← Book details Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 76

Sashe 6

Raina Kama Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Doctor bai 6oyema Galadima komaiba, yafad'a masa gaskiya jikin Abban yayi tsanani, dan yaji raunuka Na tashin hankali, ga karaya a jikinsa takai hud'u.
Galadima ya cije lips d'insa, kafin yace, “ina police d'in dasuka kawoshi nan?”.
“ai wlhy yalla6ai basu kwana ba, tun jiya around 11pm suka tafi abinsu, kuma har yau basu dawoba”.
Amatuk'ar fusace Galadima yace “Why!!?”.
Doctor yagama rikicewa, jiki Na rawa yace “ban saniba wlhy ranka ya dad'e”.
Harara Galadima ya watsa masa, yace “saboda kaima bakasan aikinka ba? wai......”.
Nuren yay sarin fad'i “Cool down Sameer!”.
“haba Nuren, kajifa wani zancen banza, saboda jami'an tsaron k'asarnan basu san aikinsuba, su kawo mutum cikin irin wannan mawuyacin halin amma bazasu dakata suji wani issues akansaba su tafi, bazama su iya zama zuwa washe gariba ko za'a iya buk'atarsu”.
“sorry ranka ya dad'e”. ‘cewar doctor a tsorace’.
Dady da baba k'arami dake tsaye abakin k'ofa tun d'azun suka k'arasa shigowa, sune suka kwantarma Galadima hankali da nuna masa yayi hak'uri. A girmame ya risina ya gaidasu da tambayar mai jiki.
Suka amsa masa da Alhmdllh.

Cikin mintuna 30 Galadima yasa aka canjama Abba d'aki Na musamman, sannan aka kawo police 5 suka zagaye d'akin.
Hakan yama familyna dad'i sosai, dansu baba k'arami tun a daren jiya sukaga wasu sunata zagaye-zagaye a k'ofar d'akin da Abban ke kwance, ba k'aramin tsoro abin yabasuba, amma basuda mai taimakonsu, sai addu'a dasukai tayi da Neman tsarin ALLAH akan mutanen. Amma gashi yanzu ALLAH ya kawo musu Galadima.
Galadima yasaka doctor yayi shirye-shirye daduk tattara bayanan Abba.

Da k'yar Nuren ya lalla6a Galadima ya amince aka masa treatment d'in hannunsa shima, sai da Dady yasa baki ma, amma da ya dage akan abarsa shifa baya masa ciwo, saigashi hardasu d'inki akayi masa a wajen.
Daga nan suka fito daga office d'in doctor d'in, sunason zuwa inda Accident d'in yafarune.
Harsun kusa fita Galadima yatuna, ya buk'aci abashi wayar Abba idan babu damuwa.
Baba k'arami yace, “ai bama azo da wayarsa asibitin ba gaskiya, maybe ma tana can inda abun yafarune”.
Galadima ya jinjina kai kawai suka tafi.
Su innarmu sunji dad'in abinda Galadima yayi, innaro sai kwararo masa addu'oi takeyi tana kuka.

____(((★)))____

Zuwa yanzu hankalina yakai k'ololuwar tashi, saboda mafarkin Abba na danayi da daddare, abin mamaki a barcin safema dana koma hakance ta faru, nakuma mafarkin Abba yana cikin mawuyacin hali, a firgice na farka jikina sharkaf da zufa, wayata na lalubo nashiga neman wayar Abbana, amma Switch up, nakira Innarmu network yahanata wucewa, hakama Munubiya, hankalina fa ya tashi, haka naitabin Number's d'in 'yan gidanmu ina kira. Amma daga Wanda zaik'i amsamin sai wadda zan kira switch up, saikuma marasa tafiya. kuka nazauna rerawa babu mai lallashina.
A wannan halin Samha tashigo ta sameni, itama hankalinta tashi yayi, takira Momma a waya ta sanar mata gani inata kuka.
Babu shiri Momma tabaro jakadiya da aunty Mimi a hospital tanufo gida, dan itama a cikin damuwa take, na rashinjin Galadima. dan bai sanar da ita ina zaijeba, itakuma bata kawo yana Nigeria bane, tunda bai ta6a tafiya bai sanar mataba, tazata tafiyar kota shafi company d'insu ne.
Ta iso ta iske Samha nata lallashina, jikinta a sanyaye tazo bakin gadon ta zauna, hannuna ta kamo ta jawoni jikinta, batayi maganaba tashiga shafa kaina da bubbuga bayana, munkai kusan 10minutes a haka, harna bar kukan sai ajiyar zuciya kawai.
A tausashe tace, “kiyi hak'uri kinji Munaya, ni kaina hankalina a tashe yake da rashin kiran, dan baita6a hakaba”. (ALLAH Sarki momma ita ta zata saboda rashin kiran Galadima ne, shima rashin jinsa na damuna kam, amma yanzu na Abba ya danne komai).
Samha tace, “Momma amma an gwada Number sa ta Nigeria?”.
“Samha banyi tunanin can yajeba, amma bara na gwada na gani”.
Wayarta ta d'auka ta kira number Galadima ta Nigeria, a mamakinta kuwa saita shiga, cikeda al'ajabi taciro wayar a kunnenta takuma kallon number d'in, tabbas itace dai da gaske. Harta katse bai d'aukaba, takuma kira a karo na biyu.

