← Book details Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 76

Sashe 19

Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yunwar da yakeji tasashi bayan yayi shiri ya samu fresh milk yasha kawai, sannan yafito, d'akin Munaya ya lek'a, saiya isketa baje a gado tana shak'ar barci, baiyi yunk'urin tashinta ba yafito.
Har dogaransa sun taso yace suyi zamansu su huta, zai fita shida Sauban, cikin damuwa sarkin mota yace, “kayi hak'uri ranka ya dad'e, koda nine kawai mu fita, Mai martaba ya sanar yau a fada kar'a sake barin wani d'an gidannan yafita wani waje shi kad'ai”.
Kallonsa Galadima yayi, kamar zaiyi magana saikuma yafasa ya bud'e mortar da kansa ya shiga, batare da ya jira an bud'e masa ba.
Da hannu sarkin mota yayma sauran dogaran nuni da su biyosu a baya idan sun tafi.

A wani waje suka had'u da Nuren, Nuren ya fito daga motarsa yadawo inda Galadima yake, sai sarkin mota yafita yabasu waje kawai.
Galadima yace “please idan kaine ka sakeshi”.
Da mamaki Nuren yace, “wai Muftahu n dai? am telling you banida alak'a da d'aukarsa. yarinyar Minister ce kawai a hannuna”.
“innalillahi, wlhy Nuren inajin tsoro, karsuje su cutar dashi”.
“Sameer! nifa ina zargin kawai ya had'a baki da wasune suka kamashi dan yayi wasa da hankalinmu”.
Idanu Galadima ya tsurama Nuren tamkar yana hango gaskiyar maganarsa, ya saki wani guntun murmushi, sannan ya gyara zamansa yana fad'in “well, koma minene dai zai fito ai”.

Nuren yace “ni kaga dama kabar zancen wani Muftahu n banza can, way note mu wuce gidan sirikanka kozamu samu wasu evidence daga canma akan Accident d'innan”.
Agogon hannunsa ya kalla, sannan ya kalli Nuren d'in alamar suje.

Anan Nuren yabar motarsa suka tafi ata Galadima, saida suka fara tafiya Galadima ya lura da mototin dogaransa a bayansu.
d'an murmushi yayi yana kallon Sarkin mota, yace “sarkin mota an karya min doka kenan?”.
Sarkin mota daya fahimci Galadima yagane dogarai Na binsu sai yayi 'yar dariya, yace “ka gafarceni ranka ya dad'e, bazai yuwu mu barka ka fita kai kad'aiba ai, dan fitarka babu kowa tafi ta kowa had'ari a masarautarnan, mai martaba ma nasan saboda kaine ya saka dokar ai”.
Galadima baice komaiba sai murmushi dayayi, Nuren ma murmushin yayi, sannan yace “amma kamar bayan motar dogaranka akwai wata bak'ar mota Na bin tasu?”.
Galadima ya juya shima, tabbas anabin motar dogaran a baya, “sarkin mota su wucemu, karsu tsaya”.
“To ranka ya dad'e”.
Bayan sarkin mota ya sanar musu suka wuce su Galadima, motarma ta wuce, da kallo Nuren da Galadima suka bita, Nuren yay hanzarin d'aukar motar hoto a wayarsa. “humm da alama suna zaton kana d'aya daga cikin motocin canne”.
Murmushi Galadima yayi, a k'asaitarsa yace, “kokuma suna son wasa da hankalinmu ba”.
Da mamaki Nuren yace “kamar ya?”.
Murmusawa Galadima ya kuma yi, ya kwantar da kansa jikin seat yana lumshe idanu, “Nuriddeen! Sameer ya wuce tunanin dukkan mai tunani, kai tsaye ba'a gane manufar zuciya, kwanji ko dama basu ke nuna k'arfin ikon mai ikoba, nazarin komai daki-daki da iya sarrafa duniya a yanda tazo shike nuna k'arfin gwarzan taka, mazantaka ba'a shaidata a fuskar namiji, duk lokacinda kai gamo da nama, kud'i, mata bisa hanya, karkayi rawarkan d'auka ko murnar ALLAH ne ya baka, zata iya yuwuwa tarko aka d'ana maka, shi k'yawu had'arine, 6oyeshi kuma nagartace, maiyi baya fad'an zaiyi, sai dai aga aikinsa a k'asa, tasowar iskar hadari bashi ke nufin ruwan zai zuba ba, watak'il sunan wannan iskar gyara kayanka. Dalili da dalilai basa ta6a saka zuciyar Wanda yake nema ta raunana, time d'in da zan nunama mak'iyan mahaifina d'an zaki ya girma yayi, sun durk'usar da shi a k'asa batareda tunaninsu yabasu ya haifi Raina kama ba, Su cigaba da raina aikin Muhammad Sameer daga k'arshe kuma saisuga gayya, tafiyar hawainiya bashike nufin gazawar kuzarinta bane, lokuta da dama hanzari kan katse igiyar cikar buri, a sannu kowa zai fahimci wanene *_RAINA KAMA....._*👎🏻

