Sashe 18
Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau tun safe ta tashi ta share gidan ko ina, ɗakin su Inna ma ta gyara sosai ta buɗe ya sha iska. Wajen azahar suka dawo Alhaji Nuhu Danbatta kallo daya in kamai bazaka so ka sake ba dan gaba daya ya canza sosai, yayi wani irin rama wanda in har kasanshi sai ya tsorataka. Kwanciya kawai yakeyi yana bacci yana tashi, an sa mai catherter wanda zai dinga taimakamai gun jawo fitsari, sunce zasu barshi zuwa sati daya sai wani yazo daga asibiti a cire mai kar a ja mai infection. Shinkafa da wake tai ta yanka salad dan ragowar waken kenan na gidan, sai da sukaci abinci sukai sallah Inna a gaban Alhaji Nuhu Danbatta tasa aka kira Kursum. Tunda taji kiran gabanta ke faduwa dan kuwa ta riga da tasan kwanan zancen. Ɗauke take da tea din Alhaji Nuhu wanda take tunanin ko shi ya samu yasha saboda yunwa. A gefe ta ajiye ta tsiyaya ta matso inda yake tana kokarin tallafa mai, Inna ta kalleta tace "Ina uwar taki?" Bakinta na dan rawa tace "Sun fita da Ya Kabiru dazu ne kaina ke ciwo shine yaje ya siyo min magani. Wani mugun kallo ta zabga mata tace "Kabir din ubanki ne da zaki dinga aikensa? Ke ko tausayinsa bakya yi? Bayan kina kallo yanzun nan ya dawo daga asibiti?" Kanta na kasa tana kokarin maida kwallarta tace "Yi haƙuri Inna amma ba ni na faɗa mai ba wallahi Umma ce tace masa kaina na ciwo." Kallan Alhaji Nuhu Inna tai wanda banda girgiza mata kai ba abinda yake yi. Yawun bakinsa ya hadiya cikin maganarsa da ta koma mai sanyi da in-i'na yace "Sameera dan Allah....." Kasa magana yai saboda numfashinsa da yake hawa yana sauka. A fusace Inna tace "Tashi ki bar min daki kafin ki jamai wani abun." Kafafunta na rawa haka ta mike ta fita, hawayenta ta shiga gogewa sai jitai ance "Me ya sameki?" Muryar Kabir ce da sauri ta juya kafin ta waigo dauke da murmushin yake tace "Ya Kabir ka dawo?" Karasowa yai cike da mamaki yake binta da kallo yana sake cewa "Me ya sameki?" Yai maganar da tsawa. Inna dake cikin daki ce ta fito tace "Nice ko da wani abin?" Fuskarsa a tamke yace "Inna meke damunki wai? Dame kikeso yarinyar nan taji?" Mamakin kalamansa ne yasa ta zuba mai ido, tabbas inhar ta bari yarinyar nan ta cigaba da zama a gidanta to tabbas Kabir auranta zaiyi. Gwara tun kafin Baba ya warke dole ta aurar da yarinyar nan. Gyara tsayuwarta tai kafin tace "Tunda kazo to ka tsaya dama akwai sakon da zan baka, yaran dake san Kursum ka sanar dashi ya fito karshen satin nan a ɗau ra musu aure, in yaso sanda ya shirya sai ta tare." Da sauri ya kalleta yace "Inna? Aure? A wani dalilin za'a aurar da ita a haka? Kiyi hakuri amma tabbas bazai yiwu ba, yarinyar nan ƙanwata ce kuma indai ina da rai bazan bari a cuceta ba."
