← Book details Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 76

Sashe 2

Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Babyna wai mike faruwane haka?”.
Da gyar Munubiya ta d'ago ido daga kwancen datake a kujera ta kalli yaa Marwan dake mata tambayar.
Ta shagwa6e fuska tace, “wlhy Yaya jikinne babu dad'i, kamar jiya sai kwankwatsa kasusuwane keyi”.
Zama yay kusada ita, yad'ago kanta ya jinginata a jikinsa yana ta6a wuyanta, “please ki yarda muje asibiti adubaki mana?”.
“a'a dan ALLAH Yaya, wlhy banason zuwa, kabari muga kwana biyu idan bai dainaba saimuje d'in”.
“Amma kuma k'ya zauna da ciwo, ki daure dai, kinga ko abinci kin kasa mana fa”.
“babu damuwa Yaya, yanzu zan tashi na d'ora, dan zazza6inma ya sauka ALLAH”.
“Ana dai so aima Yaya wayo kawai”.
Murmushi tayi tana tashi daga jikinsa,, takama hannunsa ta sumbata sannan tatashi tafice daga falon.
Binta kawai yay da kallo yana murmushi, yana k'aunar matarsa kuma 'Yar uwarsa, gaba d'aya Munubiya ta canjashi, dukda bawai miskilancinsa yabariba, itace kawai yanzu baya iyama miskilancin nasa, komai a d'auren da fuskarsa take da zarar ya tunkaro gida zakiga yafara sakin murmushi, balle yay tozali da fuskar tauraruwar nan tashi mai haske da kawalwalniya a zuciyarsa.
Mik'ewa yayi yabi bayanta zuwa kitchen d'in danya taimaka mata da aikin, dan yau d'in weekend ne baije aikiba. dan yayi resume tun last week.

((★))*((★))*((★))*((★))

Tunda na idar da sallar nazame a wajen na kwanta, bawai barcin nakeba, jikinane kawai da baya min dad'i, jinake kamar ana kwankwatsamin kashin jiki, sallamarsa tasakani d'ago ido na kallesa, sannan na amsa ciki-ciki nima.
Frigate ya bud'e ya d'auki ruwa yakoma saman sofar ya zauna, murfin kawai ya 6alle ya hau kwankwad'a, saida ya shanyeshi tas sannan ya ajiye goran yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. nikam na k'ura masa idanu nakasa janyewa. saida yad'ago muka had'a idanu sannan nayi saurin yin k'asa da nawa.
Shi bai janyeba yana kallona yace, “tashi muje hospital d'in, daga nan saimu samo zam-zam d'in”.
Tunkan yakai k'arshen maganarma na mik'e tsaye, hijjab kawai nasaka nad'an gyara fuskata, shikuma ya d'auki kaya yashiga bayi ya canjo sannan muka fice.
Jin gidan shiru yasashi d'aukar waya yakira sashen bayin gidan, babu dad'ewa saiga d'aya acikinsu tazo.
Zubewa tayi tana gaishemu, ya d'aga mata hannu yayinda nikuma na amsa. yace, “ina Samha?”.
“Ranka ya dad'e sunfita suda mummy”.
Yasan aunty Mimi take nufi, dan haka bai sake cewa uffan ba yafice abinsa. sai nice nace tatashi taje, sannan nabiyoshi abaya.
Sai da yasakama k'ofar security sannan muka nufi wajen motarsa, bayin dake zaune a harabar gidan maza sukazo da sauri suna gaishemu, hannu kawai suma ya d'aga musu muka shiga motar, suka bud'e mana gate d'in muka fice.
Tunda muka fita babu Wanda yay magana tsakanin ni da shi, yana aikin tuk'insa da sauraren redio daya kunna a motar, nikam ina lafe a kujera ciwo ya isheni, dan bana fahimtar yaren dasukeyi a redio d'in, tunda ba English baneba gaskiya.

Mun Isa wani babban shagon Islamic camix, komai zaka iya samunsa daya shafi maganin muslinci.
Abinda ya kaimu muka shigayi, yad'ebo zam-zam dayawa, sannan ya kalleni yana fad'in “saikuma mi?”?
Shiru nayi ina nazari. Dame yakamata muk'ara?, zuwa can nad'an hau duddubawa ina karanta sunayen magungunan ajikin kwalin, duk maganin danaga zai iya shafar jinnu ko sihiri, saida na d'akkoshi, (a tunanina idan mun dawo gidan zan d'auki hotunansu na turama Munubiya ta bincikamin yanda yadace ayi amfani dasu.
Duk abinda nake yana a tsaye yana kallona, saida na kammala sannan nasanar masa na gama.
Mun k'arasa wajen biyan kud'i, bayan yabiya yaran shagon d'aya ya d'aukar mana zuwa mota.

