← Book details Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 76

Sashe 65

Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su mai Martaban suna tare da Galadima, sunyi farin cikin tashinsa, hakama yaran. sunkuma yima Abdurraheem addu'ar tashi shima. Sun d'an jima a d'akin, dan har saida aka shigo dasu Dady da baba k'arami, Yaa marwan, Yaa Hameed suma suka gaidashi da masa jajen ALLAH ya kiyaye gaba sannan suka fita gaba d'aya.
Daga nan manyan irinsu mama Fulani, inno matana Sarki da sauran su duk suka shigo suma, harda su innaro da akaita kuka.
Galadima dai Kansa kawai yake iya d'agawa, idonsa a lumshe. Baya buk'atar kallon kowa a cikinsu.
Su inno duk tausayinsa ya kamasu.
Innaro aka share hawaye tace, “barka da arzik'i kaji, ALLAH ya kiyaye gaba, ya shiga tsakanin nagari da mugu, ya tona asirin duk makirin dake cikin wannan satar yara”.
Duk da amin suka amsa. Galadima ma yace amin akan la66ansa. sai tunani yake ina Munaya take?, dan hankalinsa yafara tashi da rashin gilmawarta, musamman daya tuna a halin daya tafi itama ya barta.
Yadai kasa daurewa ya bud'e baki da k'yar yace, “Mom ina Munaya wai?”.
Saida mom ta matso da kunnenta sannan tajishi, tasan yana lafiya ma ya aka k'are da k'asaitar magana balle yanzun. Murmushi tayi, tace, “tana d'aki, itama sai yanzu ta farka, dan dole aka sake mata allurar barci bayan tafiyarka, waccan bata dad'eba ta saketa”.
Tausayin Munaya ya kuma kamashi, ya jinjina kai yana yunk'urawa zaune sosai. Cikin yamutse fuska yace, “Mom nima yakamata nayi wanka Na rama sallolin dake kaina”.
Mom tace, “to bara a kira su Muftahu su kamaka ”.
Kansa ya girgiza mata da mata alamar, zai iya da kansa.
Mom tace, “Alhmdllh”. Rigarsa ya jawo yasaka, dan da dagashi sai best. d'aukar Abdurrahman da Amaturrahman yayi ya fito, yabar mom tana gadin Abduraheem dabai farko ba. babu kowa a falonsa Dan duk sun fice.
Da k'afa ya turo k'ofar, Munaya Na zaune a bakin gadon rik'e da mansa zata shafa amma dukta kasa, burinta taga halinda Galadima da yaranta suke ciki kawaine damuwarta, gashi har yanzu babu Wanda yazo yakirata akan su papi sun fita. bud'e k'ofar ya sakani d'ago ido. Zummbur na mik'e tsaye ganin Galadima rungume da yaran, ai yau nama manta dawata kunyar towel na d'aura, hawaye suka shiga zarya tsakanin idona da kumatu, Galadima ya tako a hankali zuwa gareni idonsa a kaina. Da sauri namatso garesa nima, nahad'ashi shi da yaran na rungume ina sakin kuka mai k'aramin sauti.
Shiru yay kawai ya zubama gashinta ido yana tausaya mata daga ita har yaran, ansakasu a yak'in dabasu San mafariba, ya godema ALLAH da yarannan sunada sauran numfashi a duniya. Da baisan yanda zaiyi da munaya ba. Ganin kukan nata zaiyi yawa ya bud'e baki da k'yar yace, “ya isa mana”.
d'ago idanu nayi na kallesa, cikin muryarta data dishe saboda kuka nace, “Nagode yalla6ai, dasun mutu nima mutuwa zanyi”.
Murmushin gefen baki yayi, cikin d'age gira d'aya yace, “dama ana sonmu haka?”.
Sai yanzu kunya ta kamani, nai k'asa dakai ina kallon k'afafunmu.
Bai sake cewa komaiba ya ra6a ta gefena yaje ya shimfid'e yaran akan gado.
bathroom ya nufa yana cire rigar jikinsa, nidai Na k'arasa gadon Na rungume yaran ina sumbatarsu, wani dad'i da tsantsar farin ciki Na ratsani, Na d'aukesu Na fara shayar dasu ko zasu rage nauyin da sukamin, aikam kamar jira sukeyi suka kama sha. Hannun rigar namijin Na d'aga saboda tanan muke gane shaidarsu, ganin Abdurrahman ne saina fara tunanin ina Abdurraheem shikuma?, hankalina yaso tashi amma saina daure ina jiran Galadima ya fito naji daga garesa.
Galadima dake kallonta bata saniba ya d'an cije lips, ya tabbatar yanzu tana son yaransa, amma baisan miyasa take ignoring d'insu ba idan yana waje? Kokuwa tsabar jan ajinne oho?.
Har Lokacin daya fito wankan tana shayar dasu, ta shafa kan wannan ta shafa Na wannan, sosai suka birgeshi itada yaran, jin kamar motsi yasakani kallon wajen, da sauri na janye yaran daga bakin nono naja towel d'in na rufe abinna ina turo baki gaba.
Baki ya ta6e yashiga takowa inda muke, ya rankwafo kaina ruwan fuskarsa yana d'iso min a jikina, a kasalance yace, “wane darene jemage bai ganiba malama, tunkan su sha ni........”.
Da sauri na saka hannu na toshe masa baki.
Zama yayi yana janye hannunna, cikin waro idanu yace, “to mikike tunanin zan fad'a? lallai kinfi k'arfina, niba can Na dosaba to”.
Sosai naji kunya, na sauke yaran a kan gadon na sakko, zuciyata cikeda mamakin sa, ya d'aure fuska yana basarwa yayta sakin magana kuma kamar bashi yayiba.
Ficewata nayi bayan na d'auki bathrobe d'insa na d'ora akan towel d'in jikinna.
Wani kallo ya bita dashi yana ta6e baki, kafin ya maida ga yaransa daketa kalle-kalle, ya shafa kumatunsu sannan ya mik'e zuciyarsa na tunanin su Momma, addu'arsa d'aya kar wani ya sanar musu.

