← Book details Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 76

Sashe 74

Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tafiya tafara nisan da naji yana neman sakin layi, a kasalance na rik'e hannunsa dake yawo a jikina, sannan na fara k'ok'arin janye fuskata daya koma bama kisses tako ina, sai gwama numfaahi yake yana sakin tagwayen ajiyar zuciya. ganin bazai bariba nasakar masa siririn kuka, ina fad'in, “yalla6ai jegofa m....mu...mukeyi”.
Sai a lokacinne ya tsaya cak, amma yak'i d'agani, juyo da fuskata nayi na kallesa, ya sake sark'e idonsa da nawa, idanunsa sunkuma rinewa launin jaa sosai, wani murmushin takaici ya sakarmin, cikin magana da k'yar yace, “kina kukane danna mori sadakina?”..
Wannan magana tasa tamun nauyi, Dan haka na gagara bashi amsa, sai janye idona da nayi hawaye masu d'umi suka gangaro ta gefen kunnena.
Gefena ya koma ya kwanta yana cizar lips da lumshe ido, yayinda hannunsa ke shafa kaina saboda tuni d'an kwalin ya zame. A haka yafara magana a hankali, “toke yanzu Yaya kenan? naga alamar auren Contract yakusa k'arewa, gashi ko rabin sadakina ban Moraba, zaki dawomin da kayanane ko yaya?”.
Kai wannan Bawa ya shahara a fagen rainin wayo, nafad'a a zuciyata, a fili kuma sai nace, “nima sai'a biyani d'aukar ciki da nak'uda, da shayarwa ai, tunda babusu a yarjejeniyar auren”.
Yanda nayi maganar ina yamutse fusaka da murgud'a baki saiya shagala da kallon la66anta, hannu yasaka ya tallafo fuskarta yajuyo da ita sosai inda tashi take, dukda idonta a rufe suke, “kifad'i ko nawane sai a biyaki ai, nikuma ba kud'in Dana bayar nake buk'ata ba”.
Na bud'e ido baki bud'e, “to mi kake buk'ata? Naga kud'i ka bada kuma kud'i ya kamata a baka”.
Cikin ta6e baki yace, “farashina ya wuce haka”.
Nina bakin na ta6e nace, “Niba arhar banza bace”. Nayi maganar ina yunk'urawa da tashi zaune, da kallo ya bini, saida na ziro k'afafuna k'asa sannan nakuma fad'in “mun gama sahirinmu”.
Shiru yamin tamkar bazai tankaba, harma na juyo na kallesa, idonsa a rufe suke yayi filo da hannayensa, d'auke idona nayi ina gyara rigata.
Yace, “zuwa ina kenan?”.
Nace, “gidanmu”.
Tashi yay ya sauka daga gadon duka yana nufar wardrobe, saida ya bud'e yana kallon kayansa sannan yace, “mizai hana kibari ki k'arasa aikinki kawai saiki tafi gaba d'aya”.
Na murmusa ina mik'ewa tsaye nima, na koma jikin mirror na jingina ina hard'e hannayena a k'irji, idona akansa nace, “aini nagama aikina, Dan nabaka dukkan sirrin dake raina”.
Yana ciro wasu bak'ak'en wando da Riga yace, “zadai ki gamane yarinya, Abin cikin kwan bazasu gusa a kusa daniba”.
“Humm” nafad'a cikin takaici, nace, “mizai hana ka yanke dukkan alak'a, Dan nima iyayena na buk'atar ganina a kusa dasu”.
Murmushi yayi yana juyowa hannunsa d'auke da kayan daya za6o, kallo d'aya yamin ya janye ido, “mikikeci na baka na zuba babie, indai an gama yak'in ai zata yanke”.
“nikuma bana buk'atar ganin k'arshen, in ank'i cikin sauk'i zan bud'e komai kowa ya sani”.
Murmushi yay mai sauti, har fararen hak'oransa na bayyana, ya kwance igiyar rigar wankar babu kunya ko shakkar ganina, kauda idona nayi daga inda yake, yafara saka kayansa, cikeda izza yace, “wace k'arfin gwiwa gareki na samun wannan damar?”.
“Court, tabbas zan maka ka a Court, sai a kar6a min ai”.
“kinada abin dariya kwarai da gaske, a mutum dubbunai dasuka shaida na biya sadaki sannan na d'auka, mutum d'ayane yasan sirrin ba haka bane, bayan wannan hujjar kinada watane?”.
Dariya nayi irinta tsantsar rainin hankali, harya d'ago daga d'aura belt d'in da yakeyi ya kalleni sannan ya janye, zama nayi a stool mirror, na d'ora k'afa d'aya kan d'aya ina girgizawa, “yalla6ai kenan, a tunaninka zaka iya cin bulus ne?”.
Murmushi kawai yayi bai sake tankawa ba, Dan ya kula ciwon kai take Neman saka masa, ya zauna bakin gadon yana saka sock's da takalmi, yayinda Munaya taketa cika da batsewar sharetan da yayi. rigar jacket d'insa milk color ya d'ora bisa bak'ak'en kayan, komai nasa ya kasance bak'i, jacket d'ince kawai milk, ya matsa gaban mirror kusada ita yana gyara sajensa da fesa mayen turarensa. Saida ya gama dukkan uzirinsa kafin yazo gabana ya tsaya hannayesa duka zube a cikin aljihu.
Dan k'yau yayi k'yau kam, amma saina kauda kai gefe ina ta6e baki, irin bakayi d'innanba.
Shima bakin ya ta6e yana rankwafowa kaina har inajin hucin numfaahinsa, “karki damu mai yabawar tana nan tafe lokaci kusa, matar Sameer sarauniyarsa kinji yalla6iya”.
Cikin azama na mik'e, yay saurin ja da baya, Dan daya tsaya saina buga masa kaina wlhy.
Hanyar fita na nufa ina fad'in “idan kana buk'atar y'ay'anka zaka iya bina gidanmu ka kar6o abinka”.
Da kallo yabi bayanta kawai yana ta6e baki, akan la66ansa yace “iya tsiwa”.