Daga nan asibitin muka nufa, mun tarar har lokacin Abie yana barci, sai gaisawa nukayi da momma da aunty Mimi, duk sunji dad'in yanda sukaga Galadima cikin nutsuwarsa. Zama yay kusada Abie yana mai tsurama masa idanu da masa addu'oi samun lafiya a zuciya, da kuma kudirar binne Wanda ya cutar masa da mahaifi da ransa idan ya kamashi a hannu.
Momma tayi farinciki da yanayin Galadima d'in cikin k'oshin lafiyarsa, dan da a dane da yanzu shima yana gadon asibitin, amma Alhmdllh yanzu gashi normal.
Mukam ni da Samha muna gefe zaune muma, ba hira mukeba, kowa yayi shirune yana tunanin duniya.
Sauban ma yana dawowa daga school shida Khaleel nan suka taho.
Bamu bar asibitinba sai dare, harda Momma muka wuce, dan yau suna buk'atar Abie ya kwana tare da ma'aikatansu.

Koda muka shigo Galadima sama ya wuce abinsa, ganin haka Momma tace natashi na naje nima na kwanta na huta hakanan.
A kunyace na mik'e domin cika umarninta.
Na iske yana cire kaya, dan haka nakoma da baya zuwa falo, saida na kintaci yagama sannan na shigo, na iskeshi yashiga wanka, nima natu6e nawa na d'aura zani nasaka hijjab tareda d'aukar kayan barcina ina jiran fitowarsa.
Bai dad'eba sosai kuwa yafito, sanye yake da bathtub fara tas, ban yarda na kalleshi ba natashi nashige nima.
Mai makon yayi shirin barci saiya kwanta a bakin gadon a haka, k'afafunsa na k'asa, ya tsurama rufin d'akin idanu alamar yatafi duniyar tunani.
Nikam ruwa mai zafi na had'a nashiga koda zanji dad'in jikina, na dad'e acikin ruwan kwance, jinakema kamar karna fito. shikansa yafara tunanin lafiya kuwa?, lokaci-lokaci yakan kalli k'ofar bayin, Amma babuni babu dalilina.
Yana shirin zuwa yamin knocking sai gani nafito kuma, janye idonsa yayi daga saitin k'ofar cikeda basarwa.
Ni bammasan yanayiba, dama nayi shirin barcina tun aciki, saina d'auki zani na d'ora a saman kayan nasaka hijjab nayi sallar shafa'i da wutiri, bayan na idar nad'akko roban zam-zam d'in d'aya na zauna nafara karatu Qur'an acikin ruwan zam-zam d'in. a hankali nake karatun cikin nutsuwa, dukda barcin dakecin idona.
Har cikin 6argonsa da jini yakejin sautin karatuna, ya lumshe idanu yanamaijin kamar mu kwana a haka inayi. mik'ewa yayi shima yayo alwala yazo yay shafa'i da witiri yay joining d'ina muka cigaba da karatun a tare.
Bamu kwanta ba saida mukayi sallar asubahi. (da yake sai zuwa 1 zasu bari ashiga wajen Abie, yau kuma babu aiki).

____((()))((*((()))*))((()))____

Yauma dai haka innarmu tadagema abbanmu saida yakira Senator Halluru agabanta, dan Zarah tana kwance babuma lafiya, ga mamansu Yaa Hameed ita kanta kallo d'aya xaka mata kagane abirkice take.
Innarmu duksai suka bata tausayi, matan gidanmu kuwa abin magana yasamu, sai gulma da dariyar gatsatsa, ita kanta Momy Hadiza ta hannun damar mamansu yaa Hameed d'in dad'i takeji, tanadai nuna damuwarta agaban mamansu Yaa hameed d'inne.
Bayan Abba sun gaisa da Senator halluri sukad'anyi barkwancinsu na abokai sannan yasakko xancen Zarah.
Hankalin Senator halluru yatashi, danshi koda wasana baisan Zarah bata nanba, yadai lura kullum Sa'eed saiyaje gida yaci abinci, shi duk zatonsa Zaran bata iya girkine saboda ciki.
Hak'uri yashiga bama Abbanmu yace wlhy shi baima saniba, amma insha ALLAH zai bincika, zuwa dare sa'eed d'in zaizo ya d'auki matarsa.
Dahaka sukai sallana da Abba kowa nakuma bama d'an uwansa hak'uri akan lamarin.
Innarmu bata buk'atar jin k'arin bayani dantaji komai, takumaji dad'i sosai.