Kasa fitar nayi saboda jin kamar da mutane a falon da zanbi ya sadani da 6angarena.
Badan nasoba tilas Na dawo baya.
Galadima dake gaban mirror yana shafa mai yana kallonta ta ciki, amma sai yayi biris tamkar bai gantan ba.
Komawa nayi na zauna a bakin gado ina tunanin mafitar yanda zan samu kaya, da jin haushin sharenin da yayi.
Ana haka mukaji knocking, saida ya kalli Computer d'in yaga Mom Ce d'auke da Abduraheem sannan ya mik'e yana amsawa..
Zuwa yay ya bud'e mata, bata shigoba ta mik'a masa yaron da har anmasa wanka Ashe, ta mik'a masa kaya a leda tace na Munaya ne.
Galadima yace, “mom ya tashine?”.
“ya tashi, tunma fitowarka babu dad'ewa, harma an masa wanka”.
Sumbatar kumatun yaron yay yanama mom sannu

Idonsa akan yaron yana kuma sumbatar goshinsa cikin lumshe idanu ya k'araso inda nake dana zuba musu idanu cikeda sha'awa.
Kusa dani ya zauna ya d'ora minshi akan cinya. nima rungume kayana nayi na sumbaci goshinsa, inason bashi abinci amma inajin kunyar Galadima, gashi ya zubamin ido yak'i tashi.
Lura da hakan dayay ya sakashi yin miskilin murmushi ya mik'e yabar wajen.
d'an hararan bayansa nayi ina fad'in mugunta dai babu k'yau a kan la66ana..................✍🏻

“Hummm fans nasan kwace wai ina Harun ne?🤔, kumuje zuwa dai danjin ina ya shige haka? Ita kuma sarauniya Zulfah (uwar gidan Sarki mike matsalarta)?.😨😏

*_Ya Rabbi ka gafarta ma iyayenmu_*😭👏🏻
[7/17, 6:21 PM] Aysha Galadima: *_typing📲_*

💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*

*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

~Book 2~ 👉🏻2⃣8⃣

............A yanda Na kula har yanzu bayajin dad'in jikinsa, dan komai a d'an wahalce yakeyinsa, koda ya fiddo kayan daga wardrobe saiya dawo bakin gadon ya zauna ya dafe Kansa, kallonsa nayi cikin damuwa nima, Na cire Abdurraheem Na kwantar, sannan Na mik'e zuwa garesa, durk'usawa nayi Na d'ora hannayena akan gwiwarsa, “yalla6ai lafiya?”.
Shiru yamin kusan minti 1, harna fidda ran samun amsa ma na yunk'ura na mik'e da nufin barin masa d'akinma duka.
Hannuna ya rik'o, na juyo na kallesa, har yanzu yana yanda yake baiko d'ago motsa ba.
Na cije lips ina had'iye kukan dakeson zubomin, rayuwar nan tasa bana sonta wlhy, ni y'ar dangi Ce, nariga natashi gidan yawa, dukda gidanmu bahagon gidane mukanyi hira koyayane, amma shifa magana ma idan bai ra'ayiba wahala take masa, Abu na damunsa a rai amma bazai iya fiddashi yaji sauk'iba, Momma ta had'ani da aiki, a watannin baya kad'an kamar yafara canjawa, amma gashi yakuma birkicewa yanzu, tayaya Momma take tunanin zan iya canja Galadima? murd'ad'd'en mutumne shi mai wahalar sha'ani, ga tsantsar mulki da k'asaita da suka zama jinin jikinsa, s.........
Tunanina ya katse lokacin danaji an jawoni, nai firgigit saboda fad'awa danayi jikinsa, shikuma yay baya ya fad'a kan gadon, kad'an ya rage mu danne Amaturrahman, yad'an kauce kad'an yana sauke ajiyar zuciya.
Uffan bai ceminba ya maida idonsa ya lumshe.
Mamakin wannan lamari ya kamani, hannu yasaka ya kwantar da kaina a k'irjinsa yana d'an buga bayana da d'ayan hannun, zanyi magana ya d'ora yatsunsa hannunsa uku na tsakkiya akan bakin alamar nayi shiru. banida za6in daya wuce yin shirun, nabisa yanda yakeso.

Yanayin da zuciyarsa ke bugawa sai yabani tsoro, na saka hannuna na danne wajen sannan na d'ora kaina bisa hannun, ajiyar zuciya yayi yana cizar lips..
Tsawon mintuna 3 muna a haka, har knocking d'in k'ofa akayi amma baiko motsaba bai barni na motsaba, na yunk'ura zan tashi ya maidani.
Munkai mintuna 7 sannan ya zameni ya kwantar ya mik'e zaune, batareda ya kalleni ba ya sauka daga gadon, bathroom ya Shiga, babu dad'ewa ya fito, nidai kallonsa kawai nake da mamaki, Dan fuskarnan amatuk'ar d'aure take tamkar baisan minene dariyaba a rayuwarsa, ya shinfid'a abin salla, domin rama sallolin da suka riskesa yana barci.
6oyayyar ajiyar zuciya na sauke, na tashi zaune idona akan yaran, duk sun koma barci, na tsurama Abdurraheem ido, saboda fitar numfashinsa ta banbanta dana y'an uwansa, tunani nai ko yanayin nasa barcin kenan shikuma, saboda wahalar da suka sha,
d'aukar ledar kayan da mom ta kawo nayi, na fiddasu na saka, ban jira ya idarba na fice abina.
Nayi mamakin da yanzu babu kowa, harsu Munubiya sun tafi, haushi ya kamani kamar zanyi kuka, aidai sa jira na fito mu gaisa ko? hawayen da suka zubomin a kumatu na share, namafi jin haushin Munubiya wlhy.
Sallamar da akeyi na amsa da k'yar, sannan na bada izinin shigowa, cikin bayina ne guda biyu, zubewa k'asa sukayi suna gaisheni.
Cikin girmamawa d'aya tace, “dama ance mu gani idan kin fitone”.
Nace, “Hummm”.

Fahinmatar iya amsar dazan iya basu kenan ya sakasu mik'ewa suka fita, zamewa nai na kwanta cikin kujerar ina cigaba da zirar da hawaye.
Kusan mintuna 5 saiga Samha ta shigo, ta durk'usa gaban kujera tana sharemin hawayena, d'ago ido nayi na kalleta, namata murmushin k'arfin hali ina tashi zaune.
Muryarta da alamun tasha kuka itama tace, “Aunty Uncle Sam na kiranki”.
Kai na jinjina mata kawai, na tashi gaba d'aya na d'auki mayafi muka tafi tare.
Koda mukaje k'ofar falon bata Shigaba, nikad'ai na Shiga ita kuma ta juya ta fice daga sashen gaba d'aya.
Chapter 65 · 0% Book details