← Book details Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 27

Sashe 15

Ribar Kafa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Inna ce zaune ita da Baba a ɗaki, sunyi shiru cike da damuwa yace "Ni bansan meke faruwa ba gaba ɗaya." Sake ƙiran DPO yai ga mamakinsa sai jiyai ance "Hello?" Da sauri ya mike zaune yace "Yalabai inata nemanka." Ajiyar zuciya yai yace "Muna cikin tashin hankali ne, gawar tasu ce muka kai aka birne." Mikewa tsaye yai yace "Aka kaisu Nafi'u baizo yaga gawar iyayensa ba? In sune iyayensa fa?" Iskar bakinsa ya furzar cike da damuwa yace "A dole muka kai dan yanayinsu ne ba kyan gani, sai dai inada tabbacin sune suka haifeshi." Ido Alhaji Nuhu ya runtse ido zuciyarsa na zafi, DPO ne ya katse shi da cewa "Babar matsalar ba yan ƙasar nan bane, daga Niger suka zo nan suke zaune, dole sai ya dawo hayyacinsa sannan zamu san yanda zamuyi a nemi yan uwansa, shine muke roko inda hali ya cigaba da zama gunka kafin nan, akwai kudi a asusun mu zan sanar da ogan mu inda taimakon da zamu iya muku, yaran nan karka manta ta dalilinka ya rasa rayuwarsa dan wannan babu maraba da rasa rayuwarsa, sannan ya rasa iyayensa. Bana ji zaka iya hana shi zama a gunka indai akwai tausayin da mutane ke cewa kana dashi." Kasa magana Alhaji Shehu yai gaba ɗaya abinda ke faruwa jinshi yake yana zuwa mai sama ta ka. Muyar DPO ne ya katseshi "Number da yaranka ya bada naga yana whatsapp da ita zan turama hotunanusa yana yaro wanda muka samu daga gun iyayensa, dan Allah kai hakuri da neman mu kafin muji wani abu daga dangin sa da kuma gidansu dake nan ƙasar wanda muka sa cigiya." Muryar Alhaji Nuhu Danbatta na rawa yace "To!" Dan sam ya rassa abinda zaice gaba ɗaya. Komawa yai kan kujera ya zauna dabass zuciyarsa cike da tunanin da bashi da amsar su. Tabbas akwai abinda ba daidai ba a cikin abinda ke faruwa, sannan ya akai yasan yanada tausayin daya faɗa? Sannan taya zasu birne mutane ba tare da anyi binciken su waye ba? Inna ce ta katse mai tunani da cewa "Ka kwantar da hankalinka Alhaji, zaman katan saurayi a gidan nan kafin su gama binciken su bazai gagaremu ba, kawai dai Allah ya jikansu shi kuma ya dawo mai da tunaninsa." Jin kalaman Inna yasa ya dan ji sanyi a ransa sai dai yanada tambayoyi dayawa wanda bashida damar yinsu.

700 ne Kacal 🤌🏻
7065283730
Opay
khadija Abdullahi shehu.

