← Book details Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 76

Sashe 8

Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Alhmdllh natashi jikina da sauk'i, Dan kuwa babu zazza6in da ciwon jikin, hakama ciwon kan babu, bai tadani ba saida yadawo massalaci, lokacin har gari yafara haske ma.
Na idar da salla ina zaune ina addu'a yafito daga bathroom, da alama wanka yayo, Dan sanye yake da bathrobe sky blue, yana rik'e da k'aramin towel a hannu yana goge ruwan fuskarsa.
Kallo d'aya namasa Na d'auke kaina, shikoma bai kalleni ba ya wuce gaban mirror ya zauna, saida yafara shafa mai sannan Na tsinkayo muryarsa yana fad'in “ya jikin naki?”.
Yanda yay maganar a cinkushe yasakani d'agowa Na kallesa, ganin hidimarsa kawai yakeyi saina d'auke kaina, nace “da sauk'i”.
Bai sake magana ba, harya kammala yabar gaban mirror d'in, wajen wardrobe yakoma, nidai kaina Na k'asa bansan hidimar dayakeba.
Koda ya d'auki kayan saiya koma bayi ya saka tamkar yanda ya saba, ya fito ya iskeni ina gyaran gadon, ta gefen ido Na kallesa, yayi k'yau cikin wani bak'in lallausan yadi, Wanda akaima ado da jan style, nakula yanason kayan al'adarsa, dukda baitashi ya girma cikin k'abilar tasaba, sock's ya d'akko da bak'ak'en takalma sau ciki ya zauna saman sofa, yana sakawa yana magana, “uhm Zanyi wata 'yar tafiya Na kwana 2 kacal, mikike da buk'ata?”.
Tsayawa nayi daga gyaran gadon danake, Na d'ago ina kallonsa kawai, jin nayi shiru kuma yanajin alamun ana kallonsa ya d'ago shima. Ido muka had'a saina janye nawa.
“kallon fa?”. ‘yafad'a yana k'ok'arin saka d'ayan takalmin’.
Cikin la6e baki nace “yoni yalla6ai mizan kalla anan?”.
Banza yamin, saida yagama saka takalminsa sannan yamik'e tsaye yana fad'in “hakanefa, Ashe babu abin kallo anan”.
Nima shiru namasa ban tankaba, ya saka laptop d'insa dawasu 'yan abubuwa a k'aramar briefcase d'insa, ya zuge zip d'in yana fad'in “ki shirya muje kiga likita kafin Na wuce”.
Da sauri nace “a'a kaje abinka, Indai nice Na warke”.
Idanu ya tsuramin alamun tuhuma, nikuma nak'i kallonsa, ya girgiza kansa kawai sannan ya ajiye min kud'i akan gadon, “ni Na tafi, a yafi juna”.
'Dagowa nayi ina kallonsa da mamakin kalmarsa ta k'arshe, bansan sanda bakina ya su6uce nace “ALLAH ya tsare hanya, ya dawo dakai la fi ya”. ‘na k'are maganar da d'aid'aya’.
Cak ya tsaya abakin k'ofar, saboda yanda addu'ar tawa tazo masa a bazata, dan bai tunanin hakan daga gareniba, yajuyo a hankali tamkar maison gaskata abinda yaji, kallona yayi muka had'a ido, amamakina saiya sakarmin wani tsadajjen murmushi, irin Wanda zan iya rantsuwa ban ta6a gani daga garesaba. Baice komaiba yajuya yafice da sauri.
Yabar zuciyata da luguden dabansan dalilinsa ba. Wata ajiyar zuciya Na sauke, tare da zama jagwaf a bakin gadon na dafe kaina da mamakin murmushin da Galadima yamin.

Bai dad'eba sosai a hospital yamusu sallama yafito, dama tun a daren jiya ya sanar musu zaiyi tafiya, ga jirgi kuma ya kusa tashi. yafito sunata binsa da addu'oin dawowa lafiya, yayinda shikuma yake amsawa cikeda murmushi. Saida yafara xuwa sukayi magana da doctors d'in dake kula da Abie, yaji babu wata Matsala sannan yafito.
Dama Khumar ne ya kawoshi, Dan haka yanzu ma shine yatafi kaisa airport d'in. Zaman da baifi 30minutes ba jirginsu yataso zuwa 9ja.
Zaune yake kusa da window, yayinda wata matashiyar budurwa ke gefensa, tunda tazo da nufin zama yawani kuma had'e fuska, a d'age ma ya amsa mata sallamar data masa, yasaka belt tareda bud'e Newspaper yahau karatu.
Budurwar sai satar kallonsa takeyi, tanason masa magana amma bataga fuska ba. Sai da akazo tambayar misuke buk'ata?, yace Coffee.
Itama da sauri tace Coffee d'in. juyowa yayi ya kalleta, ta sakar masa wani tsadajjen murmushi.
Janye idonsa yayi yanajan tsaki a zuciyarsa. duk yanda taso yamata magana ko sau d'ayane Galadima yak'i yayi, ya had'e gabas da yamma abinsa. Haka kawai sai tunanin tahowarsu da Munaya ya fad'o masa a rai, yatuna yanda tadinga wani dakewa irin itafa ta saba da hawan jirgi. jaridar yasaka ya rufe fuskarsa yana murmushi da jinjina jan aji irinnan yarinyar, ita bata yarda aga marenarta ba. ya tuna diramarsu ta daren jiya, wani murmushin yakuma saki...... haka abubuwa da yawa sukaita dawo masa akan Matar tasa ta auren Contract. wani abun nata abin dariya, wani Na mamaki, ita bata yardaba adole big girl Ce.
Koda suka sauka baiko kalli inda yarinyar nan takeba, da sauri tabi bayansa tana fad'in “haba yayana babu sallama? Ai kodan darajar makwaftaka mayi sallama”.
Yana sauka daga step d'in k'arshe Na jirgin ya juyo ya kalleta, aransa yace yarinya sai nacin jaraba. Ta kuma fad'in “kozaka bani Number ka muke zuminci”.
Yanzu kam wata uwar harara ya zuba mata kafin yay gaba abinsa. tsaye tayi tana binsa da kallo, jitake kamar ta tsala ihu, harma tafara tunanin ko shid'in kurmane?. cikin matuk'ar mamaki ta hango wasu masu kaya iri d'aya sunyo wajensa, daka gansu kaga jama'ar masarauta. da k'yar ta had'e yawun bakinta, kenan shid'in jinin sarautane?. Batada mai bata wannan amsar, Dan haka taci gaba dabin motocin Galadima da kallo har suka fice abinsu.
Driver d'in da yazo d'aukarta yak'araso inda take, gaisheta yafarayi kafin ya k'ar6i handbag d'in hannunta. amota take tambayarsa koya San wanene Wanda masu kaya iri d'aya sukazo d'auka?.
Yace, “ma'am Galadima Sameer kenan, d'an tsohon Sarki, kusan 1month kenan da aurensa ai”.
Hararsa tayi cikin daka tsawa tace “ina ruwana dawani aurensa, bashi Na tambayeka ba. Punishment d'inka Na fad'amin abinda ban tambayeka ba shine ka nemomin number sa”.
“ALLAH ya huci zuciyarki Ma'am”.
Banza tamasa, yayinda shikuma zufa keta karyo masa dukda AC n dake motar, tunaninsa a ina shikuma zai Samo number babban mutum irin Galadima Sameer shikam? yasan idan bai samo d'inba yashiga uku, dan yarinyar nan ba mutunci gareta ba.

