Sashe 63
Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Fans insha ALLAH dai abuwa sun fara warwarar zare, sai mubi su Galadima muga yanda zasu dawo mana da triplets d'inmu gida😭, yau Munaya tabani tausayi daga ita har Galadima, dan shima dai dannewa kawai yake saboda jarumta, ALLAH ya rabamu da sharrin mak'iyi komai k'an k'antarsa, Harun da sauran munafukai MAZA BISA KANKU🏇🏻🏇🏻🏇🏻🏇🏻🏇🏻.
Barkanmu da dawowa my sweet fans🤕😡.
Yau bana cikin yanayin dariya😡
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
[7/16, 5:34 PM] Aysha Galadima: *_typing📲_*
💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._*
*_♦RAINA KAMA.....!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
~Book 2~ 👉🏻2⃣7⃣
................Tunda suka d'akko yaran suketa kuka, musamman Abdurraheem dahar shid'ewa yakeyi, ALLAH dai yabasu sa'a ne saida suka fito suka fara kukan, neman haukatasu ma sukaso yi tun amotar, jisukai tamkar su rufesu da duka, saidai babu damar hakan, dan basuga abin duka jikin wad'annan kwad'unan yaranba.
Da farko sunga kamar ana binsu, sai daga bisani ne sukaga ba haka baneba, har dai suka iso gidan y'an uku basu barsu sun shak'i iska ba.
Suna shiga suka danna musu wasu allurai, cikin mintuna k'alilan jikinsu dukya saki sukayi luf.
ganin lokaci yaja har kusan 10pm babu alamar wani motsi hankalinsu ya kwanta, dan sunsan dai tabbas sun tsira, wayar wadda ta sakasu aikin suka kira, amma tak'i yin picking.
Cikin matan d'aya tace, “kusan dai bazata d'aga ba, saboda nasan masarauta a haukace take yanzu, saidai mubari zuwa safiya”.
Tsaki d'aya yaja, “kai nifa gaskiya a tsorace nake, gara ta d'auka asan mafita, bana buk'atar gawar yarannan takwana a hannunmu, kunsanfa babansu mayene wlhy, tsaf zai bibiyemu”.
“kai dalla ai yanzu bashida wannan damar, caza'ayi a fad'ama police, sukuma aikinsu zai farane zuwa safiya, kafin sannan munma gama binne gawar yaran mun kama gabanmu”.....
“eh kumafa hakane”.
Suna tsaka da wannan hirarne su Galadima suke shigowa, gidan k'aton gaskene dan haka suka kasa fahimtar INA zasu dosa, Galadima Yakuma danne abin kunnensa da d'anyatsa d'aya cikin murya k'asa-k'asa yake fad'in “Sauban kufara muje”.
“yauwa Yaya zaku shiga hannunku Na haggu, duk sunajin maganar dan haka sukabi hannun haggu, yayinda su Ameer ke binsu a baya suma. Galadima dake gaba ya bud'e k'ofar a hankali duk suka shiga, daga can Saleem yace, “duk Ku rarrabu sir, dan abin ya nuna yaran suna ainahin tsakkiyar gidanne”.
Batare da sunyi magana ba duk suka rarrabu.
'Daya acikin 6arayin yace, “kai nifa kamar motsi nakeji gaskiya”.
“to sannu mai kunnen maciji”. cewar d'aya aciki.
Cikin matan d'aya tayi dariya tana fad'in “nakula kaidai bibo matsoracine halan?”.
Hannu ya d'aga zai kwad'eta, a harzuk'e yana fad'in “k wlhy kacaccalaki zanyi, bar ganin kinfito daga masarauta, kubadan ma an had'amu aiki dakuba kun Isa saninmu ne? jimin y'ar iskar mara kunya”.
Hak'uri y'an uwansa suka bashi, ya mik'e yana jan tsaki ya fito danya duba.
Galadima dake la6e cikin labule yay saurin fitowa, abinka da dogon mutum dan danan yasamu damar shak'osa ya shaka masa abin hannunsa, tun yana k'ok'arin kare kansa har jikinsa ya saki ya kwantar dashi a k'asa.
