← Book details Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 76

Sashe 69

Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

🤣abin dariya, ku a naku zaton yaranku sun 6oye Kansu be?, to suna hannun Galadima, lafiya kawai muke jira ya samu ya yagalgalasu kuma ya cafkoku munafukai🙄😏.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu._*😭🙏🏼
[7/18, 2:19 PM] Aysha Galadima: *_typing📲_*

💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*

*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

~Book 2~ 👉🏻2⃣9⃣

..............Harmun kwanta zuciyata ta kasa samun nutsuwa, inason naje naga halin da yake ciki, Dan koda su Nuren suka wuce ban komaba, sakkowa nai daga kan gadon, laraba dake a tsakar d'akin kan katifa tace, “ranki ya dad'e lafiya kuwa?”.
Banason ta kalli abun da wata manufa, dan haka nad'an murmusa, “uhmm iya inason duba Abbansu ne, ban saniba koyasha maganinsa kafin ya kwanta”.
“eh lallai hakan yanada k'yau, badan ma jego ba ai bai kamata ya kwana shi d'ayaba”.
“aiba shi kad'ai baneba iya, Sauban ne zai tare dashi ”.
A to hakan yayi.

Bance komaiba Na kar6i gyale wajen Samha Na saka na fita.
Masarautar tayi tsit, da alama kowa yasamu nutsuwa a sashensa, ban tsaya knocking ba na shige kawai, a falo na iske Sauban zaune yana kallon ball, cikin tsokanar da ya iya yace, aunty gimbiya kin kasa barcine?”.
Nayi murmushi, “yaa Sauban matarka taga ta kanta wlhy”.
Dariya yayi kawai, nikuma na wuce abina.
Saida nayi sallama kusan uku banji an amsaba, saina shige kawai. Zaune na iskeshi a bakin gado ya jingina da fuskar gado, hannunsa d'auke da Qur'an yana karatu a hankali, idonsa cikin medical glasses, gakuma system a gefe itama a kunne. naji dad'in yanda na sameshi, Addu'a da karatun Qur'an babban jigone dake wanke zuciya da damuwar d'an Adam (duk lokacin da ranki ya 6aci d'auki Qur'an ki karanta koki saurara, wlhy zakuji sassauci mai yawa).
Har zan juya na fita sai naji yay gyaran murya, juyowa nayi na kallesa, har yanzu dai karatunsa ya keyi. na dawo na zauna a bakin gadon ta d'ayan gefen, shikuma ya cigaba da karatunsa, kusan mintuna 6 kafin ya rufe Qur'an d'in ya ajiye, ya cire medical glasses d'insa shima ya ajiye yana kallona, ko kad'an fuskarnan babu walwala, nuni yamin da inzo.
Ban musaba na tashi nadawo 6angaren inda yake, zama nai d'an nesa dashi kad'an.
Ya lashe le6ensa da cizarsa kad'an yana hard'e hannayensa a k'irji.
Muryata can k'asan mak'oshi nace, “yaya jikin?”.
Kansa kawai ya jinjina min cikin lumshe ido, sannan ya motsa baki kamar zaiyi magana saikuma yay shiru, saida yaja wasu seconds sannan yace, “Munaya!?”.
“Na'am”. Na amsa ina kallonsa da janye idon lokaci d'aya saboda ya tsareni da nasa.
Huci yad'an furzar, ya cire hannayensa daga k'irji yana gyara zama, “Nayi nazaci sosai akan maganganun ki na d'azun, nakuma fassarasu aji-aji, na fahimcesu a yanda tawa fahimtar take, so a wannan karon rok'o nake miki na k'arshe akan ki fad'amin abinda kika sani, ni d'an Adam ne, ban isa cewa komai na sanshi a rayuwaba ko na iyashi, sai abinda Ubangiji yaso in sani kawai, Munaya ada ba haka rayuwata takeba, mutumne ni mai yawan raha dason nishad'i, amma daga lokacinda nafara sanin kaina da matsalar mahaifina sai komaina ya canja, nazama mutum mai yawan rashinson magana, nafison kullum na kasance ni kad'ai a kuma ke6antaccen waje” yay murmushin takaici sannan ya cigaba da fad'in “Bawai hakan Na birgeni baneba ko a San raina, saboda Ina shiga k'uncine, amma banida za6in daya wuce hakan. nasha wahalhalu Na rayuwa kala-kala kafin na tsaya da k'afafuna, zuciyata ta bushe namance daga wane tsatso na fito, domin idan kinganni a lokacin da nake karatu da koyan sana'oi bazaki ta6a kawo ni jinin sarauta baneba, ko d'an wani, nayi gwagwarmaya sosai irin wadda d'a Mara gata yakeyi, badan mahaifiyata bata sona bane ta tsaya tsayin daka wajen ganin na horu kona nemi na kaina, hikimarta itace nazama jarumi mai yawan juriya, nakuma kwato mana y'ancinmu a lokacinda ya dace, duk wannan fad'i tashin da kikaga inayi wlhy badan nayi mulki baneba kamar yanda su suke tunani, Burina kawai nasan miyasa aka durk'usarmin da mahaifi? Tabbas ni jinin sarautane gaba da baya, kuma yana yawo a cikin jinina, amma rashin kwanciyar hankalin dake cikin sarauta baya birgeni, kallon kitse kawai akema rogo, ayau inason Kituna kema kin haifi yaranda sun rigada sun shigo cikin wannan harmutsi, tunda tazama jininsu, ki fad'amin kodan mu gyaramusu gobensu su rayu cikin salama koda bama numfashine, nasan hakanan bazakima Harun abinda kikai masa d'azunba saboda son zuciya kawai, please miyasa kika hanashi d'aukar Abdurraheem ne? Miyasa kikak'i barina na fad'a masa gaskiyar abinda ya faru?”.