*********************

Tun bayan tafiyar Galadima saina zama wata sukuku, abin mamaki saigani da kewar Galadima wai, gaba d'aya yinin sai nayishi wani babu dad'i, ga gabana yanata yawan fad'uwa, jinake kamar wani al'amari yana shirin faruwa da rayuwata.
Sauban ma sarkin tsokana kasa shiru yayi saida yay magana.
Bayan ya dawo school sai muka tafi asibiti, tunda Na gaida Abie da Momma da Aunty Mimi saina koma gefe nayi shiru abina, ciwon jikine kawai ke nuk'urk'usata, dan ga6o6ina masifar ciwo sukemin, narasa wannan dalili? zazza6inma banaji yanzun, ga yawan fad'uwar gaban dana yini inayi, sai kasa kunne nake naji ko Galadima zai kira wani a 'yan uwansa yace ya sauka lafiya, dan zuciyata tafi karkata da fargaba a kansa.
Shirun da Sauban yaga nayi shine ya kalleni yana dariya k'asa-k'asa. “Aunty gimbiyarmu har kin fara kewar Hubbin naki halan?”.
Idanu nad'an waro ina kallonsa, ganin su Momma Na dariya saina 6oye face d'ina cikin veil d'ina ina fad'in “kai yaa Sauban ALLAH a'a”.
Dariya suka kuma sanyamin, Abie nata murmushi shidai, Momma tace, “A'a Mrs Galadima kifad'a gaskiya dai?”.
Kunya takuma lullu6eni, saina k'udundune kaina gaba d'ayama a gyalen saboda. ina k'aunar wannan family sosai a raina, saboda nima suna nunamin tsantsar k'auna, ko yau nabar cikinsu auren contract d'inmu yak'are bazan manta da alkairinsuba a gareni.
Haka nagama shirin barci Na kwanta a gadonsa ina shak'ar k'amshin turarensa danakejin dad'insa fiye da da. nadad'e ina juye-juye banyi barciba saboda damuwace cinkushe da raina, ga zazza6i mai zafi ya rufeni, bansan ina Galadima yajeba balle nayi tunanin samun number na kirashi, Na gwada number shi ta nan India tak'i wucewa, dama a wayar Samha Na d'auki number bama ta saniba, yau babu mai kulawa dani, sainaji wata kewar innarmu da Munubiyata sun dawomin sabo fil a zuciya. Sai da dare yakusa rabawa kafin barci mai nauyi ya d'aukeni.

_____ .★. _____ .★. _____

Har yamma ba'abari kowa yaga Abba ba, 'yan gidanmu sunci kuka harsun gode ALLAH, Su Munubiya da dukkan yaran gidanmu Na ma'auri tuni labari ya iso musu, kuma duk sun tattara a asibitin suma.
Doctor d'in dayake kan Abbanmu ne yafito yana basu hak'uri akan suje gida hakanan, dan gaskiya baza'a bari suga Abba ba a yau.
Sabon kukane yatashi, musamman ga innaro, idan ka kalleta dolene tabaka tausayi wlhy, yau babu jarabarnan da rashin mutunci, kuka take da fad'in Auwalu karya tafi ya barta..........
Sambatunta yakuma raunana zukatan mutane da yawa a wajen.
Munubiya tayi yunk'urin kirana amma network yahana, da Yaa marwan yakula da hakan kuma ya hanata, yace karta sake ta sanarmin yanzu. Wannan dalilin yahana a sanar min d'in.
Kowa zuciya babu dad'i suka tattara suka tattafi gida, dady da baba k'arami, yaa hameed yaa shafi'u da ya Naseer aka bari a asibitin zasu kwana.
Ranar duk Wanda yasan gidanmu yasan babu lafiya, Dan gidan yayi tsitt, kowa tashi ta isheshi a zuciya, barcima k'alilanne daga cikinsu suka yisa.

___________________________
Chapter 8 · 0% Book details