← Book details Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 76

Sashe 21

Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na kai tsawon lokaci a bayin ina Gasa jikina, dan nasan idanma banyiba kaina nama mugunta, saida naji ko ina ya saki sannan nayi wankan tsarki ina hawaye, bansan yanda zan fassara wannan muguntar ta Galadima ba kuma, wannan karon kuma tsautsayin zaice kokuwa ba yin Kansa bane?.
Haka dai na kammala na d'aura towel d'ina, a zuciyata ina addu'ar ALLAH dai yasa ya fita, dan towel d'in guntune, bai gama rufe cinyoyina bama baki d'aya.
Da sand'a na fito, yauma inajin zafi kad'an-kad'an, amma ba kamar na ranar ba. ganin baya d'akin saina ida rufe k'ofar na tako cikin d'akin sosai.
Ina neman kaya a wardrobe ina share hawaye, indai rashin tsiwar dayake fad'ace na daina masa, dan bazan zauna ya illatani a banza ba, wannan k'addararren cikinma daya hanamin gangar jiki hutawa da ciwuka ya isheni, basai na cigaba da 6alloma kaina wata muguntar tasa ba.
wata 'yar riga mai d'an nauyi-nauyi na samo, na cirota dan sanyi nakeji, juyowar da zanyi saina gansa zaune bakin gado yana danna laptop, hannunsa d'aya rik'e da glass cup yana shan fresh milk hankali kwance.
Saida nad'anja baya, nakuma bud'e rigar ina kare jikina.
Duk abinda takeyi yana kallonta ta gefen ido, amma yawani share kamar baima San da itaba.
Da bin bango da sand'a na koma bayin, ta gaba kuma ina karewa da rigar.
Saida ta shige ya d'ago kai yana kallon k'ofar bayin, saikuma ya girgiza kai yana murmushin gefen baki. cigaba yayi da aikinsa a nutse.
Barci nakeji, ga zazza6i yafara rufeni, hakan yasa ina gama saka rigar na fito, naci serious kawai sannan na fito.
d'ago idanu yayi muka had'a ido, da sauri nad'an rankwafa inajan rigar barcin k'asa wai danta rufemin cinya zuwa kwauri.
Baki ya ta6e yana wani janye ido cikeda basarwa. Irin shi baiga abin kallo d'in nanba.
Ni kuma na dalla masa Harara ina k'ok'arin hayewa gadon.
“ji mana”. ‘yafad'a cikin izza’.
Banza na masa zan haye gadon.
Yace “iyim, bakije daddarawa ba kenan yarinya, saina sake kaiki yanzunnan....”.
Kafin ya rufe baki nama iso gabansa na tsaya.
d'agowa yayi yana kallona yana kur6ar fresh milk nashi, ya d'agamin gira d'aya.
Baki na turo masa ina share hawaye.
Ya kamo hannuna ya zaunar kusa da shi, “nikam yalla6iya karki haifomin abin cikin kwan da halin kuka, bana son ragwan taka, 'yata ko macece jaruma za'ayi, irin wadda labarinta zai zaga lungu da sak'o na duniya”.
Harara na balla masa, yay saurin rik'e cup d'in hannunsa dayake zuba frash milk a ciki, “eh me, malama karkisa hantar cikina fitowa, irin wannan harara haka”.
Kad'an yarage banyi dariya ba, da gaskiyar Momma, halin Galadima d'aya da Sauban, tsantsar harmutsine da sanya damuwa a rai ya lullu6e halinsa na barkwanci, hakan kuma yanada nasaba da rashin samun mai jansa a jiki yana d'auke masa kewa da rage masa rad'ad'in damuwarsa. Momma hankalinta nakan jiyyar Abie, Aunty mimi kuma rainon Sauban, mom kuma tayi aure lokacin dayake buk'atar makusanci, s.......
Firgigit nayi saboda hancina da yaja, na kalleshi ina tura baki.
“maida wuk'ar yalla6iya, abin bana fusata bane, wace duniyar kika tafi hakane da nisa inata magana?”.
