← Book details Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 76

Sashe 47

Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

A falo muka iske jakadiya tana kallo, tamin sannu sannan ta gaida Galadima.
yafad'a mata zamu fita, tabimu da addu'ar dawowa lafiya.
Tafiyar tamu takasance shiru kamar yanda muka saba inhar ta had'amu mu biyu, maimakon muje asibiti sai gamu awani gida mai k'yau da tsari, kafin nasamu damar tambayarsa saiga Akash yafito yana zabga murmushi, rungume juna sukayi da Galadima, kafin ya d'ago yanamin sannu da zuwa.
Fuskata da murmushi Na amsa masa tareda gaishesa.
A tsararren falon gidan muka yada zango, komai ya birgrni dan an tsarashi yanda ya kamata. dandanan Akash ya tara mana kaya a gaba, sannan ya zauna muka sake sabuwar gaisuwa. Suka d'ora da barkwancinsu irin Na abokan da suka shak'u. A firar tasune nakejin Auren Akash d'in ya matso, dan zasuyi baiko next week da wadda zai aura, Na tayashi murna da fatan kaiwa da rai. ya amsamin bakinsa har kunne.
Bayanin yawan cin abincina Galadima yamasa, Akash yay dariya, “to inbanda abinka Sameer ai dole taci abinci fiyeda da, karka manta yanzu ba ita kad'ai bace, kuma saitaci abin cikinta zai samu shima, kunk'i yarda ayi scanning muga adadin 'ya'yan namu ko jinsun su”.
galadima ya murmusa kawai, karka damu, miye Na zazzari, kwana nawane insha ALLAH zaizo ko zatazo duniya, yanzu dai tunda ba Matsala bane cin abincin ai Alhamdllh”.
“no babu wata Matsala, abindama yasa zakuga yanzu takanyi saurin jin yunwa cikinta ya tsufa, shima yak'ara girma abin cikin nata, dan zama ta dingajin idan bataciba ana motsi da harbe-harbe a cikin, idan da zaka kalli cikin a time d'in datakejin yunwar sosai har yanda yake wuntsilniya saika gani kaima, Madam ko hakan baya faruwa?”.
Nace, “yana faruwa sosai, amma da zaran naci abincin sai a nutsu”.
Akash yay dariya, “Alamun yana cikin k'oshin lafiya kenan, abincinne kawai buk'atarsa”.
Galadima ya juyo muka kalli juna, gira ya d'agamin nikuma nayi murmushi ina kauda idona gefe.
Daga nan wata hirar suka koma, wadda nake zargin akan Abba nane, dan naji Akash Na fad'in doctor Johnson yabama Abba glasses d'in amatsayin medical glasses, kuma ya gargad'esa karyayi wasa dashi saboda jijiyar idonsa nason samun Matsala, to sunason glasses d'in yazama riga kafine, dayake da turanci suke magana sai yazam inaji nima.
Murmushi Galadima yayi yana jinjina kai.
A raina nace mikuma Galadima ya shiryama Abban?. banida mai bani amsa, dan haka nayi gum.
Muna niyyar tashi Akash yace bamu isaba, bazamu tafi bamuci komai a gidansa ba, kodan munga bashida matane.
Badan munsoba mukad'anci abinda zamu iya, sannan yayo mana rakiya har wajen mota.
Saida munaya tashiga mota sannan Galadima ke fad'ama Akash yayi mantuwa.
Akash yace “tami?”.
Babu kunya Galadima yad'an ciza lips yana tambayar Akash wai miyasa yanzu take gudunsa?.
Akash yabashi amsa da maybe salon cikine, danshi babu yanda baya zuwa ma mace, wani yasata sha'awa wani kuma akasin hakan, amma idan na haihu zan iya komawa normal. Galadima ya basa hannu sukai musabaha sannan ya shigo mota yana masa godiya.
Tunda muka fara tafiya saina kasa jurewa, na jeho masa tambaya muryata a sanyaye.
Kad'an ya juyo ya kalleni ya maida kansa ga tuk'i, saida yaja wasu mintuna kafin yasaki ajiyar zuciya tareda cizar lips nashi, batareda Yakuma kallonna ba yace, “Friend! Wani karatun baya buk'atar fashin bak'i, akan karantashine a barsa a yanda yazo”.