Ba Nuren ba hatta da sarkin mota maganganun Galadima ya shigeshi, tabbas mutane dayawa sunama Galadima kallon mutum mai yawan sakaci da rashin ho66asa, koshi yana d'aya daga ciki, amma wannan zantukan nasa sai suka sakasu a rud'ani, kenan akwai abinda sud'in basu saniba...........
Dole tunaninsu ya katse saboda isowarsu gidansu Munaya.

Fita sarkin mota yayi yanema musu iso, babu dad'ewa saiga baba k'arami ya fito, sarkin mota ya bud'ema Galadima, yayinda Nuren ya bud'e da kansa, zuciyarsa sai jujjuya hannunka mai sandar Galadima yakeyi.
Dukda baba k'arami yayi mamakin zuwan Galadima haka ya danne, yaymusu k'ar6a ta girma, sannan suka shiga cikin gidan.
Gidan tsitt tamkar babu mutane, saikace ba gidannan bane mai kama Dana 'yan dambe😂, (yo kowa Na tsoron a korashi gidansu🤣😝).
A falon daddy aka musu masauki, dan danan aka cika musu gaba da kayayyaki, baba k'arami ya fita domin basu damar cin wani Abu.
Babu abinda suka ta6a, dukda kuma Galadima ma yunwa yakeji, a haka daddy da baba k'arami suka dawo.
Daddy yace “anya kuwa wannan d'an namu yana d'aukar gidannan matsayin nasu?”.
Murmushi Galadima da Nuren sukayi, Galadima yace “sosaima daddy”.
Baba k'arami yace “ta INA zamu amince da haka kuwa, bayan inada tabbacin ko ruwan gidannan Baka ta6a sha ba”.
Kunya Ce ta kama Galadima, sai kuma yaga bai k'yautaba, ya rissinar da kai yana fad'in “amin afuwa zan gyara”.
Mik'ewa baba k'arami da daddy suka kumayi, “to mun bada dama ta biyu”. cewar Dady yana dariya.
Bayan fitarsu Nuren ya bud'e kulolin shima yana dariyar, danbun shinkafane daya samu nutsuwa ta musamman, sai k'amshi mai dad'i yakeyi, daga Galadima har nuren saida kwad'ayin cin abincin yazo musu.
Kallon Galadima Nuren yayi yana d'aga gira, Galadima yay murmusa tareda fad'in “kadaiji kunya”.
“kaima jinta zakayi yanzu, dan nasan ci zakayi”.

Yau dai kam Galadima yaci abincin gidansu Munaya, kuma gashi girkin innarsu, babu kunya sukaita zuba Santi shida Nuren sunama juna dariya, Galadima harda su6utar baki yana fad'in “amma my mata muguwace, bata ta6amin irin wannan ba”.🙀
Mi Nuren zaiyi inba dariya ba🤣, su Galadima anji dad'i har kwalwar kai Baki ya bud'e😂😝.