Jinjina Muftahu dake kusa dashi yamasa, sannan suka cigaba da shiga.
'Dayar baiwar tana kitchen tare da wani suna iskancinsu Nuren yasamu damar sad'ad'awa, (kunsan dai shahararren kidnapper ne🤭😂) yauma tsiyar ya aikata wajen jefa ma namijin handkerchief a fuska, macen tai yunk'urin zuba ihu yasa k'afa ya tad'ota ta fad'in, sannan ya danne bakinta da ya shak'a mata itama.
K'arar fad'uwarta taso fargar da sauran, dan haka duk suka mik'e suna fara lek'e-lek'e, aikam Muftahu yasamu ya tad'e d'aya ya fad'i, Ameer dake bayansa shima ya shak'a masa, harda mangareshi yana fad'in “kwallon shege taka ta k'are, inakai ina satar sarakunanmu insha ALLAH”.
dariya taso kufcema Muftahu amma ya danne bakinsa da hannu yana girgiza kai saboda tsiyar Ameer.
Fad'uwar wani da suka juyo ya sakasu kuma saurin waigawa wajen, Galadima ne ya sakeshi ya fad'i, “shegen k'arfin jinine dashi dak'yar abin yay masa tasiri”. Galadima ya fad'a yana halbinsa da k'afa.
Gaban d'ayar baiwar dake la6e jikin labule ya fad'in, dan tabbas wannan muryar Galadima ce, kowa yasan bai iya R ba, zuface tashiga keto mata jikinta na 6ari, ta to she bakinta saboda kuka daya kufce mata, saigata tana tsilala fitsari saboda ganin Galadima yanufo ta wajen, shikenan itakuma tata tak'e, wannan zakin gagara badau d'in binneta kawai zaiyi da ranta.
Waige-waige Galadima ya fara saboda jin numfashin mutum dayakeyi kad'an-kad'an ta wajen, har yayi gaba ya dawo baya yana yaye labulen wajen. shi da farkoma ya zata aljanace saboda yanda ta zazzaro masa ido. fincikota yayi ya Watso tsakar d'akin, mamaki ya kamashi ganinta da kayan manyan kuyangin gidansu.
“tashi tsaye”. ya fad'a cikin matuk'ar d'aure fuska, kad'an yarage kashi ya kufcemata.
“ina suke!!!”.
Yafad'a cikin matuk'ar tsawa daya firgita hatta su Sauban dake saurarensu a waya.
Wannan tsawar tasa ce ta saka d'ayan fitowa a tsorace da gun a hannu, Aunty Salamah dake bayansa bai saniba ta hankad'ashi yay gaba zai fad'in, Nuren ya ida tad'eshi da k'afa.
Gun d'in data fad'i ta silalo gaban Galadima ya taketa da k'afa yana huci da taunar lips. Handkerchief d'in hannunsa yasaka ya d'auki bindigar, ya saita namijin da ita.
Mazari jikinsa ya fara yana d'aga hannu sama, “dan ALLAH ranka ya dad'e karka kasheni, wlhy bansan komaiba, oganmu ne yasan komai da wannan baiwar”.
Kunamar bindigar Galadima ya d'ana, nanfa su Muftahu duk suka rud'e, Nuren yace, “Brother please karkayi harbi, nasan zasu fad'a mana, dan ALLAH kayi hak'uri”.
Gaba d'aya jijiyoyin kan Galadima sun mimmik'e, sai fidda huci yakeyi a wahalce.
Muftahu ma yashiga rok'onsa, Su Saleem dake sauraren komai dagacan duk suka rud'e, Sauban yace “yaa Sam ALLAH ya huci zuciyarka, amma idan ka aikata haka a wajenwa Zamu samu hasken sauran abubuwan?, dan ALLAH kayi hak'uri badan mun isa mu saka ka ba, saidan halin da mahaifinmu ya tsinci Kansa tsawon shekaru, gakuma dama tazo mana ta Sanin sirrin 6oye, muyi amfani da ita ta sauk'ak'ak'iyar hanya....”