Hannu Inna ta ɗaga kamar zata zabga mai mari dan har Kursum ta tsugunna da sauri ta toshe kunenta, tsayawa Inna tai tana mai wani mugun kallo kafin tace "Nadai fada maka in kuma har baka sanar dashi ba, Malam Badaru dake santa na islamiyarsu zan bata, na gama magana." Tana kai nan ta koma ciki, tana kallan yanda Alhaji Nuhu ke san yi mata magana amma ta dauke kai. Tabbas dole ta cire duk wani imani dake kanta har sai taga an aurar da Kursum dan kuwa tabbas tasan Kabir na santa ganewa ne har yanzu bai yi ba. Kuma yanzu ta sake tabbatar da hakan ita kuwa sai dai in bayan mutuwarta amma bazata taba bari ya auri Kusum ba ya kare rayuwarsa yana kula da mahaifiyarta. Gaba daya Kabir kasa magana yai, Kursum da gudu ta mike tai ciki, jiki a sanyaye ya fara kokarin binta daga can gefe yaji ance "In kasan ba santa kake ba ka kyaleta." Waigowa yai ya kalli Nafi'u dake jikin soron gidan, kafin yai magana ya juya yabar gun. Kursum kam tunda ta shiga daki Umma ta bita bata fito ba sai magriba tai wanke-wanke ta gyara gidan. Tana ji sanda abokin Kabir ya shigo gidan gun Inna da alama sawa tai a nemo mata shi. Tana daga nan kwance tana ji Yagana na dariya tana cewa "Damafa bakusan halin Inna bane ai in kunaso kuga rashin imaninta a taɓa mata Kabiru, bare kuma tasawa ranta zatai masa auran gata, yanzu taga auren da zai ɗebo mata, tab!"
_Nima bansan sanda nace "Tab! to shi Kabir din ba'a aure aka haifeshi?"_
700 ne Kacal 🤌🏻
7065283730
Opay
khadija Abdullahi shehu.
Katin waya MTN ta 07065283730
Shaidar biya ta 07065283730 or +447894142004
Ayusher Ce🤸🏻♂️
*RIBAR ƘAFA*
NA
*Wattpad :-AyusherMohd*
*Arewabook:- Ayushermuhd*
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀️*
Paid Book
Shafi na Goma sha Ɗaya
Duk yanda Kursum taso ta ɗauke kai akan abinda ke faruwa kasawa tai, ta sani sarai abokin Kabir wato Ahmad bawai yana santa bane tsakani da Allah, da kanshi yasha sanar mata yanasan mace mai hakuri ne saboda yana da zafin zuciya zai iya yiwa mace duka azo ana magana. Amma in mai hakuri ce yasan tabbas ba shi da matsala tunda ko me ya mata zata haƙura. Abinda ke kara ɗaga mata hankali yanda kusan ko da yaushe zai ce ya daki wane, ko ya daki wance, hatta Yayunsa mata da kanensa sai da sukai aure ya kyale su. Abu na biyu gashi da san taɓa mutum, shi yasa ko tsayawa kusa dashi bata san yi. Ta riga tasawa ranta inhar shi ɗin ne mijinta bakomai ya aure ta koma menene ya mata a ƙalla yafi Malam Badaru wanda malami ne a makarantar Alhaji Nuhu. Sai dai malintar sai lokaci lokaci yakeyi, shi matanshi uku gashi gidanshi kullum matsala ce a ciki, shi kanshi matan da yake dasu ma bai iya rike su ba bare ya ƙara da ita. Ga kuma nauyin Umma, a gidanshi iya kaci ya aura ya tara 'ya'ya ya ajiye musu buhun gero ya tafi ci rani wanda ba kudi ko kayan abinci yake turowa ba. Tasan irin wannan idan ta aureshi bata san yanda zatai ba ga Umma, ga kula da gida ga kuma matsalar kishiyoyi da yaran miji. Kanta kawai ta kwantar a bayan Umma dake ta sharar bacci hawaye ne kawai takeji suna zubo mata. Daga waje taji ance. "Kin kwanta?" Mikewa tai tazo jikin ƙofa tasa hannu zata buɗe yace "Karki fito." Hannunta dake jiki ta bari ba tare da ta murɗa ƙofar ba. A hankali tace "Yanzu zan kwanta." Jingina bayansa yai ta jikin ƙofar ya ɗan kwantar da kansa kaɗan yace "In kinsan bakyasan auren meyasa bazaki faɗa ba? Karatu kike ga exams a gabanki why zakiyi abinda bakyaso?" Murmushin datai ne yasa hawaye suka ƙara gangarowa saman kuncinta tace "Suna da ikon bani duk wanda sukeso a sanda sukai ra'ayi, na sani bazasu cuceni ba."