()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()-()

Jikin Abie dai kam yayi tsanani a tsakaninnan, yau kwana biyar kenan lamarin sai addu'a, dan baisanma Wanda yake a kansa ba, mai martaba Sarki Abdul'fatah ma yazo shida inno matarsa, (wannan ne karon farko dana gansu ido da ido), mutanen kirki masu d'aukar kowa nasu, duk da d'ar-d'ar danai tayi haka sukaita jana ajikinsu. yanda Galadima yake zubama inno da papi shagwa6a sai abin yaso bani dariya, amma dai sun birgeni, mu a gidanmu wazaima innaro wannan ta6arar bata k'arema uwarsa tanadiba, ba kamarma mu 'yan d'akinmu.
hakama sarki jalalludden shida uwargidansa sunzo da mama Fulani.
Ranar momma har tausayi tabani, kai mama Fulani batada kirki wlhy, idan kunga yanda take shinfid'a mulki a asibitin nan. Hummm🤦🏻‍♀.
Galadima ne kawai maganinta, tamasa magana ya dage ya ya6a mata bak'a shikuma.
Ba gidan suka saukaba, a hotel suka sauka, dan haka yau mun iskesu a asibitin sun rigamu zuwa.
Tunda muka shigo mama Fulani ta zubamin ido, Galadima ya gaida mai martaba da matarsa yakoma kusada Abie ya zaina.
Nima k'asa na durk'usa na gaidasu su dukansu har Momma da aunty Mimi.
Momma ta nunamin kusada ita alamar nazo na zauna kusada. banyi musuba naje na zauna, dan kallon k'urillar da Mama Fulani kemin duk sai na takura.
Tad'an ta6e baki sannan ta gyara zama idonta na kaina, tace “toke amarya halan saikin tashi haihuwa zaki koma mana? daga zuwa dubiya kuna Neman share wata 1 a india”.
Gaba nane yafad'i, dan nafahimci dani take, saina rasa amsar dazan bata..
'Yan d'akin kam kowa ido ya zuba ma mama Fulani har Galadima.
Aunty Mimi ce tace, “Ranki yadad'e Kodai kina Kishine haka? Amarya ta kwance Miki fada wajen mai gidanki?”.
Ajiyar zuciya Momma ta sauke a hankali, taji dad'in yanda aunty Mimi ta mayar da maganar wasa, ko nad'an batason abinda zai munana Munaya ko muzantata, dan bataso yarinyar taji kamar ita dabance a cikinsu.........
Wani munafukin murmushi mama Fulani tayi, ta kalli Galadima da zuciyarsa tafara hasala akan tsohuwar, kamar daga sama sukaji tace, “cikin namu wata nawane Galadima?”............✍🏼

E me🙆🏻 mama Fulani mai gani har hanji🤦🏻‍♀.

*_ALLAH ya gafarta na iyayrnmu😭🙏🏻_*
[7/3, 9:54 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*

*_Haske writer's asso...._*💡

*_♦RAINA KAMA......♦_*
_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻

~Book 2~ 👉🏻2⃣

..............Shiru Galadima ya mata, da ace babu Momma daya ya6a mata maganar da har tabar India tana mata zafi kuwa. amma duk da haka maganar ta daki zuciyarsa, bai saniba ko zancen tsohuwarnan gaskiyane.
Momma da Aunty Mimi da matar sarki kuwa kallona duk sukayi, nayi k'asa da kaina gabana Na luguden duka, saboda zancen tsohuwarnan yana son tsoratani.
Shigowar Sarki Abdul'fatah (papi) da inno matarsa da mai martaba Sarki Jalaluddeen ce ta tak'aita zancen. dan daganan kowa yasaki maganar, saidai munata juyata a zukata ni da Galadima, yayinda aunty Mimi da Momma ke fatan ALLAH yasa hakane.

_____________________________
Chapter 2 · 0% Book details