Saida suka mammala tsaf sannan su baba k'arami suka dawo, sunji dad'i dasuka iske sunci.
Daga nan sukayi gaisuwa, su baba k'arami suka d'ora da godiyar d'awainiyar Abba da Galadima ya d'auke musu.
Murmushi kawai Galadima yayi.
Nuren ya gyara zama, a ladabce yamusu bayanin son fidda Abba da Galadima kesonyi, dan likitoci sunce ana buk'atar kulawa saboda karayar hak'ark'arinsa data k'ugu, “to yanzu haka dai angama setting d'in komai gameda tafiyarsa, har asibitin daza'a kaisa, visa d'insa da komai, sai dai anason tafiya da mutum biyu a cikinsu, mi kuka gani akan Wanda za'aje da shid'in?”.
Daddy da baba k'arami suka kalli juna, summa rasa wane irin farin ciki zasu nuna dan Galadima yasan sunji dad'i? sunta jero masa k'yawawan addu'oi, kafin daddy yace “ai kawai sai atafi da jafaru da Ai'sha, dan bai kamata mutafi mu duka ba gida babu kowa, dukda akwai su Anas, gakuma su Hameed zasuke zagayowa, amma hakan yafi dai.
Duk sun gamsu da hakan, dan haka suka buk'aci passport d'in baba k'arami da inna, ita inna babu, sai sunje an mata, amma baba k'arami an samu.
Sun bari akan zuwa anjima za'azo akai inna tayo.
Daga nan Galadima ya buk'aci number da aka kira aka sanar musu da accident d'in Abba.
Daddy yace Ai'sha aka kira, saidai akawo wayar tata. Kiranta yay yace tabama cikin su Aryaan ya kawo wayarta.
Babu dad'ewa saiga Aryaan d'in da ita, yanda yaron ya gaishesu saida abin ya birge Galadima, ya yarda yaran gidan akwai tarbiyya babu laifi kam.
Galadima yace, “amma Dady ko numbers nawa Abba ke amfani dasu?”.
baba k'arami ya bashi amsa da cewar “uku ne”.
Nuren yace “kozamu samesu dukansu?”.
Dukda baba k'arami da daddy sunshiga mamaki, dansu zukatansu basu kawo musu akwai wani Abu a k'asa ba, sun d'auka kawai Abba yayi Accident ne dai.
Baba k'arami yabasu Numbers d'in duka.
Bawani bincike Galadima yayi a wayar innarsu Munaya ba, wani Abu kawai ya saka (Wanda Nima ban saniba😱) yabama Dady wayar yana fad'in “zata bar wayar anan dan a can bazatayi aikiba, kuma gashi muna buk'atar wayar, dan haka daddy saika rik'e a hannunka tunda kai kana gida”.
Dady ya amsa da to, duk su Galadima sun kuma sakasu a duhu.
Sallama sukai musu suna fito domin tafiya.
Harsun Shiga mota saiga Aiyaan da gud'u d'auke da wata Leda.
Sarkin mota ya tareshi yana fad'in yaro miya farune?”.
“Auntynmu za'a kaimawa inji innarmu”.
Galadima yayma sarkin mota nuni da yabar Aiyaan d'in ya k'araso.
Bud'e murfin Galadima yayi, Aiyaan ya k'arso, Galadima ya kamo hannun Aiyaan yana murmushi, “my friend ya akayi?”.
'Uncle innarmu ce tace akaima Auntynmu dan ALLAH”.
murmushi Galadima yakumayi, sannan ya kar6i ledan yana fad'in “ita kad'ai banda ni?”.
Aiyaan yad'an zaro ido waje, sai kuma yace “to bara naje Na fad'am innarmu kaima ta baka naka”.
Da sauri Galadima ya kamo hannunsa dan yana neman tsillawa da gudune, “kaga dakata, idan naje saimu raba wannan da ita, yanzu dai ka fad'ama innarmu ta shiryaka gobe zan aiko a d'aukeka kazo ka zauna damu tunda kuna hutu ”.
Cikin murna Aiyaan yace, “wajen auntymu?”.
Galadima ya jinjina masa kai.
“to amma kuma Aryaan fa?”.
Cikin mamaki Galadima yace, “wanene Aryaan d'in?”.
“lah baka San mu 2wins bane ba?”.
“da gaske?”.
“ALLAH kuwa”.
“to shikenan, kacema innarmu ta shiryaku Ku duka biyun zakujema Aunty hutu”.
Cikeda murna Aiyaan ya shek'a da gudu gida danya kai labari.
Galadima yay murmushi yana rufe k'ofar motar, Nuren ma murmushi yakeyi, a fili yace, “yara sunyi wlhy”.
Galadima ya kalleshi, cikin d'age gira sama yace, “kayi aure”.
Sosai Nuren yay dariya.

******
A inda suka d'auki Nuren anan suka ajiyeshi, su kuma suka koma masarauta, sun iske tuni dogaran sun dawo abinsu.
d'akinsa ya Shiga, ya iske Sauban nata barcinsa.
Bai tadashiba, yadawo falo ya zauna.

_____________________________
Chapter 19 · 0% Book details