Katin waya MTN ta 07065283730

Shaidar biya ta 07065283730 or +447894142004

Ayusher Ce🏌🏻‍♀️
RIBAR ƘAFA

NA

Wattpad:- AyusherMohd

Arewabook:- Ayushermuhd

ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀️

Paid Book

Shafi na Tara

Washegari da safe ya tashi daidai sanda yasan Kursum zata fita makaranta. Kayan jiya ya kara sawa na Kabiru wanda ke kwance yana shirgar bacci. Yana fitowa ita kuma tana kokarin fita daga tsakar gidan ita da Rahina. Saukowa yai da sauri wanda jin motsin tafiya yasa ta kalli inda motsin yake, a hankali ta sauke idanu kanshi. Wani sanyayan murmushi ne ya kwace mata wanda ita kanta bata san dashi ba. Saukowa yai shima fuskarsa a sake, Rahina tabi inda take kallo da kallo kafin tace "Nidai nayi gaba." Kai ta daga mata har ya karasa saukowa. Kusa da ita yazo yace "Tafiya zakiyi?" Kai ta daga a hankali, idanshi na kanta yace "Jiya bakice komai ba da kikaga nasa kayan nan." Kallan kayan tai cike da kunyar yanda yai magana ta kauda kanta, itakam batasan me zatace mai ba. Gaba yai yace "Muje na rakaki a hanya kya fadamin." Kasa mai musu tai sai bayanshi data bi suka fara tafiya. Sun ɗan yi tafiyar taku goma ya dan kalleta yace "Baki fada ba." Murmushi tai tana wasa da kasan hijab din jikinta tace "Kayi kyau." Sumar kansa ya shafa yana wani murmushi mai tattare da alamomi daban-daban. Tafiya suka cigaba dayi itama duk kunya ta isheta. A hankali yace "Umma bacci take?" Kai ta daga alamar eh, haka kawai takejin nauyin yin magana sosai dashi. Hannu yasa cikin aljihunsa yace "Itama batada lafiya ne?" A hankali ta dan kalleshi tare da jan birki. Murmushin yake tai tace "Eh." Ta karasa tana cigaba da tafiya. Haka suka cigaba da tafiya basu sake wata maganar ba. Ganin sun kusa isa yasa taja ta tsaya tana kallan daliban dake zuwa tace "Ka koma daga nan banaso mutane suyi tunanin wani abu." Kallan mamaki ya mata kafin yace "Wani abu?" Kai ta girgiza da sauri kafin tace "Ka koma gida." Bai musa ba ya daga mata hannu alamun bye-bye sannan ya juya. Da ido ta bishi da kallo tare da sakin murmushi sannan ta juya ta karasa cikin makarantar. Nafi'u kuwa yana isa gida ya tadda Alhaji Nuhu Danbatta a waje tare da wasu yara guda uku suna karatun Al-qur'ani. Wucewa ciki yaje zai yi yaji ance "Nafi'u!" Dawowa yai ya nuna mai kusa da daya saurayin alamun ya zauna. Zama yai sai da suka gama karatun su sannan ya kalleshi bayan sun tafi yace "Zaka iya tuna a ina kake a karatun islamiyya?" Kai ya girgiza kafin yace "A'a na dai san wasu." Ajiyar zuciya yai ya dauko qur'ani ya fara gwadashi sai dai sam bai iya ba izu dayan kasa kawai ya iya shima ba duka surorin ba. Shiru ya ɗan yi alamun nazari kafin yace "Ina ganin ka dinga fitowa muna karatu kullum, a kalla ko tunaninka ya dawo ka tuna kayi baifi muraja'a ba." Kai ya daga alamun to, ya kama hannunshi cike da tausayinsa ya ɗan bubuga kafin ya sakeshi, gaba ɗaya jiran Kabiru yake ya zo ya nuna mai hoton da aka ce an tura. Iskar bakinsa ya ɗan firzar kafin yace "Ka shiga ka amso mana abinci sai muci mu fara ko?" Mikewa yai ya shiga ciki ya karɓo musu. Anan sukaci abinci kafin Alhaji Nuhu Danbatta ya fara ɗora mai karatun, yayi mamaki sosai dan kuwa yana da saurin ɗauka. Haka ya barshi yai ta biyawa yanayi yana mai gyaran tajjuwiddi wanda da alama bashida su. Alhaji Nuhu Danbatta da Nafi'u na nan a zaune Kabir ya fito. Yana zuwa yace "Baba kaga abinda aka turo." Amsar wayar yai yana bin hotunan da kallo, da farko hotunan yaro ne dan shekara daya. A hankali Kabir na wuce mai sai gashi ankai shekara takwas wanda kallo ɗaya zaka mai kasan Nafi'u ne. Can sai gashi tsaye kusa da iyayensa sun sashi a tsakiya. Ido Alhaji Nuhu Danbatta ya runtse dan kuwa ko bai sake tambaya ba iyayen Nafi'u ne dan kuwa gasunan tare dashi. Nunawa Nafi'u yai ganin hoton yasa ya kalleshi yace "Nine ko?" Kai ya ɗaga alamun eh kafin yace "Zaka iya tuna waɗannan? Ka duba da kyau." Amsa yai yana ƙoƙarin tuno wani abu. Kabir dake tsaye ya taɓe baki yace "Mai kwakwalwar kifi ai zaiyi wuya ya iya tabuka abin arziki." Yanda Nafi'u ya sunkuya tare da matse kansa ne yasa shi yin shiru. Kansa ya ji ya sara mai kamar wanda aka buga da guduma irin mai tsinin nan. Rike gefe yai da sauri ya ɗan saki wata karamar ƙara tare da sake matse kansa. Da sauri Kabir ya amshi wayar ya riƙe shi yana cewa, "Kai Nafi'u ya isa haka nan." Kansa ne ya ke cigaba da sa ra mai wanda hakan yasa Alhaji Nuhu Danbatta ya yiwa Kabir magana akan ya kama shi ya shiga ciki dashi ya kwantar. Har suka shiga ciki idansa na kansu cike da tausayin abinda ke faruwa. Wani tunani ne yazo mai, in har sun samo hutunansu kila zasu samu sunanshi. Wayar DPO ya ƙira sai dai yaji wayar a kashe jiki a sanyaye ya ajiye tunda yasan suna da abubuwa a gabansu bazai sa ran suyi mai duk abinda ya tambaya ba. Jikinsa ne duk ya sake yin sanyi ta ina zai iya sanar da yaron nan iyayensa sun mutu? Sam bazai iya ba dan kuwa yanzu shima ba lafiyace ta isheshi ba. Addu'a ya fara tare da fatan samun sauki.

Kabir ne ya fito bayan ya ajiye Nafi'u ya zauna kusa dashi yace "Baba nifa I am smelling something suspicious, gaba ɗaya ban yadda da abinda ke faruwa ba. Anya mutanen nan sune? Shi kanshi DPO din fa akwai big question mark a kanshi. Kaga wannan yaran da kake ɗauka a matsayin ɗan ka? Shine babban rat na wannan case ɗin." Wani mugun kallo da Alhaji Nuhu ya mai ne yasa shi shafar kanshi. Kai ya girgiza kafin yace "Ko da bangane me kace duka ba a dan karamin turancinka ai dai nasan rat to in ma babban barawo ne menene naka? Me zai sata a guna?" Shiru KB ɗin yai alamun nazari shi dai ya tabbatar barawo ne to amma me yazo sata? Ganin ba fuska ya tashi ya koma ciki yana sake yin tunani.
Chapter 15 · 0% Book details