Shiru ne ya ratsa gun na wasu dakiku kafin yace "Amma babu alamun kina farin ciki da auran, in haka ne meyasa? Ko Kabir kikeso?" Kai ta girgiza da sauri tace "A'a wlh Ya Kabir a matsayin Yayana na ɗauke shi, ni kam babu soyayyar kowa a raina, wannan dalilin ne yasa nasan ko wa aka bani zan iya aura in kuma zauna dashi." Baki ya taɓe kamar zaiyi magana sai kuma taji shiru. A hankali tace "Ya Nafi'u!" Jin shiru yasa tasa hannu ta murɗa ƙofar ɗakin. Ga mamakin ta yana nan tsaye a gefe tana buɗe wa idanunsu ya haɗu da na juna, da sauri tai ƙasa da kai tace "Kayi hakuri in nayi laifi, amma duk abinda Inna tace shine zabina." Kai kawai ya ɗaga mata ya fara tafiya cikin sanyin murya tace "Nagode da kulawar ka." Bai tsaya ba bare tasa ran zai amsa mata. Har sai da ya wuce sannan ta juya ta koma ciki. Inna kam tun safe ta fita wai zataje gidan Mai Unguwa ta sanar dasu za'a zo tambayar auran Kursum tunda dai abokin Alhaji Nuhu ne itama ta haka suka shaku da uwar gidansa suna aminta sosai. To dama can shine madaurin auran balle kuma yanzu da Alhaji Nuhu Danbatta bashi da lafiya shi zai wakilceshi da yin komai. Rahina ce ta shiga kaiwa Baba ruwan sha cikin alamun jin jiki ya kalleta cikin maganarsa wanda yakeyi da kyar yace "Rahina ki ƙira min Kabir." Da sauri ta tashi ta shiga ta ƙira shi. Nafi'u na kwance aka kirashi yanaji har ya fita, haka kawai yake jin zuciyarsa na zafi ya rasa dalili. Kabir bayan ya shiga sai da ya taimakawa Baba yasha ruwa sannan ya kama hannunsa, cike da tausayin mahaifin nasa wanda har yanzu bai yadda shine ya rikiɗe rana ɗaya ya koma haka ba.
Rungumeshi yai yana maida kwallar dake zubo mai. Alhaji Nuhu cikin dauriya yace "Kabir ka taimaka ka auri Kursum, wannan ne kaɗai zai sa na mutu hankali kwance. Na sani kai zaka kula da mahaifiyarka da kanenka ita ce....." Kasa cigaba yai saboda yanda numfashinsa ya fara sama da kasa. Kallan Baba yai duk yanda yake san ya danne zuciyarsa kasawa yai sai da hawaye suka kwace mai. Ya jinjina kai yace "In dai haka ne zan aureta, sai dai ka taimaka ka cire duk wannan a ranka ka dawo Baban dana sani. Baban da muke wasa da dariya. Baban da zai fita da kafafunsa ya dawo." Alhaji Nuhu Danbatta idanunsa ne suka sake canzawa yana kallan Kabir wanda duk ya fara canzawa, yaro mai kazar-kazar da zolaya yanzu duk babu a tatttare dashi. Kallan ƙofa yai kafin yace "Nafi'u fa? Har yanzu DPO bai ne me mu ba? Ina tsoron….” Hannunsa Kabir ya riƙe cikin wani yanayi yace "Baba kanka, ka kula da kanka, kaji da kanka mu samu Allah ya baka sauki. Matsalolina ko na wasu duk ba shine kan gaba ba." Kwantar da kansa yai a jikin pillow, ya zai yi in yaran nan ya girma a haka ba tare da yasan wanene shi ba? Haka Kabir ya zauna a wajan shi yana tausasa masa zuciya akan ya kwantar da hankalinsa komai zai zo da sauki.