Sakin gun d'in Galadima yayi ak'asa yana dafe k'irji, wani mugun bugawa zuciyarsa keyi, da baya-baya yanemi zubewa a k'asa, cikin hanzari Nuren da Muftahu suka taresa, da taimakonsu ya zauna akan kujera. Yana nuna baiwar da d'ayan hannusa.
Aunty Salamah data fahimci mi yake nufi tace, “ina yaranne?”.
Jikin baiwar Na 6ari ta nuna k'ofar wani d'aki, shiga Aunty salamah tayi itada Ameer suka d'akkosu.
Saidai duk a firgice suke, dan yaran babu alamun rai tare dasu, zufa ta shiga ketoma Aunty Salamah, haka ta fito rungume da Abdurraheem da Amaturrahman, shikuma Ameer ya d'akko Abdurrahman yana fad'in “Aunty kamarfa yarannan sun mutu”.
Wannan kalma caraf a kunnen Galadima.
Wata muguwar zabura yayi yamik'e tsaye, sai ya kuma dafe k'irjinsa da sauri hajijiya tafara katantanwa dashi, basu fargaba sai jinsa sukayi kawai a k'asa.
Gaba d'aya suka kuma rikicewa, sukayi kansa.
Muftahu yace, “bamuda isashen lokaci, asuba ma ta gabato, dolene mubar gidannan dan ko yaushe zamu iya gamo da abinda bamu shirya masaba”.
Duk sunyi na'am da wannan maganar tashi, nan fa suka fara kwasar wad'anda suka sumar suna kaiwa mota, sannan suka tasa k'eyar d'ayar baiwar da wancan, suma.
Yayinda Nuren yad'an bincika gidan, ganin babu wani abunda zasu k'aru dashi yazo suka kama Galadima daya Suma suka fita dashi.
Hankalin Sauban ya tashi matuk'ar tuk'ewa, ya fito yana nufarsu da ta6a jikin d'an uwansa, “Yaa Nuren miya farune? miya faru da Yaa Sam?”.
“Sauban bamu hanya, ba lokacin wannan baneba yanzu”.
Sole Sauban ya matsa baya hawaye Na kwarara a idonsa, suka shinfid'ar da Galadima a bayan mota, sai lokacin Sauban yaga yaran a hannun Aunty salamah da Ameer, da hanzari suma ya nufesu, Aunty salamah ta bashi Abdurraheem, jujjuya yaron yayi yaji kamar baya numfashi, “innalillahi....” yashiga maimaitawa zufa Na keto masa, dolene Yaa Sam ya suma, hawaye yafarayi yana rungume yaron a jikinsa, Tausayin dukkan ahalinsa da suka kwallafa rai ga yaran ya kamashi, musamman ma iyayensu, ya ALLAH nasan bazaka jarabcemu da abinda bazamu iyaba, ALLAH kabamu juriya”.
Muftahu yace, “su shiga mota, duk shiga sukayi, Nuren dasu Ameer suka wuce da wad'ancan sauran wani waje daban, Muftahu kuma ya kira police d'in da suka shirya komai dasu, a hanya suka had'u, sai sukai joining d'insu tamkar tare sukayi aikin, suka kira manyansu suna sanar musu gashifa sun kama wani matashi da baiwar masarauta da yaran....
Wannan labari yama su d.p.o dad'i ya kira IG shima ya sanar masa, yaji dad'i shima, koba komai mai martaba zai yaba k'ok'arin dasukayi, akace yanzu suna inane?.
Amsawa sukai da gasu a masarauta, dan harda Galadima sukayi aikin, yana kuma cikin wani yanayi shida yaran yanzu haka.
Basuda za6in daya wuce suce musu to suma gasunan zuwa masarautar.
Tun'a mota su Muftahu sun gargad'i baiwar nan da d'ayan mutumin akan suce su biyune suka sacesu, inhar sukace basu kad'ai bane wlhy saiya kashesu, sannan su tanaji fad'ar wani abun ba ainahin gaskiya ba, (dan Galadima baya buk'atar police su shiga cikin aikinsa yanzu, yafison saiya kama kowa sannan, dan inhar police suka shiga aikin mutane da yawa zasuyi escape ne) shiyyasa Muftahu yayma wad'ancan gargad'in tunma kan su k'arasa cikin masarauta.