Marairaice fuska nayi ina shirin fara kuka, “please ka barni na kwanta barci nakeji”.
Kofin hannunsa ya mik'amin, na waro idanu ina girgiza masa hannu alamar a'a”.
Shima saiya waro nasa idanun yana fad'in “why?”.
“kawai ni bazan sha bane, aje a zubamin wani abu”.
“hakane kuma”. ‘ya fad'am yana kamoni ya jawoni jikinsa’.
Saman cinyarsa na zauna, da hanzari nafara k'ok'arin mik'ewa. shima saiya kama hannayena ya maidasu baya yanda bazan iya kata6us ba, madarar ya d'auka ya guntsa da yawa a bakinsa.
Waro idanu nayi ganin ya nufo bakina gadan-gadan, duk yanda naso kauda fuskata ya gagara, na datse hakwarana da sauri, shi kuma saya toshemin hanci, hakan yasa ni bud'e baki dole, dan ina buk'atar shak'ar numfashi. Tas ya juyemin fresh milk d'in abakina, sannan ya kuma rufe hancina saida na shanyeta sannan ya janye bakin, ni dashi duk muka hau sauke numfashi, kuka na sanya masa, amma hakan bai hanashi kuma guntsar madarba ya kuma juyemin a baki na, haka yayta min, ya kuma k'ara rabin kofi kuma, saida yaga ta kwalin ta k'are sannan ya sakarmin hannu na tashi zaune.
Bansan kawai na fara kaima k'urjinsa k'ananun dukaba, ina fad'in wlhy sai ALLAH ya sakamin, kai bama zan yarda ba fa, saboda k'azanta kaita had'a yawunka da fresh milk kana d'uramin, ni bazan yardaba”.
Shagala kawai yayi yana kallona, yakasa kare kanshi balle yunk'urin hanani, saida nayi mai isata sannan na fad'a k'irjin nasa ina raira kuka.
Lumshe idanunsa yayi yasaka hannayemsa ya zagayeni sosai yana kuma sakani jikinsa sosai. Nima sainayi luf Ina shak'ar k'amshinsa da yariga ya mannema fatarsa.
Munja wasu times a haka, ni ina kuka shi kuma idonsa a lumshe yana shafa kaina da saurarena.
Jiyay kawai jikinta ya saki, alamar barci ya d'auketa, sai ajiyar zuciya da take ta saukewa, bud'e idonsa yayi, sannan yakai bakinsa a hankali ya sumbaci sumar kanta dake tare da danshin ruwa har yanzu. zafin zazza6inta dake ratsa 6argon jikinsa ya sakashi fidda huci yana kuma sumbatar kanta.
Dr Farida ta sanar masa babu abinda zai hanata wannan zazza6in, koda tasha magani ya sauka saiya dawo, sai idan cikin yayi kwarine maybe ta daina ma gaba d'aya, amma mai juna biyu ba'a rabata da k'ananun ciwo makamantan haka. jiyay ya kuma k'aunar Momma d'insa a ransa, a hankali ya furta I love you my Momma”.
Tashi yay d'auke da Munaya a hannu, ya kwantar da ita sannan yaja bargo ya lullu6a mata. tare da sunkuya wa ya sumbaci goshinta ya shafa cikinta da hannunsa sannan ya mik'e ya koma inda yake.
Ya cigaba da aikin dayake a laptop Wanda ban fahimci komaiba a ciki, tsawon lokacin yana aikin, saida ya fara hamma sannan ya kashe. bayi ya shiga ya d'auro alwala, ya gabatar da nafila kafin yay shafa'i da wutiri yaja doguwar addu'a da kirari wa Ubangijin talikai, harda hawayensa sannan ya mik'e.
Ya kuma daidaita hasken fitilar d'akin sannan ya hau gadon shima ya kwanta, yay musu addu'a ya shafe cikin munaya (😂Galadima saboda tsaro ba tsoroba ko🥺).
a zatona zai rungumeta, sai naga ya gyara kwanciyarsa kawai a gefenta yaja bargo shima.
Galadima asuba ta gari, (ni dai rungume nawa mijin zanyi aradu🤫🙈⛹🏻‍♀).