Murmushi nayi ina maida hankalina gareshi, nace “yalla6ai koda shi wannan karatun zai iya fita a jarabawa?”.
“Humm” yafad'a yana rage gudun motar, yanzunma bai kalleniba, yad'an zakud'a jikin sitiyarin sosai, “sometimes akanyi burin cin jarabawane domin canjin aji ko gama makaranta ko shiga, saidai awannan karon ni nawa jarabawar da banbance-banbance tazo, dan bana buk'atar cin jarabawar kai tsaye, har sai harsashina ya isa ga zukatan malaman”.
“to amma yalla6ai karka manta Hasashefa ba shi bane yak'ini”.
“wannan gaskiyane yalla6iya. Saidai yak'ini kuma baya amsa sunan tabbaci, daga lokacinda kika shiga fili wasa kika saka aranki bazakiyi nasara ba, to da kamar wahala kiyi nasarar, duk abinda zanyi nakan rok'i ubangiji nasara Kafin yinsa, sannan na cika zuciyata da kwad'aituwar samun wannan abin, lokuta da dama mutane kan Gaza tsarkake zuciya kafin su cikata da buruka, shiyyasa kikaga duk gudun jirgi a samaniya wataran gaggawa nasakashi tarwatsa a filinda ba muhallin saukarsaba, kiringa zama mai yak'ini saikiga kin tabbata a jerin masu samu”.
Murmushi nayi har hak'orana na bayya, nace, “dakai kanarine danace kafi dukkan halittar kanari iya raira zance, dakuwa mawak'ine saina saka a jerin masu zak'ak'an murya, inkuwa a Marubuci kazo to tabbas kai Kanada yawan fik'ira, domin hikayarka zata yawaita saye zukatan mabiyanka ne”.
Gefen hanya ya gangara, ya kashe motarma baki d'aya ya maido hankalisa gareni.
“Munaaya!” yakirani cikin wani yanayi kuma murya ahankali.
nima saina amsa masa a sanyaye.
Hannuna ya kamo cikin nasa yana mirza yatsun a hankali, yaci gaba da fad'in “A shekarun baya ni mutumne mai ra'ayin Kansa, ma'ana murd'ad'd'e mai wahalar sha'ani, sannan mai zama a bisa tsarinsa, kece mutum ta farko dana fara doguwar magana da ita koda bana so, nakanyi mamaki a duk lokacin da kika taya nazamo mai sallama miki, anya kuwa bakizo da wani Siddabaru ba?”.
Idanu nad'an fiddo waje, nace “siddabaru kuma yalla6ai? to ai awajena ni har gobe kana akan wad'annan ra'ayoyin naka, dan banga canjin dakake hasashen kasamu ba, amma miyasa kace hakan?”.
Numfashi ya sauke ahankali, kafin ya ciji gefen lips nashi yana Sosa girarsa d'aya da d'an yatsa “wannan sak'on zuciyane, kibata dama, zata tabbatar miki da cewar wannan Muhammad Sameer d'in yasha banban dana shekarun baya”.
“sak'on zuciya kuma?”. nafad'a cikin hasashe, dan nikam Yakuma dilmiyar dani.
Mortar ya tada yana fad'in “well basai kin zurfafa ba, dan haryanzu akwai sauran dama”.
Baki na d'an ta6e ina gyara zama, “har walau zancen “dama! dama! dai again?, bana son saka baki a hurumin daba nawaba, amma abinda nasani dama dai duk damace, sannan mai ita yakan tanadar mata dukkan muhalin daya tadace da ita, damarmu ce mu damata takowane
hanya mukaso”.
Idanunsa ya lumshe yana sakin wani k'asaitaccen murmushi daba koyaushe yake irinsaba.
Jin Sautin murmushin ya sakani juyawa na kallesa, ya d'agamin gira yana maida hankalinsa ga tuk'insa.
Babu Wanda yasake yin magana har muka Isa gida. har yanzu babu Wanda ya dawo, dan haka muka haye sama kai tsaye. dama na k'agara na cire rigar jikina saboda azababbiyar zufar danakeji, danma ya tausaya min yad'an saka AC a mota, ban iya zama ba saida na watsa ruwa, nifa abubuwan sunmin yawa, nice jin zafi nice ci kamar gara, harda alwala nayo, Dan magriba tayi.
Ina fitowa shima yashiga yayo alwala. Koda yafito saiya wuce masallaci.
Chapter 47 · 0% Book details