Sashe 71
Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
saurarenna yakeba barci yakeyi. Ajiyar zuciya na sauke, na cigaba da fad'in “Aunty Salamah tazo gidan ta sameni ai, saboda Munubiya ta sanar mata zaka tafi dani, wannan itace damar farko dana samu na rok'onta yimin bincike akan Muftahu da Saleem yaronka na plaza, (abinda yasa Saleem yashiga Layin zargina saboda randa abinnan ya faru bayan fitowarmu shikuma naga ya fito daga tsakanin wasu motoci a firgice, dayake a time d'in bamusan mizai faruba ban kawo komai a rainaba sai washe gari, danayi bincike a kansa saina gane yaronkane na shago kuma amintacce) daga ita har Munubiya a lokacin basusan dalilina nason amin bincikenba, saidaga baya Munubiya ta fiskanci komai, dayake tanada kaifin basira, amma batasan tsakanina da baba mai kanwa ba. mun tafi India nabar Aunty salamah da wannan aikin”. Knocking k'ofa da akayine ya saka Munaya yin shiru bata cigaba ba, na kalli Galadima da har yanzu idonsa a lumshe, batareda ya bud'eba yabada izinin shigowa, yasan dai bazai wuce Sauban ba. Samha ce ta shigo, ta risina tana gaidashi, sannan tace, “Aunty Amaturrahman ta tashi itada Abduraheem”. Yunk'urawa nayi zan mik'e galadima ya katseni ta hanyar fad'in “jeki kawosu”. Na kallesa da mamaki, yayinda Samha ta fice abinta, “amma yalla6ai darefa yayi, mubari mu k'arasa zuwa gobe mana?”. “uhm-uhm”. Kawai ya fad'a. Shiru nayi nakasa cewa uffan, har Samha da Sauban suka shigo d'auke da yaran duka uku, kar6ar Abdurraheem nayi, dan yaron tausayi yake bani saboda rashin kuzarinsa (karku manta har Yanzu Munaya batasan yaron yanada irin ciwon mahaifinsa ba), su kuma Sauran ya kar6esu. Sauban da Samha suka fice sudai suna tunanin wannan zaman nasu, komi suke tattaunawa oho. Bayan fitarsu a cikin gyale na fara shayar da yaron, Galadima dai baice dani uffanba, sai kallon yaransa kawai yakeyi, na cigaba da fad'in “Abu na biyu dana fara cin karo dashi shine ganin Abie a halin daya tsinci kansa, wannan lamari ya d'aga hankali na, amma a lokacin banida wayar kiran baba mai kanwa na sanar masa, ina tsoron na saka a wayarka kuma ka gano wataran, sai kuma tarihin masarautar nan da Momma ta bani.......” Cikeda mamaki Galadima ya kalleta, dak'yar ya bud'e baki cikin yamutse fuska yace, “Momma!?”. Nace, “eh lallai Momma da kanta, dukkan rayuwar dakasha ta gwagwarmaya ta sanar min, tundaga yarinta zuwa girmanka, ta sanarmin hakanne danna lura da abinda ban saniba a masarautar, kar wani yayi amfani dani wajen cutar dakai. Bayan nan babu dad'ewa kabani waya, daga nan nasamu damar sanarma baba mai kanwa sirrinan guda biyu, ciwon Abie da tarinku. shine yabani dukkan addu'oin da maganin daza'a nema arink'ama Abie, kuma Alhmdllh munakan ganin haske. daga nan kuma na cigaba da samun haske game da dukkan Motsin Muftahu, amma kuma babu wani abinda bai daceba ko cin amana tattare dashi, damukaga mun shiga kokwanto saimuka saka Sarkin Mota da Saleem suka sace manashi a randa kaje d'akkomu a airport ni da Sauban lokacin da Abba yay accident ”. “ya salam! Kina nufin kece?”. Murmushi na masa, nace, “kwarai nice, hakan shine kawai mafita agareka damu kanmu, dan satar nashi ya zame mana haske, aunty salamah taje masa a amatsayin d'aya daga cikin matan Abie, ta hakanne kuma muka ji sunan Harun a bakinsa. daga nan muka sakama Harun ayar tambaya, su Ameer suka cigaba da bibiyar Harun d'in, kayi hak'uri ka gafarceni da abinda zan fad'a yalla6ai”. ‘nai maganar ina kwantar da Abdurraheem na d'auki Amaturrahman dake cinyarsa, itama na fara shayar da ita. “ki fad'i komi ke bakinki, na shirya kar6arsa da makamin HAK'URI”. Murmushi nayi cikin nisawa, “yalla6ai akwai sirrin dabaka saniba Wanda ya banbanta Muftahu da Harun, Muftahu shine masoyinka na gaskiya, Harun kuwa akwai manufar ra6arka tattare dashi, yasan kuma komai game da satar yarannan, akwai dalililai masu yawan gaske dazan iya kare kaina dasu, amma nabaka dama kayi wannan binciken da kanka. Sannan k'arin bayanin dazan maka shine, mak'iyane zagaye dakai, sannan kowanne akwai manufar sa a kanka, abinda yasa suka taru maka da yawa akwai k'iyayyar mahaifanka data dawo kanka a yanzu, wasu saboda tsoron ta6argazar dasuka aikatane basason kayi mulki ka yak'esu, wasu y'ay'ansu sukemawa, wasu iyayensu ne, wasu kuwa kansune, dukkuma akan inhar kahau mulki zaka iya canja komai da hukunta kowane ya sakasu wannan k'iyayyar a gareka, a yanzu dai kanada Avedance guda hud'u zuwa biyar a hannu, na farko sune wad'anda ka kama da yaran nan, yakamata kasan wanene ya saka su kafin kasan dalilin sasun, na biyu Harun, yakamata kasan miyasa yake tad'eka bayan ka yarda dashi Yakuma San airrinka, na Uku shine Saleem, dolene a wannan karon kasan wanene ya sakashi aikin tsaida CCTV cameras a waccan ranar, na hud'u shine SD minene had'insa da mahaifina, na biyar shine Fu'ad wanene ya sakashi kaimu birnin gayu a waccan ranar, sai Malam saminu driver Alhaji balala dan akwai abinda ya Sani tabbas, hakama farhat ku sake bata tsaro sosai, dan mahaifinta zai kawo kansa gareka cikin sauk'i saboda k'aunar dasuke mata, Sauran kuma zuwa nan gaba zan baka haske a kansu, wad'annan dai ka gaggauta sanin abinda suka Sani a cikin kwanaki biyunnan kacal, dan mak'iya bazasu zauna kallonka ba suma, sunacan suna had'a kayan yak'i. zanje na kwanta, saboda yakamata zuwa gobe mu fara shirye-shiryen komawa gida bisa al'adar haihuwar Fari, yau Munubiya tana can ma ita”. Ido kawai ya tsura min yakasa koda motsi, na d'auki Amaturrahman Na Goya, sannan Abdurrahman da Abdurraheem kuma a hannu nayi ficewata. Sauran bayani na k'ok'arin mahaifiyarsa Momma kuwa bazan fad'a masa yanzuba, sai komai ya lafa, saboda suna tattarene da sirrikan dasuka shafeni wad'anda bazan ta6a yarda ya sansuba................✍🏻