Ga bannin asubahi zazza6in munaya ya sauka, hakanne ya sakata samun dad'in barci sosai, ta kuma kanainaye Galadima, wanda shi da kansa ya mirgino har inda take cikin barci ya rungumeta, dukda zafin zazza6inta nata ratsa nashi jikin yakasa barinta. ahaka kiran sallar farko ya riski kunnuwansu.
Kusan a tare suka farka, ganinsu manne da juna yasaka kowa barin jikin d'an uwansa da sauri, munaya dai kunya ta sakata juya baya, amma boss ko a kwalar rigarsa, saima tashi da yayi yana wani ciccin Magani ya shiga toilet.
Alwala ya yo, baiyi mata magana ba ya fice abinsa.
Munaya ta raka bayansa da harara tana fad'in Girman kai dai rawanin tsiya wlhy. tashi tayi itama ta shiga bayin, amma sa6anin shi ita harda wankan gasa jiki (lallai kinji basawa Munaya🤭, wannan gasa jiki dabaya k'arewa haka🤥😂).
Fitowa tayi tanata kumbura fuska, ni dai na lalla6a na shige bayinta danna dandalo arzik'i😝 lol (koya kukace fans🤷🏻‍♀😂?).

****************************

Ban sake jin d'uriyarsa ba sai around 9:30am.
Tashina a barci kenan na rarrafa zuwa bayi da k'yar nayo wanka, dan banajin dad'in jikina gaba d'aya, danan ya saki sai nan ya kama ciwo.
Motsin mutum naji a bayana dan haka na waiga, Galadima ne cikin Farin wando da t-shirt itam fara tas, ya d'aure k'ungunsa da Navy blue d'in belt, sannan ya kawo jacket navy blue itama ya saka, babu takalma a k'afarsa, sai dai k'afar fes tamkar ba'a takata a k'asa, sai agogon azurfa mai k'yau d'aure a tsintsiyar hannunsa.
hummm dan k'yau kam dai yayishi, sai dai ni bawai ya birgeni bane😏 (ho Munaya banda zuk'i ta malli dai🤥🤣😝🙆🏻).
Janye idona nayi na maida kan gyaran gashina da nakeyi.
Shima baice uffanba ya wuce wajen frigate, fresh milk ya d'akko yatako gaban mirror inda nake zaune. a saman mirror ya ajiye kwalin madarar ya jingina bayansa shima, idonsa a kan gashina danake gyarawa. ya d'au madarar ya zuba a cup d'in daya d'akko tare da mik'omin.
“ni ba ita zan shaba”. na fad'a ba tare da na kalleshi ba.
“mikenan?”. shima yafad'a cikeda k'asaita.
Yanzunma ban kalleshi ba nace “tea”.
Kofin ya dire saman mirror yana tattare hannun rigarsa, “salon ki k'onamin idon abin cikin kwan kenan, to za6i ya rage naki, sha da arzik'i ko kuma d'ura”.
Babu shiri na d'auki kofin na kwankwad'e, dama iyayine inajin yunwar.
Kofin na mik'a masa ina 6ata fuska tamkar zan fasa ihu.
Ya d'agamin gira yana fad'in “taimakon kai my friend”.
Gefe nayi da fuskata ina fad'in “kai duk salon mugunta ka sani ai”.
“martabar gudan jinina nake karewa”. yay maganar yana k'ok'arin ficewa.
Baki na na ta6e ina harar bayansa, su gudan jini anji jiki kuwa.
Ganin zai fice nai saurin cewa “nifa inason zuwa kitso, kuma zan koma school”..
Tsayawa yay cak daga yunk'urin fitar da yakeyi, Batare daya juyoba yace “babu wannan tsarin a masarautar gagara badau”.
Yana gama fad'a ya ida ficewarsa.
Tamkar zan fasa kuka nayi jifa da cumb d'in hannu na ina fad'in “ina ruwana dawani tsarinku ni, makaranta ta nakeson komawa ehe”.
Yana jiyota amma ko'a jikinsa yaci gaba da k'ok'arin fitarsa hankali kwance.

★★★★★★★★★
Chapter 21 · 0% Book details