Lokacin Galadima suna mota zasuje inda Accident d'in Abba yafaru. ganin momma saida gabansa ya fad'i, harta tsinke yakasa d'auka, sai da aka kuma kira Nuren ya d'aga yasaka masa a kunne. muryarsa a sanyaye yay sallama, daga can Momma tace, “lallai Muh'd, yanzu nan dan zakaje Nigeria shine ka 6oyemin? kabi ka tada mana hankali muda matarka, maimakon ma ka sauka kakiramu hankalinmu ya kwanta”.
Runtse idanunsa yayi, muryarsa a sark'e yace, “ki gafarceni Momma, wlhy banason ki hanani zuwanne, nazo kuma na iske wani tashin hankali, shiyyasa ban kirakuba”.
Mik'ewa Momma tayi tafice daga d'akin, ni da Samha muka bita da kallo, tace “innalillahi.. miya farune Muh'd? ”.
Zuciyarsa na suya ya zayyane mata komai daya faru, dukta rikice, “kodai wani yafad'ama Munaya Muh'd?”.
“banajin hakan gaskiya Momma, dan mutanen gidansu basuda Nutsuwar ma sanar da ita, amma miya faru?”.
“hankalinta gaskiya a tashe yake, dan ina asibiti Samha takirani tana sanarmin Munaya nata kuka, babu shiri nabaro asibitin nazo gida, da k'yar na lallasheta, ni na zatama ko rashin kiran dabaka yi baneba”.
“to maybe rashin kiran nawane gaskiya. Amma batasan komaiba, Momma kuma banason tasani harsai yafara samun sauk'i kin...........”
Da sauri Momma ta katseshi “bazai yuwuba Muh'd, dolene anema mata ticket ta taho ko itada Sauban ne, mahaifi yawuce gaban wasa, ko kai baka sanar da itaba dolene wani a cikin 'yan uwanta ya sanar mata, bakuma zata ta6a samun kwanciyar hankaliba, mukuma saita mana wani kallo daban na 6oye matan da mukayi”.
“to shikenan Momma, Sauban yaje ya bincika ko'akwai jirgin dazaizo Nigeria, saiya nema musu tickets, yanzu muna kan hanyar zuwa inda Accident d'in yafaru, idan na koma gida zan kiraki”.
“to shikenan saina jika”.

Momma ta kwantarmin da hankali sosai, sannan takoma asibiti da alk'awarin indai gida nakeso zatasa Sauban ya nema min ticket natafi, amma bata fito ta nunamin ainahin abinda ya faru zanje gidanba.
Dukda inason tafiya gida sainaji kamar akwai abinda ake 6oyemin, saboda wannan tafiya ta gaggawa, sai dai ban tambaya ba nabarma zuciyata kawai.
Sauban kuma yashiga mana shirin tafiya.