Shiru nayi nakasa cewa komai, sai faman had'iye abinda ya tsayamin a mak'oshi nakeyi, Dan bansan yanda zai kalli abunba koya fahimceshi, babu Abu mafi saka rud'u irin cin amanar makusanci, gashi dai a Ransa shifa ba k'aunarka yakeba, amma kulum yafi kowa kusanci da kai, da Nuna girmama alak'ar tsakaninku. (ALLAH ka Shiga tsakaninmu da duk wani Wanda yake tare damu a matsayin fuka biyu, Dan yanzu abinda yafi komai yawaita kenan a rayuwar d'an adam☹😭).
Cikin katsemun tunani Yace, “please my friend say Something mana”.
Kaina na jinjina masa, cikin nutsuwa nafara masa bayani, Dan yau nayi alk'awarin sanar masa komai, koda zai samu wani haske akan lamarin, shima yasamu nutsuwa a rayuwarsa.

“Tabbas kamar yanda kake zargi aiki nakema wani, saidai fahimtar wanene d'in shine mai wahala, na fad'a maka tun farko a dalilin bak'on Abbanmu naji wani yankin matsalasa da bai ta6a sanarma waniba a ahalinsa, a lokacin da wancan abin yafaru Abba yak'i fad'ama kowa dalilin fishinsa a kanmu, dakuma abinda muka masa, hakanne yasaka innarmu zuwa tasamu baba mai kanwa abokin kakanmu na k'ut da k'ut ta sanar masa fushin da mahaifinmu keyi damu, ankuma bashi hak'uri yak'i sauraren kowa, gashi ba dad'in zama takejiba cikin matan gidanmu, wannan Abu daya faru sai sukejin dad'i damata arashi da habaici, harma damu kanmu. baba mai kanwa yace taje zai masa magana, bayannan bamusan misuka tattaunaba. Sai da bayan komai ya lafa harma mun fara karatu sai sanata halluru ya buk'aci abbanmu yabama y'ay'ansa biyu auren yara cikin yaransa, sunzo gidanmu har suka nuna mune za6insu, a lokacin tabbas naji a raina Sa'eed yamin sosai a rai.....”
Galadima ya tsuk'e fuska yana taune lips dajan k'aramin tsaki.
'Dagowa nayi nad'an kallesa, amma saiya basar tamkar bashine yayiba, nima sharewa nayi na cigaba, “bamusan miya faruba sukace Zarah da siyama sukeso, wannan Abu ya 6atama Abbanmu rai, dan aganinsa anyi wani abune domin k'untatama mahaifiyarmu, hakkane yasashi zuwa ya sanarma Baba mai kanwa, dama duk dai wani Abu dazai taso gidanmu shine ake sanarmawa, yayi sasanci koya tsawatar, koda kuwa innro ce. bayan Abbanmu yaje da kwana d'aya, sai innarmu ta aikemu wajensa muka kaimasa goro da y'ar sayayyar da takan masa lokaci-lokaci, saboda yamusu hallaci a rayuwa a yanda take bamu labari, shiyyasa a kullum take d'aukarsa uba”.
Mun iske baba mai kanwa a d'akinsa na zaure kamar ko yaushe, muka gaidashi cikin girmamawa da tsokanarsa a matsayinsa na kaka, shima ya tsokanemu tareda sakamana albarka kamar yanda ya saba, saiya murmusa tareda gyaran murya, hakanne yasaka muka nutsu dan fahimtar magana mai muhimmanci zaiyi, ya nisa cikin dattako na tsufa ya fara fad'in___”.
Chapter 69 · 0% Book details