Agogonsa ya d'auka bak'i ya d'aura, sannan yazuba wayoyinsa a aljihu tareda saka eyeglasses mai duhu a idonsa, ya 6oye tsananin jaa da sukayi, a falo ya iske tea a cup an had'a yanata turiri, zama yay yana lumshe idanu, yakan rasa Munaya wace irin macece ita? So salon nata akwai tsagwaron k'ayatarwa, Crossing k'afarsa yayi yana shan tea d'in a hankali, yasha kusan rabin cup ya ajiye yana mik'ewa da kallon agogonsa yanajan k'aramin tsaki.
sashen Munaya ya nufa, bayin daketa gyare-gyare suka zube suna gaidashi, hannu ya d'aga musu kawai batare da yace k'ala ba, cikin takunnan nasa na k'asaita da izza yake tafiya, bayinnan sai satar kallonsa suke, da sallama ciki-ciki ya shigo d'aki, Laraba tai saurin risinawa tana gaisheni, ya amsa batareda yako kalleta ba, ficewa tayi da hanzarinta, Samha ma ta gaidashi.
Zama yay a bakin gadon idonsa akan akwatina da Munaya ta had'a, ya janye ya maida kan yaran yana fad'in “ku shirya gobe zaku koma?”.
Cikin d'oki Samha tace, “Uncle Sam harda Aunty gimbiya?”..
Cire glasses d'insa yayi ya maka mata wani kallon daya saka hanjin cikinta mitsawa, yace “tare kuka zone?”.
Da k'yar ta had'iye yawu tana girgiza masa kai.
Da yatsa ya nuna mata k'ofar fita, jiki na rawa ta ajiye Amaturrahman tafice tana tuttura baki da share kwallan shagwa6a.
Ya lumahe ido yana jan tsaki, Munaya dai na zaune tana had'a wasu y'an kaya da suka rage a k'aramar bag, ko kallo basu isheta ba.
Rankwafawa yay duk ya sumbaci kumatun yaran, sannan ya kalleta fuska babu alamun yasan dariya yace, “wannan kayanfa?”.
Duk da na tsorata da yanayinsa, hakan bai hanani dakewa ba, cike da jan aji nace, “Na tafiya”.
Uffan baice daniba ya mik'e, kansa tsaye ya nufi k'ofa, nikuma nabisa da kallo harya fice.
Wasu hawaye danake rik'ewa tun lokacin dana baro d'akinsa suka samu damar zirarowa, hannu nasaka na sharesu ina zuge zip d'in bag d'in.

Waya na d'auka na kira Momma, na gaisheta cikeda ladabi, albishird'in cigaban jikin Abie da aka samu ta sanarmin, tsantsar farinciki ya sake kamani, nace insha ALLAH su Samha ma zasu taho da wasu magungunan. godiya tamin da sake sakamin albarka, ta tambayeni ya mukayi dashi?.
Na sanar mata yace baza'a jemai ko ina da yaraba.
Murmushi tayi mai sauti har ina jiyota. “karki damu d'iyata. Da Kansa ma zai kaiku”.
Na amsa mata da to kawai, Dan banga alamar Galadima zai tankwaru ta cikin sauk'iba akan tafiya wanka d'innan.

***********

Tunda ya fito hadimansa keta kwasar gaisuwa damasa Yaya jiki, hannu kawai yake iya d'aga musu fuskarsa babu walwala, sarkin mota da dogaran dakan bisa yayin fita suka taso da hanzarinsu, bud'e masa mota akayi ya shiga.
Saida Sarkin Mota ya tada motar sannan yace, “ranka ya dad'e ina muka nufa?”.
Banza ya masa kamar bazai tankaba, sai zuwa can yad'an nisa yana bud'e ido, “mu fara Shiga wajen mai martaba”.
“Angama ranka ya dad'e”. Sarkin mota ya fad'a cikeda girmamawa.
Bai fita a motarba, sarkin mota ne yafita domin nema masa iso, amma sai jakadiya tace, “ai takawa tunda safe suka fita shida su Masu da baraya.
Sarkin mota yazo ya sanarma Galadima, baice komaiba sai kansa daya jinjina kawai.
Chapter 74 · 0% Book details