nifa ban yarda da ɗan sanda dan bama tunda nake bantaba ji yaro ya ɓata an hana cigiyarsa ba, ka ƙira shi kace kai dai zaka kai gidan radio dan ni wannan abin gaskiya ban yadda dashi ba." Kallanta yai sai dai shi kanshi bai yadda da abinda ke faruwa ba shima, haka kawai yakejin akwai wani abu da ba daidai ba." Anan gabanta ya ɗau waya ya ƙira shi, sai data katse ya sake kira, bayan ya dauka bai jira me zaice ba yace " Alhaji Nuhu kaine?" Baba yace "Eh!" Da sauri yace "To Alhamdulila akwai mutanen da suka kiramu akan iyayen Nafi'u ne, insha Allahu gobe zasuzo, ba sai ka zo Kano ba mu da kan mu zamuzo Fagwalawa dake Danbatta, ka jiramu." Baba na shirin magana suka katse wayar, kallan Inna yai zuciyarsa cike da tunani. Ya akai suka san sunan kauyensa? Yasan yace musu Danbatta amma baice Fagwalawa ba to ya akai ya sani?
7065283730
Opay
khadija Abdullahi shehu.
Katin waya MTN ta 07065283730
Shaidar biya ta 07065283730 or +447894142004
Bonanza ki biya 500 daga yau zuwa 12th ga wannan watan kunsani ni da ku 5&6🥰
Ayusher Ce🏌🏻♀️
*RIBAR ƘAFA*
NA
Wattpad :-AyusherMohd
Arewabook:- Ayushermuhd
ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀️
Paid Book
*LAST DAY TO PAY 500 daga gobe 700*
Shafi na Bakwai
Da mamaki take kallan yanayinsa kafin tace "Me yace?" Yace gobe zai zo da alama sun samu iyayen yaran." Kai ta jinjina cike da jin dadi kafin tace "Haba har hankalina ya kwanta dama ya za'ai yaro babba kamar wannan ace iyayensa basu maida hankali ba, sai dai in ko dama gidn basu da tarbiyya." Alhaji Nuhu zai sanar da ita maganar Fagwalawa sukaji sallamar su Anty Yagana, Inna ta amsa sallama nan suka shiga zuciyarsu tas sai dariya suke, Baba guri ya basu ya fito daga dakin, har a lokacin Nafi'u na zaune yana sham koko kamar wani kashi, dan in ya kurbi daya sai yafi minti uku kafin ya kara shan wani. Murmushi yai yace "In ka koshi ka tashi mana." Shiru yai bai tashi ba kuma baie komai ba, Umma dake zaune gefen shi tace "Tsoro yake kar Kursum tamai fada." Dariya Baba yai ya kalleshi yace "Wai haka? Kai fa ba yaro bane kar ka bari Ramlah ta sa ma shirme a ranka." Kursum ce ta fito ɗauke da littafi, ga mamakin Alhaji Nuhu gani yai ta ƙaraso inda suke ta mikawa Nafi'u tace "Duba ka gani nayi daidai?" Amsa yai sannan ya fara dubawa, Baba yai murmushi yace "Malam Nafi'u da alamun dai jininka ya hadu dana Kursum, komai a kanta kake nuna mana ka taɓa yi, kayi karatu ne?" Kai ya girgiza kafin yace "Baba ban sani ba na dai san amsoshin."
Yana kallan yanda yake duba takardun ya jinjina kai alamun gamsuwa yace "Da alamun kayi, Allah ya baka lafiya." Ya faɗa yana tunanin gwara ya bari iyayensa suzo gobe su ganshi kafin ya sanar musu. Saman goshinsa ya shafa yana kokarin komawa ciki yaji ance "Wato duk faɗan dana maka akan kula Kursum bakaji ba ko?" Kursum dake tsaye daf daidai Nafi'u tai saurin cewa "Ya KB nikam meke damunka wai?"
Cike da tsawa Alhaji Nuhu yace "Ka kuskura ka ƙara magana sai na mare ka." Cak ya tsaya dan sam bai kula da Baba ba, hannunsa ya dunkule yana wani haki kamar kumurci shifa sam yaran nan bai yadda dashi ba, kallan Baba yai yanasan magana sai dai ya rasa ma me zaice, idan Baba na kanshi yace "Ka zo ka gaida Innar ka ta dawo ba shirman banza ba." Jin Inna ta dawo yasa yai ciki da sauri yana "Inna! Inna ta!" Itama tanajin muryarshi ta tashi da sauri sauri tana tafi tana "Lale da ɗan lele na lale lale!" Hannayenta ya riƙe yana shiga yace "Inna! Yaushe kika dawo?"
Kallan Alhaji Nuhu Danbatta tai dake tsaye jikin ƙofa tace "Ɗazu yaje ya ɗauko ni kasan bazai iya rayuwa a gidan nan babu ni ba."
"Ke da in aka barki a gidan ɗanki sai kije kiyi ta zama?" Baba yai maganar yana kallanta, Kabiru yai dariya yace "Inna karki damu ni in nai aure ma ɗaukeki zanyi indai Baba ya ɓata miki rai, waya kawai zakiyi zan taho da sauri na kinkimeki."
"Tunda katifa ce kaga kinkimarta ai duk sanda ka shirya sai kai," yanzun ma Baba ya jefa magana yana sakar musu labulen yabar gun. Dariya suka sa nan ya zauna a ƙasa tana kan gado ya fara bata labarin abubuwan da suka fari da bata nan, kallansa kawai takeyi dan gaba ɗaya labaranas akan wahalar da su Yagana ke ba Kursum ne, da yanda bata zuwa makaranta. Fuskarta nan da nan ta canza, ganin haka yasa yace "Inna kina jina?" Murmushin yake tai tace "KB in cigaba da yadda da maganar ka na bakasan Kursum? Ka dai san na fada maka sai dai in ka kai gawata sannan. "
Fuska ya tamke sosai tare da sakin hannunta yace "Inna dan Allah kubar maganar nan, ni wallahi yanzu ba hirar dana tsana irinta, shiyasa nake san abokina Lawan ya aureta ko na samu kyaleni da maganar ta haba."
Murmushi ta saki sosai tace "A'a ai kawai tambaya ne, kai kasan ba abinda na tsana irin wannan zancen nima." Jin haka yasa suka cigaba da hirarsu.