______________________________

Tunda Galadima ya ajiye wayar babu Wanda yayi magana a cikinsu, daga Nuren har Galadima kowa damuwar ganin halin da Abba ke ciki tanacin zuciyarsa.
Su Dady ma suna mota kowa shiru, tausayin d'an uwansu da addu'ar samun lafiyarsa kawai kowa keyi.
Police d'in dasuka musu jagora inda Accident d'in yafaru ne suka samu hanya da k'yar, dan motar Abba da thriller d'in data hau kan motar Abban sun tsare rabin hanyar, hakanne ya haddasa go slow sosai, Galadima kam yakasa koda motsi, saima tsirama motar idanu da yayi tacikin glass d'in motar zuciyarsa Na matuk'ar suya.
Saida Nuren ya taimaka masa sannan yafito.
glasses d'insa yad'auka yasaka, Wanda ya 6oye jajayen idanunsa.
thriller d'in data hau kan motar Abbanmu Na gefe itama a kife take, duk Wanda yaga motar ta abbanmu zaiyi zaton mai motar bazai rayuba, saboda fita hayyacinta da tayi.
Jingina da mota kawai Galadima yayi ya hard'e hannayensa a k'irji ya zuba musu idanu.
Nuren kam yanacan jikin motar sosai tare da police d'in dasu Dady ana laluben wayar Abba acikin motar.
Harsun fidda rai da samunta ma, da k'yar aka sami wayar, amma tayi rutsu-rutsu, ga jini dukya bushe a jikinta, cikin Leda aka Sanya, Nuren ya kar6a yabama sarkin mota.
Sund'an k'ara bincikawa kozasu samu wasu muhimman abubuwa, takardune kawai sai abinda ba'a rasaba.
Nuren ya kalli police d'in yana fad'in “amma kamarma wasu sun d'ebi wasu abubuwa a motarnan?”.
“zata iya yuwuwa ranka ya dad'e, Kasan mutane da anyi accident maimakon taimako dasuke bayarwa sai wasu su 6ige da sace-sace kuma”.
Nuren ya jinjina kai kawai, danshi ba mutane yake zargiba.
Yafi zargin wad'anda sukaso kashe abbanne kawai.
Dady da baba k'armi da suke gefe kam harda kwallan su, Dan kallon motarma kawai ya ishi bawa shiga tsantsar tashin hankali.
Sund'an jima a wajen kafin su tafi, Galadima dai yayi d'if, ko magana yakasayi.
Su baba k'arami asibiti suka wuce, sukuma birnin gayu plaza.
Tunda suka shigo ma'aikatan wajen suka zube suna kwasar gaisuwa, Nuren ne kawai ke iya amsa musu, galadima kam hannu kawai yake d'agawa. Kai tsaye Office d'insa Na plaza d'in ya shiga, saima yazo k'asar sau nawa bai shiga Office d'inba kwata-kwata.
Ya zauna tareda zame hular Kansa da glasses d'in, sannan ya jingina kansa da kujera yana mai lumshe idanu.
Nuren ma zama yayi kawai ya zuba masa ido, kusan minti 2 da zamansu Manager d'in plaza yashigo, gaisuwa yakumayi ga uban gidan nasa cikin girmamawa, Galadima ya d'aga masa hannu batare da ya bud'e idonsa ba. hakan yakuma tabbatarma manager babu lafiya kenan.

Kirane yashigo a wayar Galadima, yad'an bud'e ido kad'an ya kalli phone d'in, Harun ne, tun d'azun yake faman kiransa amma bai d'agaba, yasan labarin zuwansa k'asar yazo musune.
Yanzunma bai d'aga ba, ya share, saima kwanciya daya kuma gyarawa a jikin kujerar, da hannu Nuren yayma Manager nuni da yaje.
Manager ya gyad'a kai sannan yafice yana mamakin miya ta6a yalla6ai hakane?.

Idon Galadima a rufe yace, “Nuren wane layine akan wayarnan?”.
Wayar Abba da sarkin mota ya goge fes, duk babu jinin yanzu Nuren ya d'auka ya bud'e, Mtn ne da glo aciki. ya kalli Galadima sannan yace, “glo and mtn ne”.
Galadima ya bud'e idanunsa akan wayar shima, ya d'an yamutsa fuska sannan yace, “dolene muje office d'insu kenan, dan zanso sanin dawa yake mu'amulla, k'ilama zamu iya samun wani abidance”.
“o right, hakan yayi, amma waynote mu fara zuwa kaci abinci kasha maganinka, dan bazai yuwu muyita yawo bakaci komaiba, ni gamma ni nayi breakfast a hotel kafin na fito, kaiko nasan bakaci komaiba, gashi har time d'in lunch yayi”.
“karka damu, banajin wani yunwa ni kam, muje dai muyi salla muje”..
“ina, bazai yuwuba, bara nasa amana oder a wancan restaurant d'in naga suma sun iya abinci”.
Galadima bai sake cewa komaiba, Nuren ya d'auki waya yakira cikin ma'aikatan plaza d'in, saiga Saleem, dan Nuren yasan Galadima ya yarda da Saleem sosai, bayan ya gaishesu Nuren yabashi kud'in.
Amma sai Saleem yak'i amsa, ya fita kawai.
Kusan 30minutes saigashi da yaran restaurant d'in su uku, kowanne d'auke da babban tire, shiya dunga kar6a yana shigarwa office d'in.
Chapter 6 · 0% Book details